Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Amince Da Nada Kwamishina
Published: 13th, March 2025 GMT
Majalisar dokokin jihar Kano ta wanke Arc. Ibrahim Yakubu Adamu a matsayin kwamishina kuma mamba a majalisar zartarwa ta jiha.
A yayin aikin tantance kwamishinonin, ya jaddada mahimmancin kiyaye babban tsarin ga birane da yankunan karkara.
Ya kuma yi alkawarin bayar da gudunmowarsa wajen sauke nauyin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dora masa.
Adamu wanda a baya ya taba rike mukamin Manajan Darakta na Hukumar Kula da Tsare-Tsare Birane ta Jihar Kano (KNUPDA), ya bayyana jin dadinsa ga majalisar a yayin zaman majalisar.
Shugaban majalisar Jibril Ismail Falgore ya bukaci Adamu da ya kara samun nasarori a KNUPDA tare da yi masa fatan Alheri a sabon mukaminsa.
Nadin Adamu ya yi daidai da ikon da tsarin mulki na Gwamna Yusuf ya ba shi na nada ‘yan majalisar zartarwa ta jiha.
KHADIJAH ALIYU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kwashina
এছাড়াও পড়ুন:
Yan Sanda Sun Kama Muhuyi Magaji, Tsohon Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci a Kano
Gwamnatin Kano ta tabbatar da kama Muhuyi Magaji Rimingado, tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta jihar ranar Juma’a, inda ta yi zargi wasu ‘yansiyasa da hannu a kamen nasa.
Wata sanarwa daga ofishin Kwamashinan Shari’a Abdulkarim Maude ta ce jami’an ‘yansanda ne suka kama lauyan a ofishinsa da ke kan titin Zariya da misalin ƙarfe 5:30 na yamma, kuma suka tafi da shi hedikwatarsu da ke Bompai.
Kwamashinan ya siffanta kamen da “abin damuwa sosai” wanda “ya yi kama da yanayin aikin soja”. Ya yi iƙirarin cewa dakaru kusan 40 ne ɗauke da makamai suka je kama Muhuyi.
“Kwamashinan ya nuna cewa akwai yiwuwar lamarin yana da alaƙa da binciken da ake yi wa wasu manyan ‘yansiyasa,” in ji sanarwar.
Abdulkarim Maude ya kuma yi kira ga rundunar ‘yansandan Najeriya ta yi cikakken bayani game da dalilin kama Muhuyi.