’Yan sanda sun kama ɓarayi 5, sun ƙwato kuɗi da makamai a Gombe
Published: 27th, June 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta samu nasarar kama wasu ɓarayin daji da suka addabi garin Bajoga da ke Ƙaramar Hukumar Funakaye.
Wannan na daga cikin ƙoƙarin da rundunar ke yi wajen yaƙar masu aikata laifuka a faɗin jihar.
Ribas: Duk wani rikici tsakanina da Fubara ya ƙare – Wike NAJERIYA A YAU: Ko Wadanne Dalilai Ne Ke Hana Mata A Arewa Koyon Ilimin Kimiyya?A wata sanarwa da Kakakin Rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya fitar, ya bayyana cewa an kama mutum huɗu da ake zargi da kai wa wani matashi mai suna Muhammed Ahmed hari, wanda ke zaune a Unguwar Matasa, Bajoga.
An ce ɓarayin sun kai masa hari da makami cikin dare, inda suka tsoratar da shi da adda da sanduna, suka kuma ƙwace masa kayayyaki.
Sanarwar ta ce laifin ya faru da sanyin safiyar ranar 26 ga watan Yuni, 2025, da misalin ƙarfe 1:30 na dare.
Sun shiga gidan Ahmed ɗauke da makamai, suka kuma yi masa barazana da cewa za su kashe shi idan bai biya musu buƙata ba.
Waɗanda ake zargi da aikata wannan laifi sun haɗa da Manu Muhammed da ake kira (Bappa Charger), Auwalu Muhammed da ake kira (Yellow) mai shekaru 30 daga Bajoga.
Sauran sun haɗa da Ubaida Sani mai shekaru 19 daga Unguwar Pantami a Gombe, da Hussaini Muhammed mai shekaru 19 daga Unguwar Madaki, Gombe.
DSP Buhari, ya ce yayin da ake gudanar da bincike, ’yan sanda sun ƙwato babur ƙirar Haojue UD wanda kuɗinsa ya Naira miliyan 1.6, wayoyi uku da kuɗinsu ya kai Naira 336,000, tsabar kuɗi Naira 74,150, da kuma wuƙa.
Ya ƙara da cewa waɗanda ake zargin suna hannun ’yan sanda yanzu, kuma bincike na ci gaba da gudana.
Ya ce da zarar an kammala bincike, za a gurfanar da su a gaban kotu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda Ɓarayi zargi
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji Sun Kashe Ƴan Ta’adda 9, Sun Ƙwato Naira Miliyan 5 A Borno
Uba ya ce dakarun sun ci gaba da bincike da fatattakar ƴan ta’addan don hana su sake samun damar motsi a yankin Arewa maso Gabas.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA