Ribas: Duk wani rikici tsakanina da Fubara ya ƙare – Wike
Published: 27th, June 2025 GMT
Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya tabbatar da cewa tattaunawar da suka yi da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ta kawo ƙarshen duk wata rigima da ke tsakaninsa da Gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Siminalayi Fubara.
A daren ranar Alhamis ne Shugaba Tinubu, ya jagoranci wani zaman sulhu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, tsakanin Wike da Gwamna Fubara da kuma wasu daga cikin ’yan majalisar Ribas da aka dakatar.
Bayan ganawar, Wike ya yi magana da manema labarai, inda ya tabbatar da kawo ƙarshen rikicinsa da Fubara.
“Dukkaninmu mun amince mu yi aiki tare da Gwamna, kuma shi ma ya amince zai yi aiki da mu. Dukkanninmu ’yan gida ɗaya ne.
“Rigimarmu ta daɗe, amma zamanmu na ranar Alhamis ya kawo ƙarshenta. Dama ɗan Adam yana iya samun saɓani, amma daga baya a sasanta.”
Ya ƙara da cewa: “Kuma yau ne muka kammala komai, mun zo mun shaida wa Shugaban Ƙasa cewa mun daidaita. Don haka a gare ni, komai ya wuce.”
Wike, ya kuma yi kira ga mabiyansa da su kwantar da hankali tare da haɗa kai don ciyar da Ribas gaba.
“Ina kira ga kowa da kowa da mu haɗa kai da sauran jama’a. Babu sauran rigima, babu wani abu da za a sake yin faɗa a kai.”
Abin da rikicin ya haifarA baya dai rikicin siyasa a Jihar Ribas, ya haifar da barazanar tsige Gwamna Fubara a watan Oktoban 2024, yayin daga bisani Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a watan Maris a jihar
Sai dai yanzu ɓangarorin sun ce komai ya wuce, kuma za su ci gaba da aiki tare domin ci gaban jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Fubara Saɓani Siyasa
এছাড়াও পড়ুন:
EFCC ta kama ’yan damfara a ɗakin karatun Obasanjo
Jami’an Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), sun kai samame a Ɗakin Karatun Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta, a Jihar Ogun, inda suka kama wasu matasa da ake zargin ’yan damfara ne.
Samamen ya faru ne da safiyar ranar Lahadi a sashen otal na ɗakin karatun.
’Yan bindiga sun kashe gomman mutane a ƙauyukan Sakkwato An ɗaure tsohon Firaminista Succes Masra shekaru 20 a ChadiGidan Obasanjo na musamman yana cikin harabar ɗakin karatun.
Wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, ya nuna yadda wasu matasa ke gudu domin ka da EFCC ta kama su.
Rahotanni sun ce jami’an EFCC sun ƙwace sama da motoci 20 tare da wasu kayayyaki masu daraja.
Wani jami’in EFCC ya shaida wa Aminiya cewa samamen ya samo asali ne daga Ofishin EFCC na Legas.
Daraktan Kamfanin OOPL Ventures, Mista Vitalis Ortese, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa suna ƙoƙarin samun ƙarin bayani daga EFCC.
Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya ce zai yi bincike kafin ya yi wa manema labarai ƙarin bayani.
Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan jami’an EFCC daga Ofishin Ibadan suka kama mutum 56 da ake zargi da aikata damfara a Intanet a wani otal mai suna K-Hotel da ke Itori, a Jihar Ogun.
An kama ɗaya daga waɗanda ake zargin da bindigogi guda biyu.
EFCC ta kuma ƙwato motoci shida masu tsada, wayoyin salula 89, kwamfutoci, da wasu takardu.
Hukumar ta ce nan ba da jimawa ba za ta gurfanar da dukkanin waɗanda ta kama a gaban kotu.