Yadda na kuɓuta daga harin Filato — Wani mutum
Published: 26th, June 2025 GMT
Ɗaya daga cikin baƙin da suka tafi ɗaurin aure daga Zariya, Abbas Rufa’i, ya bayyana yadda ya kuɓuta daga harin da wasu matasa suka kai musu a Ƙaramar Hukumar Mangu da ke Jihar Filato.
A cewarsa, “Da muka tsaya a hanya domin yin tambaya, na fito daga motar domin neman hanya. Amma sai na ga yadda mutanen da ke wajen suka fara mana wani irin kallo.
“Na ji ɗaya daga cikinsu yana cewa, ‘a kashe su gaba ɗaya, a ƙone motar.’”
Rufa’i ya ƙara da cewa, “Na cire rigata, na shiga cikin daji har na sai da na samu wani mai babur, na ce masa ya kai ni wajen ‘yan sanda. Amma da muka isa wajen wasu sojoji, sai na ce ya tsaya, na sanar da su abin da ya faru.”
Ya bayyana cewa sojojin sin bi shi zuwa wajen, inda suka ceto mutane 18 da suka jikkata, yayin da wasu sun rasu.
Za mu biya diyya – Gwamnatin FilatoKwamishinar Yaɗa Labarai ta Jihar Filato, Joyce Ramnap, ta ce gwamnati za ta biya iyalan waɗanda abin ya shafa diyya.
Ta ce, “Za mu biya diyya. Amma muna jiran rahoton ‘yan sanda kafin mu ɗauki mataki.”
’Yan majalisa sun buƙaci a kama waɗanda suka aikata laifinMajalisar Wakilai ta buƙaci Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Shugaban DSS da Hafsan Sojin Ƙasa su kama waɗanda suka aikata kisan.
Hon. Sadiq Ango Abdullahi ya ce, “Rashin kama masu laifi yana ƙara kawo rashin gaskiya da ƙarancin amana ga gwamnati.”
Kowa yana da ’yancin yin tafiya — Gwamna Uba Sani
Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya ce, “Doka ta bai wa kowa ’yancin zirga-zirga a Najeriya. Gwamnoni su tabbatar da hakan.”
Ya godewa al’ummar Kudan da suka zauna lafiya duk da irin halin da suka tsinci kansu a ciki.
Za a hukunta waɗanda suka aikata laifin – Gwamnatin FilatoJoyce Ramnap ta ce an kama mutum 22 da ake zargi da hannu a harin. “Za mu hukunta duk wanda aka samu da laifi,” in ji ta.
Wannan laifi abu ne da aka tsara — Ƙungiyar Musulmai
Ƙungiyar Musulmai ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta ce, “Ba kuskure aka yi ba. Wannan kisan an shirya shi ne. Idan ba a hukunta masu laifin ba, hakan na iya jawo ramuwar gayya.”
Waɗanda suka aikata wannan laifi dabbobi ne — Ƙungiyar CANƘungiyar Kiristoci ta Arewa ta ce, “Kisan da aka yi wa waɗanda ba su da laifi ba shi ne mafi muni cikin ɗabi’ar ɗan Adam. Wannan rashin imani ne kuma bai dace ba.”
Wannan kisan laifi ne da aka shirya — Ƙungiyar Dattawan ArewaNEF ta ce, “Wannan ba kuskure ba ne, laifi ne da aka tsara. Yana nuna irin matsalolin da ke damun Arewa.”
Ƙungiyar ta buƙaci a hukunta duk masu hannu cikin lamarin.
Kisan ’yan ɗaurin auren da suka taso daga garin Zariya zuwa Filato, ya tayar da ƙura a faɗin Najeriya, inda mutane da dama ke Allah-wadai da kisan.
Yanzu haka dai an zuba wa jami’an tsaro da gwamnati ido don ganin irin matakin da za a ɗauka kan lamarin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Ɗaurin Aure diyya gwamnati hari Jami an Tsaro Tsira Zariya waɗanda suka aikata
এছাড়াও পড়ুন:
Tsohon Shugaban PDP Audu Ogbeh Ya Rasu
Tsohon shugaban jam’iyyar PDP kuma tsohon ministan noma daga 2015 zuwa 2019, Audu Ogbeh, ya rasu a ranar Asabar, 9 ga Agusta, yana da shekaru 78 a duniya, kamar yadda iyalinsa suka tabbatar.
A cikin wata sanarwa, iyalan sun ce: “Ya rasu cikin kwanciyar hankali, ya bar mana gado na gaskiya, hidima da jajircewa ga kasa da al’umma. Mun sami kwanciyar hankali daga yadda ya shafi rayuka da kuma yadda ya kafa misali.”
Ko Nawa Za A Bani Ba Zan Iya Fitowa A Matsayin Kwarto Ko Dan Daudu A Fim Ba -Dan Asabe Olala Jihar Gombe Za Ta Rungumi Shirin Farfado Da Noman Auduga Na Gwamnatin Tarayya – InuwaIyalan sun bayyana cewa za a sanar da yadda za a gudanar da jana’izarsa a nan gaba, tare da godewa abokai, da abokan aiki. Sun kuma roƙi a basu dama domin yin jimamin rasuwar baban nasu.
Rahoton LEADERSHIP ya nuna cewa Ogbeh, wanda ya shahara a siyasa, rubuce-rubuce da aikin gona, ya shugabanci PDP daga 2001 zuwa 2005 kafin ya zama minista a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp