An Yi Bikin Nune-Nunen Kayan Al’adu Na Murnar Cika Shekaru 55 Da Kulla Huldar Diflomasiyya Tsakanin Sin Da Italiya A Rome
Published: 27th, June 2025 GMT
Jiya Laraba 25 ga watan Yuni ne, a birnin Rome na kasar Italiya, aka kaddamar da gagarumin bikin nune-nunen kayan al’adu na murnar cika shekaru 55 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Italiya, karkashin hadin-gwiwar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, da ma’aikatar raya al’adu ta Italiya, da gidan adana kayan tarihi na wayin kan dan Adam na Italiya, da cibiyar koyon fasahohin zane-zane dake birnin Rome na Italiya, da kungiyar wasan kwallon kafar Italiya da sauransu.
Bikin na nuna nagartattun kayayyakin al’adu sama da dari biyu da shahararrun masu zane-zane, da magadan al’adun gargajiya da ba na kayayyaki ba, da sauran wasu masu aikin fasahohin al’adu na kasar Sin fiye da 100 suka yi, tare da kayayyakin al’adu masu daraja sama da 100 da aka adana a gidan adana kayan tarihi na wayin kan dan Adam na Italiya.
A wannan rana kuma, CMG ya shirya bikin musanyar al’adu na murnar cika shekaru 55 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Italiya a birnin Rome, inda aka kaddamar da “makon nuna fina-finan kasar Sin na shekara ta 2025 a Italiya”. (Murala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Labarin Xinjiang A Zane: Aikin Yawon Shakatawa Na Kara Samar Da Arziki Ga Al’ummar Xinjiang
A hakila, sha’anin yawon shakatawa na fadada hanyoyin samun kudi ga mutanen Xinjiang.
Alkaluman da hukumar kula da harkokin al’adu da yawon shakatawa ta Xinjiang ta samar sun shaida cewa, a yayin hutun bikin murnar kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin a kwanakin baya, yankin ya karbi baki masu yawon shakatawa sama da miliyan 18, adadin da ya karu da kashi 11.26% idan aka kwatanta da na bara, kudin da bakin suka kashe ya kai fiye da Yuan biliyan 25, kwatankwacin dalar Amurka sama da biliyan 3.5, wanda kuma ya karu da kashi 11.71%. Hakan ya nuna cewa, aikin yawon shakatawa na Xinjiang yana da makoma mai kyau.
A watan Mayu na wannan shekara, an fitar da “Shirin raya sana’o’in al’adu da yawon shakatawa na Xinjiang (2025-2030)”, wanda ya gabatar da makoma mai haske a wadannan fannoni. Wato a cikin shekaru 6 masu zuwa, Xinjiang za ta dukufa a kan raya sana’o’in al’adu da wasanni da yawon shakatawa, wadanda za su shafi kudin Sin da yawansa ya wuce tiriliyan guda, kuma ana sa ran zuwa shekara ta 2030, adadin baki da yankin zai karba zai wuce miliyan 400 a shekara.
Bunkasar yawon shakatawa a Xinjiang wani bangare ne na ci gaban tattalin arziki da zamantakewa na yankin. Hakan ya baiwa mutane kamar Birey damar kyautata zaman rayuwarsu, ya kuma fadada musu hanyoyin samun kudi. Muna da imanin cewa a nan gaba, karin mazauna yankin Xinjiang za su kara samun kudin shiga, tare da kara jin dadin rayuwarsu, kamar yadda malam Aydarbek Birey ya yi. (Mai zane da rubutu: MINA)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA