JAMB Ta Ayyana 28 Ga Yuni Don Ɗaliban Da Za Su Sake Rubuta Jarabawa
Published: 27th, June 2025 GMT
“Wannan ya nuna dalibai, 96,838 zasu rubuta jarabawa a fadin Nijeriya gaba daya duk ta wannan shekarar ce, 2025,a cibiyoyin rubuta jarabawa,183,yayin da wasu kuma za su jira.”
Hakanan ma Hukumar tace tana nan tana bankado cibiyoyin rubuta jarabawa da ake yin cuwa- cuwa, da kuma wadanda basu cancanta, ace n arubuta jarabawar a wuraren ba, saboda rashin ingancin abubuwan da ake amfani da su lokacin jarabawar.
Akwai wuraren/ cibiyoyin rubuta jarabawa wadanda aka tantance hakan kuwa ya biyo baya binciken kwakwaf da aka yi lokacin da aka yi jarabawar ta gwaji, jarabawar ta sosai,da wadda aka sake rubutawa.Kamar yadda aka bayyana, kuma kamar yadda sakamakon bincike-binciken da aka yi, akwai cibiyoyin rubuta jarabawa,113 wadanda yanzu an dakatar da amfani dasu,ko ba za ‘a,taba tunanin yin amfani da su ba,a dukkan wadansu ayyuka na hukumar ta JAMB.
Daga karshe Fabian ya kara yin bayani dangane da su cibiyoyin rubuta jarabawar an same su da aikata laifin magudin jarabawa daban daban ko su kasance suna da hannu kai tsaye wajen aikata laifukan da basu dace ba lokacin jarabawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: cibiyoyin rubuta jarabawa
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Kammala Yi Wa Yankuna 5 Na Kare Muhalli Da Halittu Na Kasar Rajista
Ma’aikatar kula da albarkatun kasa ta kasar Sin ta sanar a yau Litinin cewa, kasar ta kammala yin rajistar hakkin mallakar yankuna 5 na kare muhalli da halittu na kasar, a matsayin wani muhimmin mataki na daukaka aikin kare muhalli da halittu.
Yankunan 5 na kasa sun hada da na Sanjiangyuan da na Giant Panda da yankin kare dabbar Tiger na arewa maso gabashin kasar wato the Northeast China Tiger da na kare Damisa da ake kira Leopard National Park da daji mai dumi da damshi na Hainan wato Hainan Tropical Rainforest da kuma yankin Wuyishan.
Rajistar na bayyana ikon da matakai daban-daban na gwamnati ke da shi da bayyana hakkokin mallaka da aikin kula da yankunan da nauyin kula da albarkatun kasa da karfafa hakkin mallakar yankunan kare muhalli da halittu na kasar Sin. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp