Hamas ta yi maraba da matakin Yemen na haramtawa jiragen ruwan Isra’ila shiga teku
Published: 13th, March 2025 GMT
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi maraba da matakin da kasar Yemen ta dauka na haramtawa jiragen ruwan Isra’ila shiga tekun Bahar Maliya
Bayan sanarwar da kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen ta fitar na cewa za ta dawo da haramcin da ta yi wa jiragen ruwan Isra’ila na tsallakawa tekun Bahar Rum, Hamas ta fitar da sanarwa inda ta yi maraba da matakin.
ta bayyana wannan mataki a matsayin wanda ke nuna hakikanin matsayin al’ummar Yemen da gwamnatin kasar na goyon bayan gwagwarmayar al’ummar Falastinu.
Har ila yau kungiyar ta yi kira ga dukkanin kasashen Larabawa da na Musulunci da kuma ‘yantatun kasashe a duniya da su kara zage damtse wajen matsin lamba ga ‘yan mamaya da magoya bayansu da su kawo karshen hare-haren wuce gona da iri kan Gaza, da dage shingen da aka yi musu, da kuma tabbatar da isar da kayayyakin jin kai.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Iran Ta Jaddada Wajabcin Hukunta Gwamnatin Mamayar Isra’ila Dangane Da Ta’addancinta Kan Iran
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta jaddada cewa Ta’addancin yahudawan sahayoniyya kan Iran laifi ne na yaki da ya zama wajibi duniya ta yi mata hukunci a kai
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya yi kira da a dorawa mahukuntan yahudawan sahayoniyya alhakin munanan laifukan da suka aikata a kan al’ummar Iran, musamman a lokacin da ake ci gaba da kai hare-hare a birnin Tehran fadar mulkin kasar da sauran garuruwan kasar ta Iran.
A wani sakon da ya wallafa a dandalin X a yau Asabar, Baqa’i ya ce, “Harin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai a asibitoci da kurkukun Evin a ranar 24 ga Yunin wannan shekara ta 2025, wanda ya yi sanadin shahadar fararen hula da ma’aikata da kuma masu shigewa da yawansu ya kai mutane 79, yana cikin laifukan yaki da kuma keta dokar jin kai ta kasa da kasa.”
Ya yi nuni da cewa, harin ya afku ne a daidai lokacin da iyalan fursunonin ke taruwa domin ziyartar ‘yan uwansu, kuma sun makale a karkashin baraguzan ginin inda suka yi shahada sakamakon harin wuce gona da iri na jirgin saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila.