Ya kafa cibiyar ‘Yakubu Gowon Centre’, wadda da farko ta maida hankalinta ne kan zaman lafiya, da raba rigima, daga baya kuma sai ta ta fadada ayyukan da take yi da suka hada da lamarin kula da lafiya, musamman ma yadda za a kawo karshen, cuta mai karya garkuwar jiki, Zazzabin maleriya,  da kuma cutar Hanta da aka fi sauran kamuwa da ita.

Yanzu cibiyar ta yi hadin gwiwa da Hukumar ci gaban sashen Arewa maso gabas (NEDC) saboda a hana yaduwar cutar Hanta mai saurin kamuwa,a Jihoihn sashen  wadanda suka hada da Adamawa,Bauchi, Gombe, Borno, Taraba,da kuma Yobe.

Gowon ya ci gaba da kasancewa mai hannu a cikin lamurran da suka shafi zaman lafiya, shirya yin addu’oi saboda kasar Nijeriya da kuma kara bunkasuwar hadin kan al’umma, abin da za a iya ganewa, da amfani da shi a matsayin wata sheda, lokacin da ya kan kasance, babban bako na musamman a taron karol na kirsimati na shekara a Jihar Plateau. Lokacin taron ya bayyana muhimmancin addu’a, zaman lumana da kuma yin yafiya, da kuma sasantawa tsakanin al’ummar Nijeriya wadanda suka bambanta lamarin addini da kuma yadda al’umma suka rarrabu ta hanyar.

A shekarar 2016, an karrama shi da nambar  National Goodwill Ambassador ko kuma wani jakada saboda kokarin kawar da cutar Hanta mai saurin kamuwa a Nijeriya.

Da yake jawabi dangane rayuwa da Shugabanci na Gowon, wakilin kasa na cibiyar Carter a Nijeriya, Dakta Emmanuel Miri, ya nuna irin fafutukar da ya yi wajen kawar da cutar Kurkunu a Nijeriya. Lokacin da cutar take cikn ganiyarta, Nijeriya tana da mutane fiye da 650,000 wadanda suka kamu da cutar – ita ce wadda tafi sauarn kasashe 20 da suka kamu da cutar. Shigar Gowon cikin al’amrin ya yi sanadiyar ta samu takardar sheda daga Hukumar lafiya ta duniya saboda yadda aka gama da cutar.

Dokta Miri ya nuna jin dadin irin gudunmawar daya bada da maida hankali, inda har ya tuna da yadda tafiya da kafa zuwa wurare suke da wahalar zuwa, yana ilmantar da mata da yara  yadda za a kaucewa kamuwa da cutar, irin  hakan babu wani wanda ya taba Shugabancin Nijeriya da zai iya yin hakan.

Janar Yakubu Gowon wasu baubuwan da yak e yi bayan ya yi ritaya shi ne lamarin kamar yin hidima saboda al’umma wato yin duk wadansu abiubuwan da aka san za su taimaka masu, kamar kulawa da lafiya hada kan kasa, yin abinda ko abubuwan da za su kara bunkasa  yadda al’umma za su samu kyakkwarar rayuwa yanzu da kuma gaba.

Obasanjo:

Ya ba  harkar kasuwanci muhimmanci, Ilimi,bunkasawa da ci gaban Shugabanci

Tsohon Shugaban kasa Olusegun Matthew Okikiola Ogunboye Aremu Obasanjo shi tsohon soja ne mai mukamin ritaya Janar, wanda ya yi Shugabanci kasa sau biyu, da farko Shugaban kasa na mulkin soja daga shekarar 1976 zuwa 1979, sai kuma na mulkin farar hula daga shekarar 1999 zuwa 2007.

Tun lokacin daya kammala wa’adinsa na biyu a watan Mayu 2007, Obasanjo ya fara rayuwa bayan Shugabancin kasa wanda ya kammala wadda take dauke da abubuwa daban- daban, da suka shafi zuba jarin kasuwanci, harka da kasashen waje, Shugabanci da  harkar ilimi.

Obasanjo ya kasance wani mashahurin mutum tsakanin kasa da kasa, sau da yawa ya kan fita zuwa kasashen waje domin ya yi jawabi saboda zaman lafiya, mulkin farar hula,da kuma irin yadda tattalin arzikin Afirka zai kasance zuwa gaba. Shekarun da suka gabata harkar ta shi ta sha gaban Nijeriya, abin ya kai ga wasu kasashe kamar Kamaru, da kuma jamhuriyar Benin – inda yake maida hankalinsa kan bangarorin Otal, wutar lantarki, da kuma aikin gona.

Ta kamfanin Obasanjo Holdings (OHL), mai hedikwata a gidan Agbelobam hanyar Kuarry, Abeokuta, Jihar Ogun, yana da babban Kamfanin a jamhuriyyar kasar Benin. Yayin da a Kamaru kuma yana da kamfanin da ake sarrafa kayan amfanin gona wanda ya kai dalal Amurka milyan 700 in wutar lantarki da kuma aikin gona.

Obasanjo yana ba da muhimmayar gudunmawa a tafarkin tattalin arziki wanda yake fatan zai saita kasashen Afirka saboda a jawo hankalin masu zuba hannun jari daga kasashen waje. Iinda za a rika hada kai ta bangarorin wutar lantarki, aikin gona, da kuma abubuwan more rayuwa.

Harkar shakatawa da dakin karatu na Shugaban kasa

Obasanjo shi ne wanda ya dauki nauyin dakin karatu na Shugaban kasa a Abeokuta (OOPL) Abeokuta,  wani babban wuri ne wanda yake bayanin kan ayyukan da yayi, da kuma kara daukaka Shugabanci da yadda ya dace a tafiyar da shi, sai kuma tarihin Afirka.Duk a cikin filin da aka yi dakin karatu akwai  Green Legacy Hotel, wurin shakatawa wanda aka yi shi saboda baki, da kuma masu zuwa yin bincike.

Bugu da kari ma yana da wuraren da baki za su kwana a wani wuri  wanda aka kebe  na musamman a Ibara Gobernment Reserbation Area (GRA) a Abeokuta, wanda yake samar da wuraren kwana na musamman ga baki.

Obasanjo mutum ne wanda ya dade yana sha’awar aikin gona ya kafa wata gona da ake kirra da suna Ota  a shekarar 1976 lokacin da yake Shugaban kasa na mulkin soja,a  karkashin tsarinsa na ‘’ciyar da kasa da abinci.” Halin da ake ci yanzu al’amuran aikin gona na Obasanjo ya baza su a Jihohi da dama da suka hada da Benue, Oyo, Edo, da kuma Delta,hakan ta say a kasance babban wanda ya zuba jari ta harkar bangaren kasuwancin noma.

Mai da’awar damukuradiyyar Arewa

A gida, Obasanjo ya ci gaba da kasancewaabin koyi da kuma bada ta shi gudunmawar kan lamurran cikin gida. Musamman ma yadda yake zama uwa da makarbiya kan mulkin farar hula na nahiyar Afirka, wato wanda yake tafiya abubuwan al’umma wadanda suke tafiya tare da al’adun mutane, ba yadda za a rika ban a kasashen waje fifiko ba, inda wanda ya samu nasara yake “dauke dukkannin abubuwan shi kadai ba tare da tunanin wani ba” .

Domin ya ce kasashe ko kungiyoyin Afirka suna bukatar tsarin gwamnati wanda yake tafiya tare da al’adunsu, da kuma yadda koda wane lokaci za a rika tafiya tare da cimma matsaya. Yawancin takardun da yake rubutawa Shugabannin kasa a shekarun da suka gabata, su kan abin yin mahawara  a tsakanin ;yan kasa, ko kuma yin suka akan abubuwan da wasakun suka kunsa amma ko sai dai duk koma menene za ace sau da yawa ko mafi akkasarin lokaci maganganun da suke tafe ne tare abubuwan ci gaba wadanda suka kamata su Shugabannin su rika yi ma wadanda suke mulka wato mafi akasari ko yawansu Talakawa ne.

So da kaunar lamarin ci gaban ilimi

Shi Obasanjo ya  mai da hankaline  akan lamarin ilimi wannan ma wata wata sheda ce da take nunawa a fili dalilin da yasa ya kirkiro Jami’ar Fasaha da ke Bells Ota, Jihar Ogun. An kafa ita Jami’ar ne domin ta samar da ilimi mai nagarta irin na manyan makarantu wanda ya maida hankali kan fasaha da wasu shigo da wasu nau’oi ne na shawarwariin daga karshe ko shakka babu dama duk bukatar bata wuce aga an daukaka fasaha ba ta bangaren na ilim.

Baya da hakan har ma ya kafa wata gidauniya ce wanda duk domin a samu bunkasar lamarin ilimin daga karshe wanda hakan zai samar da tallafin karatu ga ‘ya’yan Talakawa wadanda iyayensu basu da wta hanya da za su dauki nauyin ilimin ‘ya’yansu.

Ko da wane lokaci mu ‘amalar malarsa wadanda suke da ruwa da tsaki kan lamarin daya shafi ilimi bai wuce a samu taiamakon da zai bunkasa ilimin ba, wato kamar mutanen da ke ciukin al’umma irinsu Chief Afe Babalola (SAN), wanda ya malllaki Jami’ar Afe Babalola (ABUAD) da Farfesa Peter Okebukola.

Buhari: Yana ci gaba da lamarin aikin gona da kuma ci gaba

An haifi ranar 17 ga Disamba 1942, shi ma kamar tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo Allah ya bashi damar yin Shugabancin kasa har sau biyu da farko na mulkin soja na biyu kuma farar hula daga shekarar 2015 zuwa 2023. Sai kuma na sojan daga 31 na Disamba 31, 1983 zuwa 27 ga Agusta 27, 1985

Tun bayan daya bar karagar mulki a watan Mayu 2023, Buhari ya dauki rayuwa wadda take da sauki, inda ya koma garin da aka haife shi Daura cikin Jihar Katsina daganan ya koma  Kaduna. Sai dai kuma duk da yake ake  ganin kamar ya b siyasa saboda baya kan mulki, har yanzu yana fada aji ba wata dushewa ya yi ba yana da matukar muhiummanci,bama kamar ta bangaren aikin gona,ilimi,maganar makamashi, da kuma dorewar kula da muhalli.

Tuni aka dade da sanin san a mai mu’amala ne akan aikin noma Buhari  saboda da hakan ya maida hankalinsa kan lamurran aikin gona/ noma.A gonarsa ta Daura ya ci gaba da kiwon dabbobi musamman ma Shanu yanzu kuwa abin ya ci gaba domin har madarar yake samarwa zuwa kasuwanni  a cikin Jihar Katsina.Daliin maida hankalinsa kan aikin gona abode ya kawan da sanin lamarin noma shi ne ke taimakawa wajen bunkasar tattalin arziki da kuma ci gaban karkara.

Idan  ana maganar noma Buhari lamarinsa ya zarce bukatar kan shi kadai.Har yanzu mai goyon bayan tsarin da yayi ne lokacin yana Shugaban kasa na mulkin soja,samar da filayen noma a kasa baki daya tsarin da ake kira da suna NALDA. Authority (NALDA) da kuma kungiyar matasan manoma ta kasa ko kuma  (NYFS).

Wadannan tsare-tsaren ana ci gaba da yin aiki da su inda shi Buhari yake bada shawara ga masu ruwa da tsaki da kuma bibiyarsu kan irin ci gabada suke samu ko ake samu dangane da hakan.

