Gwamnatin Gombe za ta sayi takin N8.8bn don tallafa wa manoma
Published: 26th, June 2025 GMT
A ƙoƙarinta na bunƙasa noma da samar da isasshen abinci, Gwamnatin Jihar Gombe ta amince ta sayi tan 10,000 na taki, wanda ya yi daidai da buhu 200,000 domin shirin noman daminar bana.
Kwamishinan Harkokin Noma na Jihar, Dokta Barnabas Musa Malle, ya ce za a kashe Naira biliyan 8.8 wajen sayen takin.
Ya ce hakan na nuna yadda gwamnatin jihar ke ƙoƙarin tallafa wa manoma da kuma ƙara samar da abinci a jihar.
Dokta Malle ya ce, “Gwamnati ta fito da sabbin hanyoyin aiki sama da yadda aka yi a baya, kuma za a raba wa manoma takin domin su fara amfani da shi kafin damina ta sauka.”
Ya kuma bayyana cewa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya zai ƙaddamar da wannan shiri a ranar Alhamis, 26 ga watan Yuni, 2025.
An shirya sayar da takin a farashi mai rahusa domin manoma su iya saya.
Wannan shiri yana daga cikin matakan gwamnatin na tabbatar da ci gaba a harkar noma da kuma shawo kan matsalar ƙarancin abinci a nan gaba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: gwamnati Kwamishina
এছাড়াও পড়ুন:
Soja ya kashe matarsa, ya hallaka kansa a Jihar Neja
Wani soja mai muƙamin Las Kofur ya ɗirka wa matarsa harbi har lahira sannan ya kashe kansa a Jihar Neja.
Las Kofur Akenleye Femi da ke aiki a Bataliya ta 221, ya yi wannan aika-aika ne a Barikin Sojoji na Wawa da ke Ƙaramar Hukumar Borgu a Jihar Neja.
Muƙaddashin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Soja ta 22 da ke Ilorin, Kyaftin Stephen Nwankwo, ne ya tabbatar da lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce abin ya faru ne a ranar 11 ga Oktoba, 2025.
Ya ce mutuwar sojan da matarsa ta haifar da tashin hankali a cikin sansanin soja, inda mazauna wurin suka shiga ɗimuwa da mamaki kan abin da zai iya jawo irin wannan lamari.
Yaƙin Gaza: Hamas da Isra’ila sun fara sakin fursunoni Zaɓen Kamaru: Tchiroma Bakary na da kwarin gwiwa a yayin da ake jiran sakamako“An gano gawar Last Kofur Femi da matarsa ne a cikin dakinsu da ke Block 15, Room 24 na Corporals and Below Quarters a Wawa Cantonment,” in ji Kyaftin Nwankwo.
Ya ce binciken farko ya nuna cewa sojan yana kan aiki a cikin sansanin kafin ya nemi izinin zuwa gida domin wasu bukatun kansa, sai daga bisani aka gano gawarsu a gida.
Kyaftin Nwankwo ya ce an ajiye gawar mamatan domin ci gaba da bincike, kuma rundunar sojan na aiki tukuru don gano musabbabin lamarin.
Rundunar Soja ta Najeriya ta bayyana matuƙar baƙin cikinta kan wannan abin takaici, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalai, abokai da abokan aikin mamatan.
Kwamandan Rundunar, Birgediya Janar Ezra Barkins, ya sha alwashin gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru, tare da ɗaukar matakan da za su hana faruwar irin haka a nan gaba.