Aminiya:
2025-11-27@21:38:21 GMT

Sheikh Dahiru Bauchi ya cika shekara 101 a duniya

Published: 27th, June 2025 GMT

Babban malamin addinin Islama kuma jagoran mabiya Darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya cika shekaru 101 a duniya, a lissafin kalandar Musulunci.

An haifi Sheikh Dahiru Usman Bauchi ne a ranar 2 ga watan Muharram a shekara ta 1346 bayan hijira, inda a gobe Juma’a, 2 ga Muharram na shekarar 1447, yake cika shekaru 101 cif a ban kasa.

Ƙarancin abinci: UNICEF ta tallafawa yara 600,000 a Borno, Yobe Gwamnatin Katsina ta amince da ƙidayar almajirai, makarantun Islamiyya

Duk da cewa iyalai da almajiran Maulana Shehu Dahiru Usman Bauchi ba su yi wani biki don taya shi murnar cika shekara 100 a duniya, amma masoya da almajiran Shehin Malamin sun bayyana farin cikinsu da yi masa addu’o’i musamman a dandali daban-daban na shafukan Intanet.

Sun yaba da irin hidimar da ya yi wa Musulunci da Bil Adama, inda suka jinjina rawar da ya taka a matsayinsa na shugaba mai kishi da kuma tsayuwar daka.

Daya daga cikin almajiransa, Malam Ahmad Tijjani Saeed ya ce, “Yayin da Maulana Sheikh yake cika shekaru 101 cikin koshin lafiya, ya bar abin koyi mai tarin yawa a rayuwa wajen bauta wa Allah da hidimta wa al’ummarsa da kuma bil’adama.”

Sauran almajiran irinsu Malam Ahmad Tijjani Kolo, Sanusi Ahmad, da Muhammad Sogiji, sun yaba wa jajircewar Sheikh Bauchi wajen yin magana kan zalunci da azzalumai da kuma matsalolin zamantakewa kamar cin hanci da rashawa, kungiyoyin asiri, da shaye-shayen miyagun kwayoyi.

Sheikh Dahiru Usman Bauchi wanda babban jigo a Darikar Tijjaniyya a Nijeriya da Afirka, shi ne Mataimakin Shugaban Kwamitin Fatawa na Majalisar Koli kan Harkokin Addinin Musulunci ta Nijeriya.

Babban malamin na da ’ya’ya kimanin 100 da jikoki 406, da tattaba-kunne 100, wadanda su ma suka gaje shi a fannin  haddar Al-Qur’ani.

Abin sha’awa, 78 daga cikin ’ya’yansa da jikoki sama da 199, da tattaba kunne 12 su ma sun haddacce Al-Kur’ani, hadi da ilimin boko da na addinin Musulunci.

Sheikh Bauchi ya yi aikin Hajji sau 56 da Umrah sau 207.

Hidimar Al-Qurani

Sheikh Bauchi ya fara Tafsirinsa ne a Jihar Bauchi a shekarar 1948, kuma ya shafe shekaru 77 wajen yin tafsirin Alkur’ani mai girma.

An fara yada Tafsirinsa a gidan rediyon Bauchi a shekarar 1976, kafin daga baya gidan rediyon Najeriya Kaduna ya fara yadawa a 1980.

A halin yanzu, gidajen rediyo da dama a arewacin Najeriya suna yada koyarwarsa, musamman a cikin watan Ramadan.

Karatunsa

Ya fara karatunsa na Musulunci ne a hannun mahaifinsa, Alhaji Usman, inda ya haddacce Alkur’ani mai girma tun kafin ya cika shekara 20 a duniya.

Ya ci gaba da karatunsa a karkashin manya malaman  Musulunci na ciki da wajen Najeriya, inda Sheikh Ibrahim Inyass ya kasance babban malaminsa.

A halin yanzu Sheikh Bauchi yana zaune ne a Kofar Gombe da ke birnin Bauchi.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

An Zabi JMI A Cikin Majalisar Zartarwan Ta Hukumar Yaki Da Makaman Guba Ta Duniya CWC

Bayan an zabi kasar Iran a matsayin mamba a kwamitin zartarwa na hukumar yaki da makaman guba ta duniya, wato ‘ the Chemical Weapons Convention (CWC)’ da kuriun jimillar yan majalisar, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa Iran zata yi amfani da damar da ta samu na bin hakkin mutanen kasar Iran dangane da makaman guba wadanda Sadam Husain ya yi amfani da su a kan mutanen kasar a yakin shekaru 8 (1980-88).

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a taron CWC a birnin Hague a ranar Talatan da ta gabata. Ya kuma kara da cewa Iran zata bukaci a hukunta kasashen da suka taimakawa Sadam Husain a wajen amfani da iran wadan nan makamai wadanda suka kashe kuma suka raunata Iraniyawa da dama.

Ministan ya isa birnin Haque ne a ranar Talata da safi don halattan taron na yaki da amfani da makaman guba ta kasa da kasa. A jawabinsa ya ce binciken da gwamnatin kasar Jamus ta yi a bayan, wanda ya tabbatar da laifi kan mutum guda bai wadatarba. Saboda akwai wasu kamfanonin da kum mai yuwa Jami’an gwamnatin kasar Jamus da dama a lokacin suna da hannu a cikin wannan babban laifin da aka aikata kan kasar ta Iran.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka HKI Tana Amfani Da Tsagaita Wuta A Gaza Don Sake Shata Kan Iyakokin Yankin November 27, 2025 Yawan Falasdinawa Da Suka Yi Shahada Na Karuwa Saboka Keta Yarjeniyar Tsagaita Wuta November 27, 2025 An Rutsa Da Tsohon shugaban Kasar Najeriya A Guine Bissau Bayan Juyin Mulki November 27, 2025 Iraki: An Dakatar Da Tura Iskar Gas Zuwa Injunan Bada Wutan Lantarki A Yankin Kurdistan November 27, 2025 Ma’aikatar Harkokin Wajen Falasdinu Ta Sanar Cewa Akalla Yan Mata 33000 Ne Isra’ila Ta Kashe A Gaza November 26, 2025 Mataimakin Shugaban Nijeriya Ya Dawo Gida Bayan Kammala Taron G20 A Afrika Ta Kudu. November 26, 2025 Aljeriya Tayi Kira Da A Dakatar Da Israila Game Da Hare-haren Da Take Kaiwa November 26, 2025 Sojoji Sun Sanar Da Kwace Mulki A Kasar  Guinea Bissau November 26, 2025 Larijani Iran Tana Maraba Da Tattaunawa Ta Gaskiya Amma Ba Tsararren Sakamako Ba November 26, 2025   November 26, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Najeriya : Ana ci gaba da alhinin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi
  • Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi ta bar babban gibi a Najeriya – Tinubu
  • Mutuwar Sheikh Dahiru Bauchi Babban Rashi Ne Ga Kasa Baki Daya- Shugaba Tinubu
  • Mutuwar Sheikh Dahiru Bauchi Babban Rashi Ne Ga Kasa Baki Daya
  • Gwamna Kefas Ya Bayyana Alhininsa Bisa Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
  • Abubuwa 20 da ya kamata ku sani game da Sheikh Dahiru Bauchi
  • Sheikh Dahiru Bauchi: Malamin da zuri’arsa ta fi kowacce yawan mahaddata Alkur’ani
  • Gwamnan Bauchi ya yi ta’aziyyar rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
  • Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa
  • An Zabi JMI A Cikin Majalisar Zartarwan Ta Hukumar Yaki Da Makaman Guba Ta Duniya CWC