2027: Zan karɓi kowane irin muƙami da Tinubu zai ba ni — Sanata Barau
Published: 26th, June 2025 GMT
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya ce zai karɓi kowane irin muƙami da Shugaba Bola Tinubu ya ba shi, amma ya ce a yanzu ba ya son a yi magana kan batun zama mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Yayin wata ganawa da manema labarai kan shirin sauraron ra’ayoyin jama’a da za a yi kan sauya kundin tsarin mulki, Barau ya ce, “Duk abin da Shugaba ya ce na yi, zan yi shi da yaƙini na gaske.
Wannan na zuwa ne bayan ya shawarci wani rukuni da ke goyon bayan ya zama mataimakin shugaban ƙasa da su mayar da hankali wajen tallafa wa ayyukan Tinubu maimakon batun siyasa.
Ya ce, “Yin wannan magana a yanzu bai dace ba. Ban san waɗannan mutane ba, amma na gode da yadda suka yarda da ni.
“Na faɗa musu su daina ɓata lokaci kan abin da lokacisa bai yi ba, su yi amfani da kuɗinsu da ƙarfinsu wajen tallafa wa Shugaban Ƙasa.”
“Idan lokacin siyasa ya yi, za mu shiga. Amma yanzu lokaci ne na aiki.”
Barau ya bayyana Shugaba Tinubu a matsayin jagoran siyasarsa, wanda ya ce yana yi wa biyayya.
Ya gode masa saboda taimakonsa wajen warware rikicin jam’iyya a Kano, dawowarsa majalisa a 2023, da kuma tallafa masa ya zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa.
“Ina son na sanar da ku, idan Shugaba ya ce yana buƙatar na yi aiki tare da shi, zan ce masa ‘na gode sosai,’ kuma zan yi. Duk abin da ya buƙaci na yi, zan yi shi. Zan yi masa biyayya. Shi ne uban ƙasa, kun sani.”
Barau, ya ce su dukkaninsu ’yan jam’iyyar APC ne, kuma suna da ra’ayoyi iri ɗaya.
“Mun fito daga gida ɗaya, mun sadaukar da kanmu ga ci gaba. Ina da ra’ayin ganin an samu ci gaba. Don haka zan yi wa Shugaban Ƙasa cikakkiyar biyayya. A 2027, duk abin da ya ce na yi, zan yi.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Sanata Barau Zaɓe
এছাড়াও পড়ুন:
Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano October 10, 2025
Manyan Labarai Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Karyata Batun Yi Wa Kiristoci Kisan Ƙare Dangi October 10, 2025
Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 9, 2025