Leadership News Hausa:
2025-08-11@02:12:50 GMT

Wannan Imanin Ne Ya Kai Likitocin Sin Nahiyar Afirka…

Published: 26th, June 2025 GMT

Wannan Imanin Ne Ya Kai Likitocin Sin Nahiyar Afirka…

Ban da haka kuma, wani babban dalilin da ya sa kasar Sin ke kokarin tallafa wa sauran kasashe a fannin aikin likitanci, shi ne akidarta ta “kafa al’ummar duniya mai kyakkyawar makoma ta bai-daya”. A cikin gidan kasar, an yi nasarar kawar da talauci, da kokarin neman wadatar da dukkan al’ummun kasar, lamarin da ya sa ake samun jituwa a tsakanin al’umma, da ci gaban tattalin arziki mai dorewa.

Saboda haka, kasar Sin na ganin cewa, kamata ya yi, a yi kokarin tabbatar da ci gaban tattalin arzikin kasashe daban daban na bai-daya, inda za a dinga rage gibin dake tsakanin kasashe, da na zaman rayuwar al’ummu daban daban, ta yadda za a iya daidaita matsalolin da dan Adam ke fuskanta, da tabbatar da kyakkyawar zamantakewa a duniya.

Wadannan tunani da imani na Sinawa ne suka kai marigayi Zhang Junqiao nahiyar Afirka, inda ya yi kokarin ba da taimako wajen ceton mutane, har ma ya sadaukar da ransa. Amma karin likitoci Sinawa suna ci gaba da kokarin nuna wannan imanin a wurare daban daban na duniyarmu. Da ka ga wadannan mutane, to, za ka yarda cewa, tabbas za a samar da duniya mai dadin zamantakewa da jituwa da ci gaba a wata rana. (Bello Wang)

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Jarumar Kannywood Rahama Sadau ta yi aure

Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau, ta yi aure da masoyinta, Ibrahim Garba.

An ɗaura auren a ranar Asabar a Masallacin da ke Unguwan Rimi, a Jihar Kaduna, bayan Ibrahim ya biya sadaki Naira 300,000.

Za a biya ma’aikata 445 garatutin sama da biliyan ɗaya a Kebbi Kotu ta ɗaure wata mata shekara 3 a kan damfara 

Rahama, ta sanar da ɗaurin auren a shafinta na Facebook, inda ta gode wa Allah tare da neman addu’a daga masoyanta.

Ta bayyana farin ciki da godiyarta, tare da fatan wannan sabon babi na rayuwarta zai kasance mai albarka.

Auren mata na zuwa ne watanni biyu bayan rasuwar mahaifinta, Ibrahim Sadau.

’Yan uwanta sun yaɗa hotuna da bidiyon bikin a kafafen sada zumunta, inda mutane da dama suka yi mamakin yadda aka yi bikin ba tare da sanin jama’a ba.

Rahama, wacce furodusa ce a Kannywood, an naɗa ta memba a Kwamitin Fasaha na shirin Investment in Digital and Creative Enterprise (iDICE).

An ba ta muƙamin ne a 2024 ƙarƙashin ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Na Yi Lokacin Da Idan Aka Gan Ni Ake Gudu A Masana’antar Kannywood – Mai Dawayya
  • Ana Zanga-Zanga A Isra’ila Kan Shirin Netanyahu Na Mamaye Gaza
  • Andrei Okounkov: Sinawa Na Daukar Koyon Abubuwa Da Muhimmanci 
  • An Ɗaura Auren Rahma Sadau A Kaduna
  • Jarumar Kannywood Rahama Sadau ta yi aure
  • Ina Fatan Taka Inda Yayana Ya Taka A Fagen Ƙwallon Ƙafa A Duniya -Jobe Bellingham
  • Afrika Ba Ta Cikin Jerin Fannonin Da Muke Ba Fifiko – Amurka
  • An Bude Taron Mutum-Mutumin Inji Na Duniya Na 2025 A Yau Juma’a
  • Sin Ta Gabatar Da Korafi Da Babbar Murya Dangane Da Kalaman Jagoran Philippines 
  • Faɗace-Faɗacen Daba Da Ƙwacen Waya A Kano Ya Ɗauki Sabon Salo