An tallafawa iyalan jami’an ‘yan sanda da Naira miliyan N13.4m a Borno
Published: 26th, June 2025 GMT
Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta gabatar da cakin kuɗi Naira 13 da dubu ɗari 4 da 28 da ɗari 6 da 59.95 ga ’yan uwan ’yan sanda 10 da suka mutu a bakin aiki.
Taron gabatar da kuɗin wanda aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Maiduguri, na da nufin bayar da tallafin kuɗi ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, ya bayyana hakan ne manema labarai a hedikwatar rundunar da ke garin Maiduguri.
Kwamishinan ’yan sanda, CP Naziru Abdulmajid ne ya gabatar da jawabin a madadin Sufeto-Janar na ’yan sanda (IGP), Kayode Adeolu Egbetokun.
Wannan shiri yana ƙarƙashin Ƙungiyar ’yan sandan Najeriya (Group Assurance Life and IGP Welfare Scheme) wanda aka tsara don rage wahalhalun da iyalan ma’aikatan da suka yi sadaukarwa ke fuskanta.
Kwamishina Abdulmajid ya jajantawa iyalan waɗanda suka rasu, yana mai tabbatar musu da jajircewar sufeto-janar na ’yan sanda na tabbatar da jin daɗin jami’an da ke aiki da kuma jaruman da suka mutu.
Ya jaddada cewa, sadaukarwar da waɗannan jami’an suka yi ba za a taɓa mantawa da su ba, kuma rundunar ta ci gaba cewa za ta ci gaba sadaukar da kai wajen tabbatar da jin daɗin iyalan da suka bari.”
Kwamishinan ’yan sandan ya kuma shawarci waɗanda suka ci gajiyar kuɗaɗen da su yi amfani da kuɗaɗen cikin adalci, inda ya buƙace su da su saka hannun jari a harkar kasuwanci mai ɗorewa da zai taimaka wajen tabbatar da makomar waɗanda suka mutu na jami’an na su.
Da yake jawabi a madadin waɗanda suka ci gajiyar shirin, Jerry Joel ya bayyana matuƙar godiya ga rundunar ’yan sandan Najeriya da babban sufeton ’yan sandan ƙasar bisa goyon bayan da suka bayar a wannan lokaci mai cike da ƙalubale a gare su.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: waɗanda suka
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya yi alhinin rasuwar tsohon shugaban PDP, Audu Ogbeh
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga jama’a da Gwamnatin Jihar Binuwai bisa rasuwar Cif Audu Ogbe tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Cif Audu Ogbeh.
Ya kuma yi wa iyalansa, abokansa da dukkanin ’yan uwansa ta’aziyya kan rashin da suka yi.
Kotu ta ɗaure wata mata shekara 3 a kan damfara Tsohon Ministan Noma Audu Ogbeh ya rasuCif Ogbeh, ya rasu yana da shekaru 78 a duniya, ya hidimta wa Najeriya a ɓangarori daban-daban ciki har da Ministan Sadarwa a lokacin Jamhuriya ta Biyu.
Sannan daga baya ya zama Ministan Noma a Gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari.
A cewar sanarwar Bayo Onanuga, mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labaru, Ogbeh mutum ne mai basira da zurfin tunani wanda ya taimaka wajen tsara manufofin gwamnati da magance manyan matsalolin ƙasa.
Ogbeh, ya fara harkar siyasa a shekarun 1970 a matsayin ɗan majalisa, sannan daga baya ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar APC.
Shugaba Tinubu, ya bayyana shi a matsayin “Ɗan ƙasa wanda hikimarsa, jajircewarsa, da ƙoƙarinsa na ci gaba suka bar tarihi a siyasar Najeriya.
“Kullum yana da hujjoji da alkaluma don kare ra’ayinsa. Ƙasa za ta yi matuƙar kewar gogewarsa.”
Shugaban ya yi addu’ar Allah Ya jiƙansa ya kuma bai wa iyalansa haƙuri da juriya.