Tirela ta afka cikin kasuwa ta kashe mutum da raunata 5 a Taraba
Published: 27th, June 2025 GMT
Aƙalla mutum ɗaya ne aka tabbatar da mutuwarsa tare da wasu biyar suna jinya bayan da wata babbar mota ƙirar tirela ta ƙwace ta kutsa cikin kasuwar Mile Six da ke Jalingo babban birnin Jihar Taraba.
Shaidun gani da ido a wurin sun bayyana cewa, duk ƙoƙarin da direban motar ya yi na hana afkuwar lamarin ya ci tura.
Aƙalla motoci biyu ne suka yi mummunan lalacewa a lamarin.
Jami’an Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) da hukumar tsaro ta farin kaya sibil defens (NSCDC) da kuma rundunar ’yan sandan Najeriya (NPF) sun halarci wurin da jajantawa yankin tare da kawar da ababen hawa don kaucewa sake aukuwar lamarin.
Ɗaya daga cikin manyan motocin da suka tunkari wurin domin wucewa ta hanyar an yi ta jifan su da duwatsu.
Wannan dai shi ne ibtila’i na biyu da ya shafi manyan motocin dakon kaya a yankin inda na farko wata tankar dizal ce wanda ya zube bayan ta faɗi.
An dai ga wasu mutanen da ke wurin suna kuka yayin da wasu kuma suka ɗora alhakin faruwar lamarin a kan rashin ingantattun birki na motoci da ke kan hanyar zuwa kasuwar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Taraba
এছাড়াও পড়ুন:
Gobarar tankar mai ta ƙone gidaje a Jihar Neja
Wata tankar mai ta yi gobara a wani gudan mai a yankin Tungan-Bunu da ke Ƙaramar Hukumar Rijau a Jihar Neja, lamarin da ya janyo ƙonewar gidaje da kadarori da masu yawa.
Shaidu sun ce gobarar ta tashi ne a lokacin da tankar take shirin sauke mai a ranar Litinin da yamma, inda wutar ta bazu zuwa gidajen da ke kusa.
Duk da cewa babu wanda ya rasa ransa, lamarin ya haifar da firgici inda mazauna yankin suka yi ta tserewa suka bar gidajensu yayin da tankar ke ci da wuta.
Tankar mai ta yi hatsari a hanyar Lapai-Agaie Amurka za ta tallafa wa Nijeriya daƙile matsalar tsaro Mayaƙan Boko Haram sun fille kan mata 2 a BornoA wani lamari ba daban, wata tankar mai ta kife a kan hanyar Lapai zuwa Agaie, lamarin da ya toshe hanya tare da haddasa cunkoson ababen hawa.
Shaidu sun ce tankar, wadda ke ɗauke da fetur daga Legas zuwa Gombe, ta kife ne da misalin karfe 10 na safe a ranar Litinin bayan jikinta ya rabu da kan motar, ya ƙetare hanya, abin da ya tayar da hankalin jama’a.
Wani mazaunin yankin, Malam Mahmud Abubakar, ya ce jami’an tsaro sun garzaya wajen domin tsare yankin, sannan aka tura ma’aikatan kashe gobara don kauce wa tashin wuta.
Ya ƙara da cewa lamarin ya faru ne a yankin Efu-Nda-Egbo na Ƙaramar Hukumar Lapai, inda ya haddasa cunkoson ababen hawa mai tsanani.
Kokarin tuntuɓar Darakta-Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Abdullahi Baba Arah, bai yi nasara ba, domin bai amsa kiran wayar da wakilinmu ya yi masa ba.