Yadda ’yan Boko Haram suka sha da ƙyar a hannun tawagar Gwamna Zulum
Published: 13th, March 2025 GMT
Jami’an tsaro da ke rakiyar tawagar Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, sun daƙile wani harin Boko Haram a kusa da garin Gujba a Jihar Yobe.
Gwamnan da tawagarsa na kan hanyarsu ta komawa Maiduguri daga Biu lokacin da suka haɗu da ’yan ta’addan, wanda hakan ya tilasta musu tserewa bayan musayar wuta.
Bayanai sun ce dakarun tawagar sun ƙwato bindigogi, harsasai, babur, tare da ceto wasu fasinjoji da aka sace.
Wani direba da aka ceto, Malum Ari, ya bayyana yadda maharan suka tare hanyar: “Sun karɓe motata suka tilasta mana kwanciya a ƙasa.
“Amma da suka hango tawagar gwamna, sai suka firgita suka tsere. Wani daga cikinsu ya faɗi a kasa sau biyu kafin ya tsere saboda tsananin firgici.”
Wani fasinja da aka ceto ya koka kan yadda hare-haren suka zama ruwan dare: “Boko Haram na tare hanya da tsakar rana. Ba mu da kwanciyar hankali kwata-kwata.”
Wannan na zuwa ne kwana uku bayan da ’yan ta’adda suka kai hari gari Gujba, inda suka kashe wani ɗan sa-kai mai suna Modu Bulama, tare da ƙone gidaje da shaguna.
Wani jami’in tsaro da ya shaida lamarin ya ce, “Waɗannan ’yan ta’adda sun ƙara samun ƙarfi sosai. Suna kai hare-hare ba tare da tsoro ba. Dole a ɗauki ƙwararan matakai don tabbatar da tsaro.”
A baya-bayan nan ne mayaƙan Boko Haram suka sace wani Farfesan Jami’ar Soji ta BIU da ke Jihar Borno (NAUB) da wasu fasinjoji.
Haka kuma sun sace wani alƙalin kotun Borno, wanda daga baya suka sako shi bayan biyan kuɗin fansa mai yawa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Boko Haram Jami an Tsaro Tawaga
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Bindiga 18 Sun Muta a Wata Arangama da Rundunar Operation Fansan Yamma
Daga Nasir Malali
An kashe ’yan bindiga guda goma sha takwas a wani samame da Rundunar Hadin Gwiwa ta Operation Fansan Yamma ta kai a kauyen Kurawa da ke Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sokoto.
A wata hira ta wayar tarho, wani shaida daga yankin, Malam Aminu Muhammad, ya shaida wa Rediyon Najeriya a Sokoto cewa, nasarar samamen ta fara ne bayan rundunar ta samu bayanin cewa wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mazauna yankin da ke kan hanyarsu ta zuwa kasuwar mako-mako a kan hanyar Tarah zuwa Karawa a Sabon Birni.
Sojojin sun garzaya cikin gaggawa bayan jin harbe-harbe, inda suka kusan awa guda suna musayar wuta da maharan.
Shaidan gani da idon ya ce sojojin sun kwato bindigogi da babura takwas, tare da tabbatar da cewa babu jami’in tsaro ko farar hula da ya rasa ransa ko ya ji rauni a samamen.
Da aka tuntube shi ta waya, dan majalisar dokoki mai wakiltar Sabon Birni a Majalisar Dokokin Jihar Sokoto, Honarabul Aminu Boza, ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa rundunar hadin gwiwar na ci gaba da gudanar da aikin bincike a maboyar ’yan bindigar tare da taimakon wani dan bindiga da aka kama wanda ke nuna wa sojojin hanya a yayin binciken.