Aminiya:
2025-10-13@18:08:27 GMT

’Yan sanda sun kama mutum 5 kan kisan Kanawa 2 a Benuwe

Published: 26th, June 2025 GMT

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Benuwe, sun kama mutum biyar da ake zargi da hannu a kisan wasu matasa biyu ’yan asalin Jihar Kano.

Waɗanda aka kashe sun haɗa da Jamilu Ahmad da Barhama Suleiman, kuma an kai musu hari ne cikin daren ranar Litinin a unguwar Agan, kusa da ƙofar shiga Makurdi.

Gwamnatin Neja ta rufe Jami’ar IBB bayan ɓarkewar rikici 2027: Zan karɓi kowane irin muƙami da Tinubu zai ba ni — Sanata Barau

An yi jana’izarsu a ranar Talata a Babban Masallacin Abuja, inda manyan jami’ai suka halarta, ciki har da Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, Malam Nuhu Ribadu, da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.

An birne su a maƙabtar Gudu, inda Ribadu da Gwamna Abba sukatabbatar da an yi musu sutura kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada.

Da yake magana da manema labarai bayan jana’izar, Gwamna Abba ya bayyana kisan da cewa: “Abu ne mai ban takaici, zalunci, kuma ba za mu yafe ba.”

Ya buƙaci Gwamnatin Benuwe da hukumomin tsaro su gaggauta kamo waɗanda suka aikata laifin.

“Wannan babban rashi ne ga Kano da ƙasa baki ɗaya. Dole ne a hukunta masu hannu a wannan aika-aika,” in ji Gwamnan.

A gefe guda kuma, ya buƙaci Gwamnatin Jihar Edo ta hanzarta biyan iyalan mafarautan da aka kashe a harin garin Uromi, inda ya yi kira da a tabbatar da adalci da gaskiya wajen magance rikice-rikicen ƙabilanci.

A nasa ɓangaren, Gwamna Hyacinth Alia na Jihar Benuwe, ya yi Allah-wadai da kisan, inda ya ce abin kunya ne kuma ba za su amince da shi ba.

A wata sanarwa daga mai taimaka masa, Tersoo Kula, ya ce ‘yan sanda sun riga sun kama mutum biyar da ake zargi da hannu a lamarin.

“Mutanen Benuwe sun shahara wajen karamci da zaman lafiya. Ba za mu bari wasu ‘yan ta’adda su ɓata mana suna ba. Waɗanda ke da hannu sai sun fuskanci hukunci,” in ji Gwamna Alia.

Ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga gwamnatin Kano, tare da tabbatar da cewa za a yi adalci.

Gwamna Alia, ya ce ya tattauna da Gwamna Abba kan lamarin, kuma ya roƙi jama’ar Kano da Benuwe su zauna lafiya.

Muhammad Ibrahim Khalil, ɗan uwan ɗaya daga cikin mamatan, ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi da ba za su manta da shi ba.

Ya ce abin baƙin ciki ne ganin irin wannan lamari na faruwa a ƙasar da ke da hukumomin tsaro.

Ya roki Allah Ya gafarta musu.

Kisan Jamilu da Barhama ya faru ne a lokacin da ake fama da tashe-tashen hankula a yankin Arewa Ta Tsakiya.

Kwanaki kaɗan kafin faruwar lamarin, wasu ‘yan ɗaurin aure mutum 13 daga Jihar Kaduna sun rasa rayukansu a garin Mangu da ke Jihar Filato.

Gwamnatin Kano ta roƙi jama’ar ta da su kwantar da hankali, su guji ɗaukar fansa, kuma su bar hukuma ta ɗauki mataki.

A cikin wata sanarwa, Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kare ‘yan Kano a ko’ina suke a faɗin Najeriya.

“Kowane ɗan Najeriya yana da ’yancin yin rayuwa, motsi da aiki a ko’ina a cikin ƙasar nan ba tare da tsoro ba.

“Ka da mu bari ƙiyayya da tashin hankali su zama halayenmu,” in ji Gwamna Abba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Arewa Gwamna Benuwe hari kanawa Gwamna Abba

এছাড়াও পড়ুন:

Majalisar Shura ta fara ganawar sirri da Malam Triumph

Majalisar Shura ta Jihar Kano ta fara zama da Malam Lawan Shu’aibu Abubakar (Triumph) kan zargin da wasu kungiyoyi biyar ke masa zargin batanci ga Manzon Allah SallalLahu alaihi Wasallama.

Wannan tattaunawa tana gudana ne a cikin sirri a Ofishin Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) kuma ya samu halarcin fitattun malaman Musulunci na Jihar Kano.

Mahalarta sun haɗa shugaban majalisar shurar  Malam Abba Koki da Wazirin Kano, Sa’ad Shehu Gidado, da sakatare, Shehu Wada Sagagi, da mambobin kwamitin da Majalisar Shurar ta kadfa domin zargin binciken zargin da ake wa Malam Triumph.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisar Shura ta fara ganawar sirri da Malam Triumph
  • Rundunar Ƴansanda Ta Kama Gaggan Ƴan Fashi 9 A Kano
  • ‘Yan Sandan Jihar Neja Sun Tabbatar Da Masu Sa-kai Kan Sahihiyar Kariya.
  • Hukumar Hisbah Ta Kama Wasu Matasa Da Suka Yi Aure Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Kano
  • Mutumin da ya sayar da ɗansa kan N1.5m ya shiga hannu a Ebonyi
  • Sojoji Sun Kashe Kwamandan IPOB ‘Alhaji’, Da Wasu 26, Sun Kama 22
  • ’Yan sanda sun ceto mutum 10 daga hannun ’yan bindiga a Kaduna
  • Shugaba Tinubu Ya Yi Wa Maryam Sanda Afuwa Bayan Shafe Shekaru 6 A Gidan Yari
  • Dalilin IFAD Na Zuba Naira Biliyan 16 A Fannin Noma A Benuwe
  • Sibil Difens ta cafke mutum 3 kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi a Kano