Misali, a lokutan hare-haren, an kone gidaje da dama, inda wasu ahali ma, wanda yawansu ya kai, har zuwa 15, aka shafe su, daga doron kasa, a lokacin da suke kan bacci, a gidansu.

Wasu daga cikin wadanda suka tsallake Rijiya da baya daga hare-haren na ‘yan ta’addar, sun bayyna yadda ‘yan ta’addar, suka cinnawa wasu shaguna da ke a wata kasuwa, da ka mayar a matsayin wajen kwanan, ‘yan gudun hijira, wuta.

Duk da kokarin da wasu matasa da kuma kokrin jami’an tsaro na dakile maharani, hakan ya faskare su, hatta wani daya daga cikin jami’in tsaro da aka tura wanzar da tsaro, ya rasa ransa.

Duk a 2025, a watan Afiiru an kai hare-hare a Logo da Ukum, inda aka kashe sama da 50.

Abin takaicin shi ne, duba da cewa akasarin masu kai hare-haren, sai sun sanar sanar suke kai hare-haren.

A gafe daya kuma, shuwagabbin alumma a wadannan yankunan su kan ankarar da hukumomi kafen kai hare-haren, amma abin takaici, mahukuntan, ba su daukar matakan dakile kai hare-haren.

A kwanan baya, Shugaba Bola Tinubu, ya umarci manyan Hafshoshin sojin kasar, da su gaggauta, kawo karshen kai hare-haren, tare da dawo da zaman lafiya a jihar.

Kazalika, ya danganta kashe-kashen, a matsayin na rashin imani da janyo koma baya, inda kuma ya yi kira ga jagororin ‘yan siyasa da shuwagabanin alumomi da ke a jihar, musamman a yankunan da lamarin yafi yin kamari, da su dakatar da rura wata, kan rikice-rikicen, musamman kan yadda suke furta kalaman kiyayya.

Fafaroma, Leo na 14, a na sa bangaren, ya yi tir da kashe-kashen a jihar, inda ya danta lamarin da kisan Kiyashi.

Hakazalika, Gwamnan jihar Hyacinth Alia, a martaninsa, ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta kawo wa jihar dauki, wanda ya yi nuni da cewa,  Biniwe ba wai dokar ta baci take bukata ba, daukin gaggawa take bukata, ta hanyar tura jami’an tsaro da kayan aiki, domin a yaki, masu kai hare-haren.

Sai dai, wannan furucin na gwamnan, tamkar holoko ne, kawai, domin alummar jihar, sun gaji, da yin wani zaman makoki, sun fi bukatar, a samar masu da jami’an tsaro, su kuma koma su ci gaba da noma gonakansu, suna kuma son su ci gaba da barcinsu, da idanuwansu, biyu, a rufe, ba tare da wata fargabar, za a kai masu hari a yayin da suke kan yin barcinsu ba.

A gafe daya kuma, ana ci gaba da cacar baki a tsakanin Gwamna Alia da wasu jiga-jigai na jihar, inda Gwamnan a kwanan baya, ya yi zargin cewa, akwai wasu ‘yan siyasar jihar, da ke zaune Abuja, suke ci gaba da kara rurar wutar rikici a jihar, ciki har da ma wasu jiga-jigan ‘yan Majalisar kasa da suke wakiltar mazabunsu, a majalisar.

Koda yake dai, ‘yan Majalisar, sun karyata wannan ikirarin na Gwamnan, inda suka zargi Alia, da kin wanzar da dokar barin yin kiwo a bainar jama’a a jihar.

Bai wai kawai cafko masu aikata ta’asar ya kamata ayi, ya zama wajibi, a hukunta su, kamar yadda dokar kasar, ta tanada.

Bugu da kari, dole ne Gwamnatin Tarayya, ta gagauta daukar matakai, tare da kuma taimakawa Gwamnatin jihar, domin ta samu karfin tarwatsa masu kai wa alumomin, hare-haren da kare alumomin.

Ya kuma zama wajbi, a sake yin nazari, kan batun iyakokin jihohi da batun burtanin masu kiwon dabbobi da kuma karfafa dangantaka, a tsakanin Fulani makiyaya da sauran alumomin da ke a jihar.

Hakazalika, ya zama wajibi, Gwamnatin Tarayya ta hada taron tattaunawa na kasa, kan batun na kai hare-haren.

Wannan Jaridar, ita ma, ta bi sahun sauran ‘yan Nijeriya, wajen mika ta’aziyyarta, bisa rasa rayukan da hare-haren ya rutsa da su tare da kuma kira da a dauki matakan gaggawa kan batun, ba wai kawai, yin bayanai ba.

Lokaci ya yi, da za a kawo karshen rikice-rikice da nuna kiyaya, a tsakanin juna.

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: kai hare haren kai hare hare

এছাড়াও পড়ুন:

Kano Pillars ta kawo ƙarshen wasanni 8 ba tare da nasara ba

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta samu nasara a wasan mako na 14 na Nigeria Premier Football League (NPFL), bayan da ta doke Ikorodu City da ci 2–1 a filin wasa na Muhammad Dikko, da ke birnin Katsina.

Wannan ita ce nasara ta uku da Pillars ta samu a kakar bana, cikin wasanninta 14, inda ta yi kunnen doki uku, sannan ta sha kashi shida.

’Yan bindiga sun yi yi garkuwa da mutane 11 a Kwara Chelsea za ta kece raini da Barcelona a Gasar Zakarun Turai

Kafin wannan wasan, Kano Pillars ta yi wasanni takwas a jere ba tare da samun nasara ba.

Pillars ta zura kwallayenta ne ta hannun Rabiu Ali, wanda ya zura ta farko a minti na 3, sai Olakunle Alaka ya kara ta biyu a minti na 30.
A daidai minti na 45, kafin a je hutun rabin lokaci, Joseph Arumala ya rage tazara ga Ikorodu City.

Duk da wannan nasarar, Kano Pillars ta ci gaba da zama a matsayi na 20, inda take da maki 9 a ƙasan teburin gasar.

A wani labarin, ƙungiyar Katsina United ta samu nasarar doke Enyimba da ci 3–2 a birnin Ilorin, inda take buga wasanninta na gida bayan dakatar da ita daga yin wasa a filin gidan ta a Katsina.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Wata mata ta kashe ’yar shekara 7 a Ribas
  • Gwamnati Za Ta Biya Wasu Kudaden Ariyas Ga Masu Fensho Wannan Wata
  • NAJERIYA A YAU: Amafani Da Karfin Soji Ko Tattaunawa Ne Zai Kawo Matsalar Tsaro A Najeriya?
  • Aljeriya Tayi Kira Da A Dakatar Da Israila Game Da Hare-haren Da Take Kaiwa
  • Isra’ila Tana Ci Gaba Da Rushe Gidaje A Yankin Gaza
  • An haramta cin naman Kare da Kyanwa a Indonesia
  • Kano Pillars ta kawo ƙarshen wasanni 8 ba tare da nasara ba
  • An buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarawaba a Katsina
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 8 a Kano
  • Abin da ya sa nake haxa harkar fim da harkar karatu-Nabila