NAJERIYA A YAU: Ko Wadanne Dalilai Ne Ke Hana Mata A Arewa Koyon Ilimin Kimiyya?
Published: 27th, June 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Doctor Zainab Muhammad na daya daga cikin mata a Arewacin Najeriya da ta jajirce tare da kudirin cika burinta na karantar kimiyya duk da kalubalen da wasu matan dake yankin Arewa suke bayyanawa suna fuskanta wurin karantar fannin.
Doctor Zainab ba kimiyya kawai ta karanta ba, ta karanci daya daga cikin kimiyyoyin da ake ganin sun fi kowanne wahala wanda a mafi yawan lokuta ba mata kadai ba har da mazan ma na kauracewa wannan karatun.
Zainab Kwararriyar likita ce wacce ta shahara wurin kula da marasa lafiya a asibitoci. NAJERIYA A YAU: Yadda ‘Yan Najeriya Za Su Kula Da Lafiyar Jikin Su DAGA LARABA: Ko Najeriya Na Da Kudin Renon Sabbin Jihohi?
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai duba ne kan dalilan da suka sa matan Arewacin Najeriya ke tsoron karantar ilimin kimiyya.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kimiyya matan Arewa
এছাড়াও পড়ুন:
Kotu ta ɗaure wata mata shekara 3 a kan damfara
Wata babbar kotu a Jihar Borno, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Aisha Kumaliya, ta yanke wa Kalthum Mustapha hukuncin ɗaurin shekara uku a gidan gyaran hali bayan samun ta da laifin aikata damfara.
Hukumar EFCC ta bayyana cewa, an fara gurfanar da Kalthum a ranar 13 ga watan Mayu, 2024.
Tsohon Ministan Noma Audu Ogbeh ya rasu Fashewar gurneti ya kashe yara uku a BornoAna tuhumarta da karɓar kuɗi Naira miliyan 1.35 daga hannun Muhammad Lawan Sani, Abubakar Umar, da Yusuf Jafar domin samar musu da kayan abinci da ake amfani da su wajen ciyar da yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki.
Sai dai ba ta kawo kayan ba kuma ba ta mayar musu da kuɗinsu ba.
A lokacin shari’ar, lauyoyin masu shigar da ƙara, Mukhtar Ali Ahmed da Faruku Muhammad, sun gabatar da shaidu da hujjoji.
Mai shari’a ta kuma bai wa Kalthum zaɓin biya tara ta Naira 50,000 maimakon zaman watanni shida a gidan gyaran hali.
Bugu da ƙari, kotun ta umarce ta da ta biya Naira 635,000 a matsayin diyya ga waɗanda ta damfara.
Idan kuma ta gaza biyan diyyar, za ta ƙara fuskantar ɗaurin shekaru biyu a kan waɗanda aka yi mata.