Maida hankalinsa kan taimakawa matasan Nijeriya da uma bunkasa tattalin arzikin  Karkara ba sai da yayi ritaya bane aka fara yin shirin.Makusantan shi sun ce, sau da yawa yaa tuntuba kan lamaurran da suka shafi  tsarin  ci gaban aikin gona ,inda kuam yake tabbatar da cewa ayyukan da ya kirkiro suna ci gaba da bunkasa.

Ta bangare makamashi zamanin mulkin farar hula na Buhari shi ne wanda yasa aka fara babban aiki na jawo iskan gas daga Jihar Edo da kuma bada lasisi ga kananan matatun manfetur a sashen yankin da suke samar da albarkatun main a kasa.

Duk da yake baya mulki amma dai wani abu daya shi ne yana ci gaba da yin mu’amala da kuntubar juna da masu fada aji,inda yake kara basu shawara kan abinda yafi son ganin ya kasance dangane da makamashi, wanda daga karshe hakn zai iya taimakawa bunkasar tattalin arzikin Nijeriya.

Ilimi haka yana daga cikin abubuwan da Buhari yafi baiwa fifiko Buhari.Lokacin da yake Shugaban kasa, ya zuba jar fiye da Naira Tiriliyan1.7 ga manyan  makarantu ta hanyar Asusu ko gidauniyar tallawa ilimi (TETFund).Rahotannin tare da bayanan wadanda suka taimaka masa lokacin yana mulki sun nuna cewar Buhari yana ci gaba da taimakawa Talakawa mazauna karkara wasu abubuwan da zasu taimakawa harkar ilimi a Arewacin Nijeriya, yana samar da guraben karo ilimi ta hanyoyin da babu wani lamari na wala- wala.

Ci gaba da bunkasa lamarin daya shafi ilimi nan ma wani wuri ne da yake nuna sha’awarsa matuka. Buhari ya kafa Hukumar kasa ta kulawa da sauyin yanayi inda ya nada Salisu Dahiru a matsayin babban Shugabanta.Lokacin yana kan mukinsa ana yi ma shi bayani na kan halin da ake ciki dangane da ayyukan da ita hukumar tayi,wato kamar yadda wasu dabarun da zasu taimakawa bangaren noma domiun yin maganin matsalolin da aka iya fuskanta sanadiyar shi sauyin yanayin.

Duk da yake dai shi  Buhari  ba wani abu na mulki yake rike da shi ba, sai dai duk da haka nana yi ma shi kallonana ci gaba da daukarsa da kuma yi masa kallon yana daga cikin tsoffin Shugabannin da ake ci gaba da ganin darajarsu.Ta hanyar aminansa kamar su Adedoyin Salami da Segun Awolowo, ba tare da wata wahala ba sai ya zama shi ma ana damawa da shi ta bangaren tsare tsare na kasa kan aikin gona, taimakawata bangaren taimakawa da kudi yadda al’ummar karkara za su bunkasa rayuwarsu ,ga kuma bunkasa fitar da kaya zuwa kasashen waje. Ci gaba ra kasancewarsa ta bangarorin hakan ya sa aya kawo yadda za a taimakawa bunkasar Nijeriya daga bayan fage.

Bayan ya yi ritaya, Buhari ya yanke shawarar daukar rayuwa mafi sauki ta bada misali musamman ga matasa masu tasowa ta rungumar rayuwa mafi sauk, wato wadda daga karshe za a taimakawa al’umma ne ta hanyar irin rayuwar da yayi wadda ba tada wata daudar da zata sa a rika gudun mutum ya kasance kamar Mujiya idan ta shigo cikin Tsuntsaye . Duk da yake ya bar ofishin Shugaban kasa ana ci gaba da irin nau’oin shin a tafiyar da rayuwa wadda take cikin ci gaban Nijeriya, musamman ma ga bangarori wadanda suka zama suna da matukar muhimmanci ga ci gaban kasa.

