Ƙarancin abinci: UNICEF ta tallafawa yara 600,000 a Borno, Yobe
Published: 27th, June 2025 GMT
Asusun kula da Ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya bayar da rahoton samun gagarumin ci gaba a ƙoƙarin da take yi na ceto rayukan ƙananan yara.
Da kuma samar da damammakin ci gaba a jihohin Borno da Yobe duk da ƙalubalen da ke tattare da tashe-tashen hankula da talauci, UNICEF ta samu gagarumar nasara a jihohin.
Shugaban ofishin UNICEF na Maiduguri, Joseph Senesie ne ya bayyana hakan a jawabin da ya yi a lokacin wani taron tattaunawa da manema labarai kan ɗa’ar aikin jarida da rahoton kare haƙƙin yara a Damaturu, babban birnin Jihar Yobe.
A cewarsa, a shekarar 2024 UNICEF ta tallafawa jinyar yara kimanin dubu 600 da ke fama da matsanancin halin rashin abinci mai gina jiki, tare da yi wa yara miliyan 1.2 allurar rigakafin cutar kwalara, tare da kai wa mutane miliyan 1.6 allurar rigakafin cutar kwalara.
Bugu da kari, an tallafa wa sama da yara rabin miliyan masu watanni 0-59 da rajistar haihuwa, kuma yara 500,000 sun samu ilimin boko a jihohin Borno da Yobe.
“Duk da haka, duk da waɗannan yunƙurin, ƙalubalen ya ci gaba ne kawai yadda yara 3 cikin yara 10 a Borno, Yobe, da Adamawa aka yi musu rajistar haihuwarsu. Duk da haka, kusan yara miliyan 2 ba sa zuwa makaranta a Arewa maso Gabas, wanda ke nuna buƙatar halin gaggawa na jin ƙai da ci gaba”.
Lamarin da ya ce ya ƙara dagulewa da matsalar ilimi, inda kashi 72 cikin 100 na ɗaliban da suka kammala firamare a yankin ba su iya karatu da rubutu ba, wadda wannan yana nuna babbar gazawa wajen ba da ilimi a matakin farko, kuma yana nuna buƙatar shiga lamarin cikin gaggawa.
UNICEF ta ci gaba da jajircewa wajen yin aiki tare da gwamnatoci da abokan hulɗa domin magance waɗannan ƙalubale.
Haka nan hukumar ta sadaukar da dala miliyan 270 don bayar da agajin jin ƙai da kawar da fatara a Najeriya, inda ta mayar da hankali kan ilimi da lafiya da kuma kariya ga yara masu rauni.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram a Borno
Dakarun Sojin Najeriya sun kashe wani babban Kwamandan Boko Haram, mai suna Abu Nasr, wanda ya jagoranci kai hari garin Rann, da ke Ƙaramar Hukumar Kala Balge, a Jihar Borno.
A makon da ya gabata, dakarun rundunar Operation Hadin Kai, sun daƙile harin da Boko Haram suka kai garin Rann.
Jarumar Kannywood Rahama Sadau ta yi aure Za a biya ma’aikata 445 garatutin sama da biliyan ɗaya a KebbiSun kashe ’yan ta’adda da dama, duk da cewa sojoji biyu sun rasa rayukansu sakamakon harba roka da ‘yan ta’addan suka yi.
Rann na da iyaka da ƙasar Kamaru, kuma daga Maiduguri yana da nisa kusan kilomita 196.
Bayanan jami’an tsaro sun tabbatar cewa Abu Nasr, wanda ya jagoranci tawagarsa zuwa Rann daga Kamaru, ya mutu tare da wasu ’yan ta’addan.
An kuma samu nasarar ƙwato bindigogi, harsasai, bama-baman roka da sauran abubuwan fashewa.
Harin ya faru daga ranar Alhamis, 7 ga watan Agusta, zuwa safiyar Juma’a, 8 ga watan Agusta, 2025, tare da taimakon bayan jiragen sojojin sama.
A cewar jami’an tsaro, an gano gawarwakin ’yan ta’adda bakwai a wajen, kuma akwai yiwuwar sama da hakan sun rasu.