Tattalin Arzikin Sin Na Ci Gaba Da Ba Da Gudunmuwa Ga Habakar Tattalin Arzikin Duniya
Published: 27th, June 2025 GMT
Firaministan Sin Li Qiang, ya bayyana a yau Alhamis cewa, tattalin arzikin Sin zai ci gaba da zama mai bayar da gudunmuwa ga ci gaban tattalin arzikin duniya, kuma fadada da ingantuwar babbar kasuwar kasar Sin za ta ci gaba da samar da kyakkyawar gajiya da za ta kara damarmakin cinikayya da zuba jari ga sauran kasashe.
Da yake jawabi yayin bikin bude taro karo na 10 na kwamitin gwamnonin Bankin Raya Ababen More Rayuwa na Nahiyar Asiya (AIIB), Li Qiang ya tabbatar da kudurin Sin na fadada bude kofa da kokarinta na ganin dunkulewar tattalin arzikin duniya, wanda wani yunkuri ne da zai samar da sabbin damarmakin ci gaba a fadin duniya. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Mu Tuna Da Jinin Da Aka Zubar Don Kiyaye Hasken Da Muke Da Shi Yanzu
A cikin fim din “Dead to Rights”, an ce, “Mu tuna da jinin da aka zubar a yakin, don mu kiyaye hasken da muke da shi yanzu.” Abin haka yake, yau mun waiwayi abubuwan da suka faru a tarihi, ba don neman ci gaba da kiyaya da juna ba, a maimakon hakan, muna son kira ga al’ummomin duniya da su tsaya tsayin daka a kan kiyaye zaman lafiya da magance yaki a tsakaninsu.
Yakin duniya na biyu babbar masifa ce ga dan Adam, kuma irin ra’ayi da ake rike da shi game da tarihin yakin, ya zama wata jarrabawa ga dan Adam. A bana ake cika shekaru 80 da al’ummar Sinawa suka samu nasarar yaki da mahara Japanawa, da ma kasashen duniya suka samu nasarar yaki da ‘yan Fascist, kuma rike ra’ayi madaidaici game da tarihin yakin duniya na biyu a daidai wannan lokaci, yana da ma’ana ta musamman ga kasashen duniya, musamman a yayin da ake fuskantar rikice-rikice da zaman dar dar a duniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp