Shugaban APC na ƙasa Ganduje ya yi murabus
Published: 27th, June 2025 GMT
A wani mataki na ba-zata, shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya yi murabus daga muƙaminsa nan take.
Ganduje, wanda tsohon gwamnan Jihar Kano ne, ya bayyana dalilan rashin lafiyarsa ne ya sa ya ɗauki matakin murabus, inda ya bayyana cewa yana buƙatar ya maida hankali kan lafiyarsa.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-Bissau
Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya maƙale a Guinea-Bissau bayan da sojoji suka yi juyin mulki tare da karɓe ragamar mulkin ƙasar.
Jonathan da sauran baƙi baƙi masu sanya ido kan zaɓen da aka gudanar, ba za su iya barin ƙasar ba domin sojoji sun rufe iyakokin ƙasar baki ɗaya, tare da dakatar da zaɓen gaba ɗaya.
Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka Andrea Thompson ta zama mace mafi ƙarfi a duniyaLamarin ya samo asali ne bayan manyan ’yan takara biyu sun yi iƙirarin samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana.
Ba jimawa wasu dakarun sojin ƙasar suka hamɓarar da gwamnatin farar hula ta ƙasar.
Sun kuma sanar da dokar hana fita da kuma kama manyan jami’an da ke da alaƙa da zaɓen.
“An hamɓarar da gwamnatina,” in ji Shugaba Umaro Sissoco Embalo cikin wata tattaunawa ta waya da gidan talabijin na ƙasashen waje.
Jonathan ya je Guinea-Bissau ne a matsayin shugaban tawagar West African Elders Forum (WAEF) domin sanya ido kan zaɓen.
Ya ziyarci wasu rumfunan zaɓe a ƙasar kuma ya wallafa bayanai a kafafen sada zumunta kafin juyin mulkin.
Mutanen da ke tare da shi sun ce yana cikin ƙoshin lafiya, amma ba shi da damar barin ƙasar.
Sojojin suna kuma ƙoƙarin katse Intanet, lamarin da ya sa ake samun tangarɗa wajen sadarwa a ƙasar.
Hakan ya sa ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa suka fara nuna damuwa kan tsaron manyan ’yan siyasa da jami’an zaɓe.
A cikin wata sanarwa, Jonathan da wasu shugabannin Afirka sun yi Allah-wadai da juyin mulkin.
“Mun yi Allah-wadai da wannan yunƙuri na daƙile tsarin dimokuraɗiyya, kuma muna kira ga Tarayyar Afirka da ECOWAS su ɗauki matakin dawo da tsarin mulki,” in ji su.
Sun buƙaci mutanen Guinea-Bissau su kwantar da hankalinsu, tare da kira ga sojoji su saki dukkanin jami’an da suka kama domin a ci gaba da gudanar da zaɓe cikin lumana.