Xi Jinping Ya Gana Da Firaminitan Senegal Da Shugaban Ecuador
Published: 27th, June 2025 GMT
Yau Jumma’a da safe, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Senegal Ousmane Sonko da shugaban kasar Ecuador Daniel Noboa a birnin Beijing, fadar milkin kasar Sin. Wadannan shugabannin biyu sun zo kasar Sin ne domin halartar taron dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya na lokacin zafi na Davos.
A yayin ganawarsa da Ousmane Sonko, Xi Jinping ya ce, kasar Sin tana son zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Senegal, tare da aiwatar da “Manyan matakai 10 bisa hadin gwiwar abokantaka” yadda ya kamata, da kuma kaddamar da karin ayyukan tallafawa al’umma, tare da sa kaimi ga kamfanonin kasar Sin su zuba jari a kasar Senegal domin raya sabbin makamashi, da gina ababen more rayuwa na zamani da dai sauransu, ta yadda Sin da Senegal za su kasance abokan juna dake hadin gwiwa da cimma moriyar juna.
A nasa bangare kuma, Ousmane Sonko ya ce, kasar Senegal da kasar Sin mambobin kasashe masu tasowa ne dake da buri iri daya, kuma kasar Segenal tana son yin mu’amala da kasar Sin kan harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya, tana kuma tsayawa tsayin daka wajen karfafa huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare da kasar Sin, domin inganta yanayin adalci na duniya, tare da kiyaye moriyar kasashe masu tasowa.
Ban da haka kuma, bayan ganawar shugaba Xi Jinping da shugaban kasar Ecuador Daniel Noboa, an kulla shirin “Hadin gwiwa tsakanin gwamantin Jamhuriyyar Jama’ar kasar Sin da gwamantin Jamhuriyar kasar Ecuador, wajen inganta shawarar ‘Ziri daya da hanya daya’”. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Lai Cing-te Ba Zai Cimma Nasarar Kalubalantar Dokar Kasa Da Kasa Ba
Kwanan baya, jagoran yankin Taiwan na kasar Sin Lai Cing-te, ya fitar da wani bayani a fili, inda a ciki ya canja asalin tarihin kasar Sin, kana ya musanta cewa yankin Taiwan wani yanki ne na kasar Sin tun da da can, kuma, ya kauce wa yin tsokaci kan jerin takardun dokoki na kasashen duniya, wadanda suka bayyana yankin Taiwan a matsayin wani yanki na kasar Sin bayan yakin duniya na biyu.
Kazalika, ya kalubalanci kuduri mai lamba 2758 na babban taron MDD da dokokin kasashen duniya. Babu shakka, abin da Lai Cing-te ya yi ya sa ya zama abokin gaban dukkan al’ummomin kasar Sin, da yawansu ya zarce biliyan 1 da miliyan 400, kana ya mai da shi kansa a matsayin mai adawa da tsarin kasa da kasa da yanayin adalci na duniya.
Sai dai, ko me mahukuntan gwamnatin Lai Ching-te za su yi, ba zai canja anihin batun ba, wato yankin Taiwan wani yanki ne na kasar Sin, kuma ba zai canja ra’ayin gamayyar kasa da kasa ba na tsayawa tsayin daka kan manufar “kasar Sin kasa daya tak” a duniya, balle hana dunkulewar kasar Sin baki daya. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp