Gwamnatin Neja ta rufe Jami’ar IBB bayan ɓarkewar rikici
Published: 26th, June 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Neja, ta rufe Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBBU) da ke Lapai saboda matsalolin tsaro da suka janyo mutuwar wasu ɗalibai.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Abubakar Usman, ya ce an ɗauki wannan matakin ne saboda rashin tabbacin tsaro da ke barazana ga rayuwar ɗalibai da ma’aikata.
Yadda na kuɓuta daga harin Filato — Wani mutum 1447: Yau ce ranar sabuwar shekarar Musulunci – Sarkin MusulmiGwamna Umaru Bago ya amince da rufe jami’ar nan take, kuma za ta ci gaba da kasancewa a rufe har sai an samu sauyi.
“Lafiyar kowa, musamman ɗalibai da malamai, na da matuƙar muhimmanci ga gwamnatin Jihar Neja,” in ji sanarwar.
“Mun yi matuƙar baƙin ciki da abin da ya faru, kuma muna ɗaukar matakan gaggawa don magance lamarin.”
Gwamnatin ta roƙi ɗalibai, malamai da ma’aikatan jami’ar su kwantar da hankalinsu, kuma su kasance masu lura, su kuma yi aiki tare da jami’an tsaro a wannan lokaci.
Haka kuma gwamnatin ta tabbatar da cewa tana ɗaukar matakai domin wanzar da zaman lafiya.
Ta ce duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.
“Za mu ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a, da kuma tabbatar da doka da oda a faɗin Jihar Neja,” in ji sanarwar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ɗalibai Gwamnatin Neja
এছাড়াও পড়ুন:
Jami’ar MDD: Taron Kolin Matan Duniya Ya Zo Daidai Lokacin Da Ya Dace
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Mutane A Fadin Duniya Sun Soki Ayyukan Neman ‘Yancin Kan Taiwan October 12, 2025
Daga Birnin Sin Sharhi: Lai Qingde Ba Zai Iya Jirkita Gaskiya Ba October 12, 2025
Daga Birnin Sin Wang Yi: Sin Na Maraba Da Dukkanin Matakai Na Dawo Da Zaman Lafiya A Gaza October 11, 2025