Aminiya:
2025-06-27@21:21:22 GMT

Ƙudan zuma ya tarwatsa ɗaliban da ke jarrabawar NECO

Published: 27th, June 2025 GMT

Wasu gungun ƙudan zuma sun kai hari tare da tarwatsa ɗaliban da ke rubuta jarrabawar Hukumar da ke shirya jarrabawar kammala sakandare ta ƙasa ta Najeriya (NECO) a makarantar sakandaren kimiyya ta Mairi da ke Maiduguri a Jihar Borno.

Wannan hari na ba-zata da gungun ƙudan zumar suka kai ya tilastawa ɗalibai da malaman makarantar tserewa daga harabar makarantar domin neman tsira.

Shugaban APC na ƙasa Ganduje ya yi murabus NDLEA ta kafa cibiyar kula da masu shaye-shaye a Yobe 

Shaidun gani da ido sun ce, sun ga ɗalibai na barin litattafai da takalma da jakunkuna, har ma da kekunansu yayin da suke gudu daga makarantar.

A cewar wani ɗalibin da ke jarabawar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, ƙudan zuman sun daɗe da tarewa a wannan makarantar, amma ba su kai hari a baya ba sai a yanzu.

“Muna rubuta jarrabawar harshen larabci (Arabic) sai ƙudan zuma suka fito gadan-gadan daga wurin da suke da ke harabar makarantar suka far mana da harbi wanda ban san abin da ya jawo harin ba,” in ji wani dalibin.

Wannan lamari dai na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan wani harin ƙudan zuma da suka kai a makarantar Shehu Sanda Kyarimi da ke kan titin Bama a birnin na Maiduguri.

Ma’aikatar ilimi, kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire ta jihar Borno ce ke kula da harkokin ilimi a jihar, gami da tabbatar da tsaron makarantu.

Duk da haka, abubuwan da suka faru irin waɗannan suna nuna buƙatar matakan kare ɗalibai daga barazanar da ba zato ba tsammani makamancin abin da ya faru a yanzu.

Harin dai ya kawo cikas ga gudanar da jarabawar NECO cikin kwanciyar hankali, lamarin da ya janyo damuwa a tsakanin ɗalibai da malamai da iyayen wannan makaranta.

Rahoton na nuna cewar, an yi sa’a kawo yanzu ba a samu asarar rayuka ko mummunan jikkata ba.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Ganduje Ya Ajiye Shugabancin Jam’iyyar APC

Ganduje, wanda ya kasance Gwamnan Jihar Kano daga 2015 zuwa 2023, ya zama shugaban APC a watan Agustan 2023 bayan murabus ɗin tsohon shugaban jam’iyyar, Sanata Abdullahi Adamu daga yankin Arewa ta Tsakiya.

Tun daga wannan lokacin ne wasu daga cikin mambobin jam’iyyar suka fara sukar jagorancinsa, suna ganin naɗa shi ya karya tsarin raba muƙamai na cikin gida da jam’iyyar ke bi.

Dama tuni wasu manyan dattawan jam’iyyar da shugabannin yankuna daban-daban suka bayyana rashin jin daɗinsu, inda suka dk ga kira ga jam’iyyar da ta gyara wannan tsari.

Majiyoyi sun ce saukar Ganduje za ta samar da haɗin kai a cikin jam’iyyar, da kuma gyara matsalolin rabon muƙamai don sake farfaɗo da APC kafin babban zaɓen 2027.

A halin yanzu, babu wata sanarwa da Ganduje ko jam’iyyar APC ta fitar kan murabus ɗinsa.

Murabus ɗin na Ganduje na nuna wani babban sauyi a shugabancin jam’iyyar APC tun bayan hawan mulkin Shugaba Bola Tinubu.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • JAMB Ta Ayyana 28 Ga Yuni Don Ɗaliban Da Za Su Sake Rubuta Jarabawa
  • Ganduje Ya Ajiye Shugabancin Jam’iyyar APC
  • WAEC Na Buƙatar Kwaskwarima
  • Ribas: Duk wani rikici tsakanina da Fubara ya ƙare – Wike
  • Gwamnatin Neja ta rufe Jami’ar IBB bayan ɓarkewar rikici
  • Yadda na kuɓuta daga harin Filato — Wani mutum
  • ’Yan bindiga sun kashe ɗan sanda, sun jikkata wasu 3 a Zariya
  • Bello Turji ya kashe ’yan sa-kai sama da 40 a Zamfara
  • Bejjo Turji ya kashe ’yan sa-kai sama da 40 a Zamfara