Ƴan Majalisa Na Binciken Cibiyoyin Ci Gaban Masana’antu 30 Da Aka Yi Watsi Da Su
Published: 27th, June 2025 GMT
Ya kara da cewa, babban makasudin kafa cibiyoyin da kudaden jama’a shi ne bunkasa masana’antu, da rage bukatar musayar kudaden waje, da samar da fa’idoji masu yawa ga kasar nan.
Idu ya ce IDCs, musamman Cibiyoyin shiyyoyi hudu, sun cika da manyan injina don yada ilimin fasahar masana’antu da fasahar da za su yi tasiri matuka kan yunkurin kasar na samar da masana’antu.
Ya bayyana damuwarsa cewa, “A tsawon shekaru, kusan dukkanin IDCs, ma’aikata da kayan aiki a yi asarar su kuma wasu kayan aikin sun daina aiki.
“Duk da cewa gwamnatin tarayya ta mika wadannan cibiyoyi ga hukumar kula da masu kananan sana’o’i ta kasa (SMEDAN) tsawon wasu shekaru a yanzu, babu wani abin da aka yi gaba daya don gyara wadannan cibiyoyi a halin da ake ciki.
“Idan ba a duba wannan yanayin ba, kasar za ta ci gaba da rasa moriyar masana’antu, wanda hakan zai shafi yanayin rayuwar jama’a.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Kashe Sama da Naira Miliyan 5 Don Tallafawa Shirin AGILE
Daga Usman Muhammad Zaria
Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa, Dr. Builder Muhammad Uba, ya aiwatar da wani aiki na da naira miliyan biyar domin tallafa wa aiwatar da Shirin Tallafawa Yara Mata (AGILE) a yankin.
Aikin ya hada da gyaran ajujuwa biyu da samar da muhimman kayan aiki, ciki har da injunan dinki, injin yin surfani wato (monogram) da shirin AGILE ya bayar kyauta wanda Dr. Uba ya shirya, ya taimaka wajen ganin an fara amfani da shi, tare da samar da janareta da tabarmi domin inganta koyarwa da horo.
Wannan ci gaban ya biyo bayan wani bincike da tawagar AGILE ta jihar Jigawa ta gudanar a baya, inda ta bayyana cewa wuraren koyon sana’o’in na bukatar gyara.
Shirin AGILE, wani shiri ne na Gwamnatin Tarayya tare da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Jigawa, wanda aka ƙirƙira domin bai wa matasa mata ƙwarewar da za su dogara da kansu, inda ake sa ran mutum 50 za su amfana a horon da ke tafe.
A lokacin ƙaddamar da aikin, Mai kula da shirin AGILE a Birnin Kudu, Hajiya Maryam Hassan Jibrin, ta yaba da jajircewar Dr. Builder Uba ga ci gaban al’umma, tana jinjinawa kokarinsa tare da yi masa addu’ar ci gaba da jagoranci mai tasiri.
Da yake tabbatar da jajircewar gwamnatinsa wajen ci gaban matasa, Muhammad Uba ya yi alƙawarin bayar da gagarumin tallafi ga mahalarta bayan kammala shirin cikin nasara.