Ganduje ya yi murabus daga shugabancin jam’iyyar APC
Published: 27th, June 2025 GMT
Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi murabus daga shugabancin jam’iyyar.
Murabus ɗin nasa ya fara aiki nan take.
Sojoji sun yi wa ’yan bindiga luguden wuta a Neja ’Yan sanda sun kama ɓarayi 5, sun ƙwato kuɗi da makamai a GombeGanduje, wanda tsohon Gwamnan Jihar Kano ne, ya bayyana rashin lafiya a matsayin dalilin da ya da ya ajiye muƙaminsa.
Ganduje ya zama Shugaban APC a watan Agustan 2023, a lokacin da jam’iyyar ke fama da rikicin cikin gida.
Lokacin da ya kwashe a matsayin shugaban jam’iyyar na cike da cece-kuce da suka.
Dalilin murabus ɗinsaKo da yake Ganduje ya ce rashin lafiya ce ta sa ya yi murabus, wasu majiyoyi sun bayyana cewa rikicin siyasa a cikin jam’iyyar ne suka tilasta masa ajiye muƙamisa.
Haka kuma, an danganta murabus ɗinsa da zarge-zargen almundahana da karkatar da kuɗaɗe.
Wasu ’ya’yan jam’iyyar sun koka cewa ofishinsa na tilasta musu biyan kuɗi da yawa, musamman masu neman tikitin takara a Abuja.
Tasirin murabus ɗinsa ga jam’iyyar APCMurabus ɗin Ganduje babban sauyi ne ga shugabancin jam’iyyar APC.
Yanzu haka, mutane da dama suna jiran su ji yadda jam’iyyar za ta shawo kan wannan lamari.
Har yanzu jam’iyyar APC ba ta fitar da wata sanarwa kan murabus ɗinsa ba.
Matsalolin da suka shafi Ganduje kan shugabancin jam’iyyarA farkon shekarar 2024, wata kotu a Jihar Kano ta hana Ganduje ci gaba da kiran kansa da ɗan jam’iyyar APC, bayan wasu shugabannin jam’iyyar sun shigar da ƙara a kansa.
Daga baya kuma, wata kotu a Abuja ta yi watsi da ƙarar da wasu ke yi don a tsige shi daga shugabancin jam’iyyar.
Zamanin Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar cike yake da rikice-rikice, kuma murabus ɗinsa yanzu zai sanya dasa ayar tambayoyi domin neman wasu amsoshi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Murabus shugabancin jam iyyar murabus ɗinsa jam iyyar APC
এছাড়াও পড়ুন:
An Naɗa Farfesa Adamu Muƙamin Mataimakin Shugaban Jami’ar Yakubu Gowon, Abuja
Gwamnatin Tarayya ta naɗa Farfesa Mathew Adamu a matsayin sabon mukaddashin Mataimakin Shugaban Jami’ar Abuja, wadda aka sake wa suna zuwa Jami’ar Yakubu Gowon. Farfesa Adamu zai maye gurbin Farfesa Patricia Manko Lar, wadda ta riƙe wannan muƙamin na tsawon watanni shida tun daga Fabrairu 2025. Farfesa Adamu zai fara aiki daga ranar Litinin, 11 ga Agusta, 2025, inda zai riƙe wannan muƙami na tsawon watanni uku.
Farfesa Adamu ƙwararren masani ne a fannin likitancin dabbobi wanda ya fara karatunsa da digiri daga Jami’ar Maiduguri a 1998, sannan ya samu digirin digirgir a Jami’ar Pretoria, Afrika ta Kudu a 2012, an ɗaga darajar shi zuwa cikakken Farfesa a 2019.
Farfesa Yilwatda Ya Zama Sabon Shugaban Jam’iyyar APC Na Ƙasa Gwamnatin Tarayya Za Ta Farfaɗo Da Noman Dabino – ShettimaA cikin shekaru 27 na aikinsa, Farfesa Adamu ya yi fice a koyarwa, da bincike, da gudanarwa a fannin ilimi. Ya taɓa aiki a matsayin likitan dabbobi na hukumar Youth Corps, sannan ya samu damar koyarwa a Jami’ar Noma ta Makurdi inda ya kai matsayi na Farfesa. Haka kuma ya rike muƙamai da dama ciki har da Mataimakin Tsangaya na Kwalejin Likitocin Dabbobi.
Sanarwar ta bayyana cewa sabon VC zai tallafa wa Kwamitin Gudanarwa don kammala zaɓin cikakken Mataimakin Shugaban Jami’a bisa ga ƙa’idojin doka, kuma an gode wa Farfesa Lar kan jajircewarta a lokacin da ta riƙe mukamin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp