Sarkin Zazzau ya ziyarci iyalan ’yan ɗaurin auren da aka kashe a Filato
Published: 28th, June 2025 GMT
Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ya ziyarci iyalan ’yan ɗaurin aure da aka kashe a Jihar Filato.
Tun da farko, Hakimin Basawa, Haruna Abubakar ne, ya wakilci Sarkin lokacin da lamarin ya faru, saboda Sarkin ya yi tafiya.
Bom ya kashe mutum hudu da raunata 21 a Yobe Ganduje ya yi murabus daga shugabancin jam’iyyar APCSarkin, ya bayyana baƙin cikinsa bisa wannan mummunan lamari, inda ya roƙi iyalan da su ɗauki wannan a matsayin ƙaddara.
Ya yaba da yadda suka yi haƙuri kuma suka bar komai ga hukuma, ba tare da ɗaukae doka a hannunsu ba.
Sarkin ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Kaduna na ƙoƙarin ganin an bi wa waɗanda abin ya shafa haƙƙinsu.
Ya ƙara da cewa zaman lafiya da haƙuri su ne mafita ga duk wata matsala, kuma hakan zai kawo ci gaba a tsakanin al’umma.
A yayin ziyarar, Sarkin ya samu rakiyar wasu daga cikin ’yan majalisarsa da hakimai.
Ya sake roƙon jama’a da su ci gaba da zaman lafiya tare da miƙa lamarin ga Allah.
Da yake magana a madadin iyalan garin, Mallam Muhammadu Dan Bami, ya gode wa Sarkin bisa ziyarar da ya kawo, tare da bayyana cewa mutanen garin masu bin doka da son zaman lafiya ne.
Daga ƙarshe, ya roƙi Sarkin da ya taimaka wajen ganin gwamnati ta cika alƙawarin da ta ɗauka na bi masu haƙƙinsu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Ɗaurin Aure Sarkin Zazzau ziyara
এছাড়াও পড়ুন:
Soja ya soka wa ɗan sanda wuƙa har Lahira a Taraba
Wani kurtun soja ya soka wani ɗan sanda mai mukamin Constable, Aaron John da wuƙa har lahira a garin Jalingo, hedikwatar Jihar Taraba.
Kakakin ’yan sanda na jihar, James Lashen, ya ce wannan mummunan al’amari ya faru ne da misalin karfe 9 na dare a ranar Litinin, a unguwar Mayo-Goyi, da ke gefen birnin Jalingo.
Lashen ya bayyana cewa marigayi John ya samu kiran gaggawa daga wasu mazauna yankin dangane da sabani da suka samu da sojan.
A yayin da yake kokarin warware rikicin, sai sojan mai suna Dauda Dedan, ya soka masa wuƙa.
Ya ce, “Mun samu rahoton lamarin daga hedikwatar Brigade ta 6 ta Rundunar Sojin Najeriya, da tabbacin cewa za a kamo sojan da ya tsere domin fuskantar hukunci,” in ji Lashen.
Ya ƙara da cewa rundunar soji ta fara bincike kan lamarin, tare da tabbatar wa ’yan sanda cewa za su haɗa kai wajen kamo wanda ake zargi.
“Sojoji da ’yan sanda na aiki tare. Mun kai ziyara har gidan sojan, kuma za mu tabbatar an kama shi domin ya fuskanci hukunci daidai da abin da ya aikata,” in ji Lashen.
Ya jaddada cewa dangantaka tsakanin sojoji da ’yan sanda a jihar Taraba tana da kyau kuma babu wata matsala a tsakaninsu.