Babangida (IBB): Har yanzu yana taimakawa ta bangaren harkokin siyasa duk da yake baya kan mulkin

An haifi ritaya Janar Ibrahim Bdamasi Babangida ranar 17 ga Agusta, 1941, Janar Ibrahim Badamasi Babangida wanda aka fisani da (IBB) ya mulki Nijeriya daga shekarar 1985 har zuwa 1993 inda ya dan sauka daga mulki saboda matsalolin da suka taso dangane da soke zaben Shugaban kasa da aka yi ranar 12 ga Yuni, 1993.

Tun lokacin daya sauka daga mulki Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya dan yi shiru kan wasu lamurra, sai dai kuma har gobe ruwa yana maganin tsafta in ana maganar tafarkin siyasa kowa ya san har gobe yana da tasiri.

Duk da yake ba a san ko yana yin wata harka ta kasuwanci ba, iyalan Babangida’ sun dade da kafa makarantun El-Amin da suke Minna, inda suke ba da ilimi tun daga Firamare zuwa bangaren Jami’a. Haka nan ma da akwai gidan Burodi wanda suka fara yi kafin ya zama shugaban kasa na mulkin soja.

Baya ga wadannan kamfanonin, ana danganta ko alakanta Babangida da yadda ya iya siyasa da kuma wasu harkokin tattalin arziki wadanda ba kowa bane ya sani. Ya taka muhimmiyar rawa wajen kasancewar Olusegun Obasanjo ya zama Shugaban kasa a shekarar 1999.

Duk da yake ya bayyana sa bakinsa kan harkokin siyasa tun yana dan shekara 70, har yanzu dai ruwa yana maganin dauda, idan har ana maganar lamarin siyasar Nijeriya. Lokacin da ake cikin ganiyar zabubbuka gidan sa da ke kan dutse Minna ya zama wuri da ya kasance na neman tubarraki na siyasa da kuma tattalin arziki, saboda wasu suna zuwa wurin ne ba da sanin kowa ba,ko kuma su tafi cikin ayarin jama’a, domin su nemi shawara ko kuma goyon baya.

Akwasu wasu maganganun da ake yi da suke nuna babu wani  wanda ya kasance Shugaban kasar Nijeriya tun daga shekarar 1999 ba tare da ya tuntubi Babangida ta wannan ko waccan.Dalilin da yasa yake ci gaba da zama yana da tasiri abin ya dogara ne kan yadda ya iya siyasa, sai kuma kamar yadda wasiu ke cewa ya kan sa baki wanda hakan kan sa sakamakon zabe yake sauyawa kamar yadda suka ce. Duk da yake dai bai da wani dan takarar da yake cewa shi za’a zaba,wata majiya tace yana taimakawa da kudi da wasu  hanyoyin da za su taimaka. Sai dai kuma kamar yadda majiyar tamu ta nuna

Babangida yana wasu mutanen da suka nakalci siyasa sosai,wadanda suma su kan bashi shawara, ta haka ne kuma yake samun damar nazarin yadda zabe zai iya kasancewa, wanda irin haka ke sa ya sani da kuma fahimtar siyasar Nijeriya kwarai da gaske.

Ta bangaren  tattalin arziki duk da yake ba ataba samun shi kai tsaye ba wajen alakanta wasu kamfanoni da shi ba, sai dai iyalai suna da sha’awar kan lamarin Banki, harkar Mai, gidaje, da kuma kamfanonin sadarwa, suma din ana sa ran wasu amintattu ne ke tafiyar da su.

“Yana da harkokin kasuwanci wasu ma ba za a iya ganewa ko nashi bane,”  cewar wani dan cikin gida kamar yadda ya bayyana. “Yana yin harkokinsa ta hannu aminansa wadanda suke tare tun lokacin da yake mulki, bai kuma yadda ayi ga wuri ga waina.Sai dai kuma ‘ya’yansa suna mamaye lamurran a hankali suna kuma kare muradansu.”

Majiyar ta yi bayanin cewar, “Sai dai idan akwai wani babban dalili, in ba haka ba su barai hakanan a samu ganawa da shi. Saboda sun san irin kirkin da ayke da shi mutumin kirki ne, ba zasu bari har a kai ga bata wata cikin harkokin kasuwancin iyalin ba.”

Ga wadanda suke kusa da iyalansa,Janar Ibrahim Badamasi Babangida bai damu da son wata hatsaniya ba ko yawan magana ba.Sai dai kuma har gobe wani mutum ne wanda ba a isa ace ba ayi da shi ba, a lamarin siyasar Nijeriya, saboda ya ci gaba da kasancewa yana yin hakan,amma dayin taka tsantsan.Tasirin da yake da shi yana  yin amfani a wurare da dama da kuma iya takunsa .

 

Abdulsalami: Shi yafi damuwa ne da gabatar da zabe cikin zaman lafiya da kuma nagarta

An haifi Janar ritaya Abdulsalami Abubakar ranar 13 ga watan Yuni shekarar,1942. Yayi Shugaban kasar Nijeriya na mulkin soja daga shekarar 1998 zuwa 1999 inda kuma ya mika mulki ga zababben Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ranar 29 ga Mayu, 1999.

Bayan daya kammala wa’adin mukinsa ya mika mulki,Abdulsalami kama harkar noma ne inda ya kafa gonar  Maizube da take a Minna, Jihar Neja,ana kiwon Shanu da Jimina.

Yayin da harkar noma ta kasance abinda ya fara yi ne bayan sauka daga mulki, babban abinda ya fi maida hankalinsa kai shi ne bukatarsa ta inganta zaman lafiya, musamman ma zaman lafiya lokacin zabe, duka a gida Nijeriya da nahiyar Afirka.

Janar Abdulsalam ya bada muhimmiyar gudunmau kan lamarin daya shafi shiga tsakani domin zaan lafiya tsakanin kasa da kasa,yafi maida hankali ne kan yin zabe cikin zaman lafiya. ya kuma kasance nagartacce..

Ayyukan na shi har sun zarce Nijeriya saboda ya jagoranci lamarin daya shafi zaman lafiya ta shiga tsakani a kasashen Afirka, inda yake bada goyon bayan kan kan sahihin zabe da hanya mai sauki ta koSaboda ya nuna lamarin na shi da gaske ne ya kafa cibiyar zaman lafiya ci gaba mai dorewa ta Abdulsalami Abubakar a Minna.  Cibiyar tana horarwa na gajeren lokaci da kuma nag aba da haka saboda masu da’awar zaman lamarin kawo zaman lafiya.

Jonathan: Ya mayar da hankai kan zaman lafiya na duniya

An haifi Goodluck Ebele Azikiwe Jonathan ranar 20 ga Nuwamba, 1957. Ya yi shugabancin Nijeriya daga shekarar 2010 zuwa 2015 ya kuma fadi zabe shekara ta 2015 inda tsohon Shugaban kasa na mulkin soja ritaya Janar Muhammadu Buhari ya akada shi a zabe. Shi ne Shugaban kasa na farko wanda ya amince da cewar an kada shi zabe.

Jonathan ya muki Nijeriya lokacin da ake fuskantar matsaloli masu yawa da kuma wahala, da kuma yadda tarihin siyasar Nijeriya yake tattare da ita siyasar wadda ta zama ita ma akwai babbar matsala. Abin da ya sa ya kasance ya bambanta da saura shi ne yadda ya amince ya fadi zabe duk kuwa lokacin yana iya ki amma kuma tun kafin a bayyana sakamakon ya amince da cewa ba shi ne ya samu nasara ba, ya taya Muhammadu Buhari dantakarar Shugaban kasa na APC murnar lashe zaben shekarar 2015.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Nijeriya lamarin daya shafi mulkin farar hula siyasar Nijeriya tattalin arziki a kasashen waje Duk da yake ba kasar Nijeriya duk da yake ba ya ci gaba da lokacin da ya Janar Ibrahim daga shekarar wadanda suke Lokacin yana wadanda suka lokacin yana zaman lafiya abubuwan da Obasanjo Ya a taimakawa kan lamarin daga karshe Nijeriya da ta bangaren ne wanda ya kamar yadda Ta bangaren Obasanjo ya

এছাড়াও পড়ুন:

Amince Wa Al’umma Mallakar Makamai Zai Ƙara Tsananta Rashin Tsaro — IGP

Ya kuma yi watsi da ikirarin da ake yi na cewa ‘yansanda na taimakawa wajen magudin zabe, yana mai bayyana irin wadannan zarge-zarge a matsayin mara tushe, tare da cewa aikin ‘yansanda a lokacin zabe ya takaita ne kawai wajen samar da tsaro da tabbatar da zaman lafiya.

“Mu ba ’yan bangar siyasa ba ne, mu kamar alkalan wasa ne, aikin ‘yansanda ya takaita ne kuma ya ta’allaka ga samar da tsaro a lokacin zabe, gwargwadon yadda ya kamata, ba za mu yi zabe ba, jama’a ne za su kada kuri’a, INEC ta kidaya, muna sa ido.

“Kuma wannan ita ce matsayarmu, sannan kuma hanyar da za a bi domin cimma nasara ita ce, sake sabunta hadin gwiwa tsakanin hukumomi, da suka hada da gwamnatin jiha, INEC, da kungiyoyin farar hula, gami da horas da jami’ai domin tabbatar da sun ci gaba da aikinsu yadda ya dace,” in ji shi.

A nasa bangaren, SGF Akume ya ce sauye-sauyen da gwamnatin shugaban Kasa Bola Tinubu ta bullo da su na shimfida ginshikin dorewar zaman lafiyar kasa da kuma bunkasar tattalin arzikin kasa abin a yaba ne.

Akume wanda babban sakataren harkokin siyasa da tattalin arziki a ofishin SGF, Nadungu Gagare ya wakilta, ya ce dole ne sake duba tsakiyar wa’adi inda zai zama aiki ne na tabbatar da dimokuradiyya, ba al’amuran biki ba.

SGF ta lura cewa Tinubu ya karbi mulki ne a daidai lokacin da tattalin arzikin duniya ya tabarbare da kuma lalacewar kasafin kudi na cikin gida, amma duk da haka a cikin shekaru biyu, gwamnatin ta fara aiwatar da sauye-sauyen tsari a muhimman sassa.

“Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya Cibiyar jijiya ce ta hadin gwiwa tsakanin bangarori daban-daban. A cikin shekaru biyu da suka gabata, mun kara himma wajen daidaita manufofin gwamnati da daidaita su da abubuwan ci gaban kasa; da samar da hadin gwiwa tare da Majalisar Dokoki ta kasa, kungiyoyin farar hula, abokan ci gaba, da gwamnatocin kasa da kasa da kuma tallafa wa tsarin aiwatar da ayyukan ci gaba, ciki har da manyan tsare-tsare da suka hada da tsarin aiwatar da ayyukan ci gaba, ciki har da manyan tsare-tsare da suka hada da tsarin aiwatar da ayyukan ci gaba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ganduje Ya Ajiye Shugabancin Jam’iyyar APC
  • Rundunar Sojin Nijeriya Ta Tabbatar Da Kisan Jami’anta A Kaduna Da Neja
  • Amince Wa Al’umma Mallakar Makamai Zai Ƙara Tsananta Rashin Tsaro — IGP
  • An tallafawa iyalan ‘yan sanda da Naira miliyan N13.4m a Borno
  • Yadda aka kama mai garkuwa da mutane yana tsaka da cin kasuwar shanu a Neja
  • Yadda na kuɓuta daga harin Filato — Wani mutum
  • Shugabannin Sin Da Mozamqiue Sun Mikawa Juna Sakon Taya Murnar Cika Shekaru 50 Da Kafuwar Huldar Diflomasiyya
  • Gwamnatin Gombe za ta biya ’yan fansho Naira biliyan 6.6 kuɗin ritaya
  • DAGA LARABA: Ko Najeriya Na Da Kudin Renon Sabbin Jihohi?