Aminiya:
2025-11-27@21:56:06 GMT

Yadda aka kama mai garkuwa da mutane yana tsaka da cin kasuwar shanu a Neja

Published: 26th, June 2025 GMT

An kama daya daga cikin mutanen da ake zargi da yin garkuwa da mutum uku a ƙauyen Daku da ke Gwagwalada Abuja lokacin da yake tsaka da cin kasuwar shanu ta Izom da ke Guraran jihar Neja.

Rahotanni sun ce a ranar tara ga watan Yunin 2025 ce dai aka sace wasu makiyaya su biyu da wani direba a kusa da kauyen na Daku.

An sace mutanen ne lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa gida daga kasuwar ta Izom.

’Yan sanda sun kama mutum 5 kan kisan Kanawa 2 a Benuwe Ba zan yi Tinubu ba a 2027 matukar ya canza Kashim Shettima – Sheik Jingir

Mutanen da aka sace ɗin dai a wancan lokacin sai da suka biya kudin fansa har Naira miliyan 15 kafin su shaƙi iskar ’yanci.

Wani ɗan kungiyar sintiri ta bijilan a yankin, Ishaku Daniel, ya ce an cafke wanda ake zargi da garkuwa da mutanen ne wajen misalin karfe 4:00 na yamma a kasuwar bayan daya daga cikin waɗanda ya sace ya gane shi.

Ishaku ya ce an kama mutumin ne sanye da dogayen kaya lokacin da ya shigo kasuwar domin yin sayayya.

Ya ce nan take ’yan sintirin da ke kasuwar suka cika hannu da shi, duk da cewar jama’ar gari sun so su halaka shi a nan take.

Ya kuma ce ’yan sintirin sun sami fakiti-fakitin sigari da tiramol da maganin tari da kuma wiwi a cikin buhun wanda ake zargin.

Ishaku ya ce daga bisani sun mika shi ga jami’an tsaro da suka je kasuwar daga Lambata a jihar ta Neja.

Shi ma wani jami’in tsaro da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da kama mutumin, inda ya ce tuni ya amsa laifinsa yayin da ake ci gaba da bincike a kan lamarin.

Sai dai yunkurin wakilinmu na jin ta bakin Kakakin ’yan sandan jihar ta Neja, SP Wasiu Abiodun, a kan lamarin ya ci tura har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: garkuwa da mutane

এছাড়াও পড়ুন:

An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi

Rahotanni na cewa ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace yayin harin da suka kai a Makarantar Sakandiren Mata da ke garin Maga a Jihar Kebbi sun shaƙi iskar ’yanci.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya
  • ’Yan sanda sun kama masu laifi 34 a Kaduna
  • ’Yan sanda sun kama masu laifi da 34 a Kaduna
  • Tabarbarewar Tsaro na Barazana ga Siyasar Ƙasar Nan Gabanin Zaɓen 2027-Ado Doguwa
  • Uganda: An Kama Fiye Da ‘Yan Hamayyar Siyasa 300 A Lokacin Yakin Neman Zabe
  • Ko sisi ba a biya ’yan bindiga ba kafin su saki ɗaliban da suka sace – Gwamnan Kebbi
  • DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?
  • ’Yan bindiga sun sake kai hari a Kwara, sun sace mutum 11
  • An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi
  • ’Yan bindiga sun yi yi garkuwa da mutane 11 a Kwara