Pezeshkian: Babu Batun Tattaunawa Da Amurka A Karkashin Matsin Lamba
Published: 12th, March 2025 GMT
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi kakkausar suka ga matakin da gwamnatin Trump ya dauka kan Iran, yana mai bayyana cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba Ukraine ba ce, kuma ba za ta yi shawarwari da Amurka bisa barazana ko tilasci ba.
“Dole ne mu kiyaye dangantaka da duniya. Ba ma son mu yi sabani ko jayayya da kowa, amma hakan ba yana nufin za mu durkusa cikin wulakanci a gaban kowa ba,” in ji Pezeshkian yayin wani taron kungiyar ‘yan kasuwan Iran a Tehran a ranar Talata.
“Muna iya mutuwa da daraja, amma ba za mu taɓa rayuwa cikin kunya da kaskanci ba.”
Pezeshkian ya yi watsi da abin da ya bayyana a matsayin wa’adi daga Donald Trump, yana mai nuni da wata wasika da aka ce shugaban Amurka ya aike zuwa Iran.
Wasikar ta bukaci Tehran da ta dakatar da shirye-shiryenta na nukiliya da makamai masu linzami da kuma daukar wasu matakai domin samun sassaucin takunkumi.
Ya soki Trump da rashin mutunta takwaransa na Ukraine, Volodymyr Zelensky, yayin da ya matsa masa lamba kan ya amince da wata yarjejeniya da Rasha.
Shugaban na Iran ya ce halin da Trump ya nuna a ganawarsa da Zelensky a fadar White House abin kunya ne.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Araghchi : Iran a shirye take ta shiga tattaunawa da Turawa bisa mutunta juna
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Tehran a shirye take ta shiga tattaunawa da kasashen Turai bisa mutunta juna.
A wata tattaunawa ta wayar tarho, Araghchi da Ministan Harkokin Wajen Netherlands Caspar Veldkamp sun tattauna hanyoyin inganta alakar juna da sabbin abubuwa dake faruwa a yankin da na kasa da kasa.
Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya nanata tsarin kasar na kulla kyakkyawar alaka ta diflomasiyya da kasashen.
Iran da kasashen Turai dai na tattaunawar ba-zata kai a kai tun shekara ta 2021, shekaru uku bayan da Amurka ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar iran – tare da maido da takunkumin da Washington ta kakaba wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
bangarorin kasashen Turai da suka shiga yarjejeniyar nukiliya – Birtaniya, Faransa da Jamus – sun kasa cika alkawarin da suka dauka na dawo da Washington cikin yarjejeniyar.