Leadership News Hausa:
2025-11-27@21:54:55 GMT

WAEC Na Buƙatar Kwaskwarima

Published: 27th, June 2025 GMT

WAEC Na Buƙatar Kwaskwarima

Duk da haka, a cikin ‘yan shekarun da suka wuce, rashin daidaituwa na jiki ya bayyana. Jami’ai sun fara fitar da takardun tambayoyi domin samun kudi a wasu kwanaki kafin a fara jarabawar, inda ‘yan kasuwa marasa kishi, dillalai, da malalata dalibai suka lalata shirin.

Wannan ya gurgunta kyawawan manufofin WAEC da ta bada fatawa da kuma kawo cikas ga ingancin takaddun shaida.

Abubuwan da suka faru na baya-bayan nan sun kara jaddada lalacewar tsarin ilimin kasar. Kusan wata guda da fitowar WASSCE, matsalar tsara JAMB ta tilasta wa dubban daliban UTME a jihohi shida da wasu sassan Legas yin jarrabawar bayan an basu maki kadan.

Wannan abin takaici ya sa wata daliba da abin ya shafa ta kashe kanta a Legas, sai dai daga baya hukumar ta JAMB ta yarda cewa babbar matsalar da aka samu gazawarta ce ba ta dalibai ba.

Shekarar 1970 ta kawo sauyi a koma bayan WAEC. Badakalar Owosho, inda wani jami’in hukumar ya fallasa amsar da dalibai suka yi a gaban jarrabawar, ya sa aka soke jarabawar a wasu cibiyoyi, wanda ya tilasta wa wadanda suka yi laifi da wadanda ba su ji ba gani ba su ci jarrabawar a shekara mai zuwa tare da kananan yaransu. Sai dai, sulhun da aka yi a shekarar 1977, wanda aka yi wa lakabi da ‘Edpo’ 77’, ya rufe rugujewar Owosho ta kowace fuska.

Dole ne WAEC ta fanshi kanta ta hanyar toshe madogarar da ma’aikatan da ba su da gaskiya suke ba da takardar tambayar ta. Dole ne ta gano tare da mika miyagu ga ‘yansanda domin gurfanar da su gaban kuliya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: WAEC

এছাড়াও পড়ুন:

Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Kashe Sama da Naira Miliyan 5 Don Tallafawa Shirin AGILE

Daga Usman Muhammad Zaria 

Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa, Dr. Builder Muhammad Uba, ya aiwatar da wani aiki na da naira miliyan biyar domin tallafa wa aiwatar da Shirin Tallafawa Yara Mata  (AGILE) a yankin.

Aikin ya hada da gyaran ajujuwa biyu da samar da muhimman kayan aiki, ciki har da injunan dinki, injin yin surfani wato (monogram) da shirin AGILE ya bayar kyauta wanda Dr. Uba ya shirya, ya taimaka wajen ganin an fara amfani da shi, tare da samar da janareta da tabarmi domin inganta koyarwa da horo.

Wannan ci gaban ya biyo bayan wani bincike da tawagar AGILE ta jihar Jigawa ta gudanar a baya, inda ta bayyana cewa wuraren koyon sana’o’in na bukatar gyara.

Shirin AGILE, wani shiri ne na Gwamnatin Tarayya tare da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Jigawa, wanda aka ƙirƙira domin bai wa matasa mata ƙwarewar da za su dogara da kansu, inda ake sa ran mutum 50 za su amfana a horon da ke tafe.

 

A lokacin ƙaddamar da aikin, Mai kula da shirin AGILE a Birnin Kudu, Hajiya Maryam Hassan Jibrin, ta yaba da jajircewar Dr. Builder Uba ga ci gaban al’umma, tana jinjinawa kokarinsa tare da yi masa addu’ar ci gaba da jagoranci mai tasiri.

Da yake tabbatar da jajircewar gwamnatinsa wajen ci gaban matasa, Muhammad Uba ya yi alƙawarin bayar da gagarumin tallafi ga mahalarta bayan kammala shirin cikin nasara.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati Za Ta Biya Wasu Kudaden Ariyas Ga Masu Fensho Wannan Wata
  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Kashe Sama da Naira Miliyan 5 Don Tallafawa Shirin AGILE
  • NAJERIYA A YAU: Amafani Da Karfin Soji Ko Tattaunawa Ne Zai Kawo Matsalar Tsaro A Najeriya?
  • An Zabi JMI A Cikin Majalisar Zartarwan Ta Hukumar Yaki Da Makaman Guba Ta Duniya CWC
  • An buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarawaba a Katsina
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 8 a Kano
  • Abin da ya sa nake haxa harkar fim da harkar karatu-Nabila
  • Amarya ta yi wa angonta yankan rago bayan kwana 3 da aurensu a Katsina
  • Gobarar tankar mai ta ƙone gidaje a Jihar Neja
  • Amurka Da HKI Sun Kawo Karshen Hukumar GHF Mai Raba Abinci A Gaza