Tawagogin tattauna batutuwan cinikayya da tattalin arziki na Sin da Amurka, sun kara tabbatar da bayanan tsarin aiwatar da muhimmiyar matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma yayin tattaunawar da suka yi ta wayar tarho a ranar 5 ga watan nan na Yuni, da karfafa sakamakon da aka cimma a tattaunawar cinikayya da tattalin arziki da aka yi a Geneva.

Kakakin ma’aikatar kula da cinikayya na Sin ne ya bayyana haka yau, inda ya ce an tabbatar da bayanan ne bayan bangarorin biyu sun ci gaba da tuntubar juna bayan tattaunawa mai ruwa da tsaki da suka yi a birnin London a ranekun 9 da 10 ga wata.

Ya ce Sin za ta bi tsarin doka wajen sake nazari da amincewa da izinin neman fitar da wasu kayayyaki da aka takaita fitarwa, ita kuma Amurka za ta cire jerin takunkuman da ta kakabawa kasar Sin.

A cewar kakakin, Sin na fatan Amurka za ta yi amfani da tsarin tuntubar juna kan tattalin arziki da cinikayya dake tsakaninsu, ta ci gaba da karfafa fahimtar juna da rage sabanin dake akwai da karfafa hadin gwiwa don ganin dangantakar Sin da Amurka kan tattalin arziki da cinikayya ya dore cikin aminci. (Fa’iza Mustapha)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: tattalin arziki

এছাড়াও পড়ুন:

An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi

Rahotanni na cewa ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace yayin harin da suka kai a Makarantar Sakandiren Mata da ke garin Maga a Jihar Kebbi sun shaƙi iskar ’yanci.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Wata mata ta kashe ’yar shekara 7 a Ribas
  • Gwamnati Za Ta Biya Wasu Kudaden Ariyas Ga Masu Fensho Wannan Wata
  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Kashe Sama da Naira Miliyan 5 Don Tallafawa Shirin AGILE
  • Majalisar Wakilai ta nemi gwamnati ta gaggauta dauko Jonathan daga Guinea Bissau
  • Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka
  • Jami’an tsaro sun ƙaddamar da shirin murƙushe ’yan bindiga a Kaduna
  • Shugaban Iran: Kasuwar jarin cikin gida sirrin nasarorin gwamnati na tattalin arziki
  • An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi
  • Amarya ta yi wa angonta yankan rago bayan kwana 3 da aurensu a Katsina
  • Amurka Da HKI Sun Kawo Karshen Hukumar GHF Mai Raba Abinci A Gaza