Ofishin kula da aikin harba kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin ya ba da labari cewa, jiya Alhamis da karfe 9 da mintuna 29 na dare agogon Beijing, ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-20, wato Chen Dong da Chen Zhongrui da Wang Jie sun cimma nasarar fitowa daga akwatin gwaji na Wentian, yin tattaki a waje na tsawon sa’o’i 6.

5, da kuma komawa akwatin, bisa taimakon na’urori masu hannun injin dake tashar sararin samaniya da jagorancin masu nazarin kimiyya da fasaha dake doron kasa.

Yayin da suke aiki a waje, Chen Dong da Chen Zhongrui sun cimma nasarar hada na’urorin kiyaye tashar sararin samaniya daga sassan wasu na’urorin da aka daddasa a sararin samaniya, da binciken na’urorin dake waje da tashar da daidaita wasu matsaloli da sauransu.

Ya zuwa yanzu, ‘yan sama jannatin suna tafiyar da ayyukansu bi da bi yadda ya kamata, daga baya kuma za su yi nazari da gudanar da aikin gwaji kan bangaren kimiyyar rayuka da tushen samuwar karamar fizga ko “jazibiyya” da kimiyyar albarkatun sararin samaniya da aikin jinya a sararin samaniya da sabbin kimiyya da fasahohin zirga-zirga a sararin samaniya da sauransu. (Amina Xu)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: sararin samaniya da

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Namadi Ya Gabatar da Kasafin Naira Biliyan 900 ga Majalisa

Daga Usman Muhammad Zaria

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya gabatar da kasafin kuɗi na shekarar 2026 na sama da naira biliyan 900 ga Majalisar Dokokin jihar.

Yayin gabatar da kasafin da aka lakaba wa suna Kasafin Kirkire-kirkire da Sauyi Don Cigaban Jigawa II,” Gwamna Namadi ya ce za a ware sama da naira biliyan 693.4, wanda ya kai kimanin kashi 76 cikin 100, don ayyukan raya kasa.

Gwamnan ya kuma ce sama da naira biliyan 208 za su tafi ne ga ayyukan yau da kullum.

A cewarsa, an ware sama da naira biliyan 310 ga bangaren ilimi da lafiya, yayin da kimanin naira biliyan 186 za su tafi ga hanyoyi da sufuri.

Malam Umar Namadi ya ƙara da bayyana cewa an ware sama da naira biliyan 74 ga bangaren noma da kiwo, sai naira biliyan 50.74 don wutar lantarki da makamashi, yayin da naira biliyan 12.68 za su tafi ga shirin ƙarfafa matasa.

Ya nuna cewa an tanadi naira biliyan 25.4 don ruwa da tsafta, sannan naira biliyan 35.4 don muhalli da sauyin yanayi.

Gwamna Namadi ya kuma gabatar da sama da naira biliyan 288 don ayyukan kananan hukumomi 27 na jihar.

 

Radio Nigeria ya ruwaito cewa kasafin shekarar 2026 ya fi na shekarar 2025 da kaso 19 cikin 100.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati Za Ta Biya Wasu Kudaden Ariyas Ga Masu Fensho Wannan Wata
  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Kashe Sama da Naira Miliyan 5 Don Tallafawa Shirin AGILE
  • Makaman Iran Masu Linzami Ne Kandagarkon  Dake Takawa Makiya Birki
  • Jihar Jigawa Za Ta Rufe Karbar Kudaden Aikin Hajjin 2026 Ranar 24 Ga Watan Disamba
  • DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?
  • Gwamna Namadi Ya Gabatar da Kasafin Naira Biliyan 900 ga Majalisa
  • Kano Pillars ta kawo ƙarshen wasanni 8 ba tare da nasara ba
  • Tashar Talabijin ta Press TV ta kaddamar da sashen harshen Hebrew
  • Mali: An Dakatar Da  Aikin Kafafen Watsa Labarun Faransa Biyu A Cikin Kasar Mali
  • NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta