Kashim Shettima Ya Tafi Habasha Ziyarar Aiki
Published: 26th, June 2025 GMT
Shettima zai kuma ziyarci manyan masana’antu da gonaki a sassa daban-daban na Habasha.
Masana’antun sun haɗa da Adama Industrial Zone, Mojo Poultry Farm, Shera Dibandiba Mojo Family Farm, Lume Avocado Nursery, da Bishoftu Pea Youth Farm.
Wannan ziyara na da nufin ƙarfafa dangantaka tsakanin Nijeriya da Habasha, musamman a fannin noma da masana’antu.
Firaminista Abiy zai kuma shirya wata liyafa ta musamman a Fadar Shugaban Kasar domin girmama Shettima da tawagarsa, a matsayin alamar ƙarfafa dangantakar diflomasiyya da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu.
Nijeriya da Habasha na da daɗaɗɗen tarihin aiki tare, musamman a fannonin tsaro, kiyaye zaman lafiya da kuma haɗin gwiwar tattalin arziƙi.
Wannan ziyara na da burin ƙarfafa wannan dangantaka da kuma samar da damar haɗin gwiwa a fannin sauyin yanayi, wadatar abinci, da ci gaban masana’antu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Ziyara
এছাড়াও পড়ুন:
Jami’an tsaro sun ƙaddamar da shirin murƙushe ’yan bindiga a Kaduna
Jami’an tsaro a Jihar Kaduna, sun fara gudanar da babban samame domin kawar da ’yan ta’adda da ’yan bindiga a wasu ƙananan hukumomin jihar.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ya ce an gudanar da aikin tare haɗin gwiwar sojoji, DSS, NSCDC, KADVS, da kuma ƙungiyoyin sa-kai da mafarauta.
Tukur Mamu ya karbi N50m daga kuɗin fansar harin jirgin kasan Kaduna – DSS Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000Aikin ya shafi ƙananan hukumomin Makarfi, Hunkuyi da Ikara.
Rundunar ta ce manufar wannan samame shi ne “share dukkanin maɓoyar miyagu, rushe sansanonin da suka kafa, da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.”
Wannan mataki ya biyo bayan umarnin Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, wanda ya umarci dukkanin rundunonin ’yan sanda a faɗin ƙasar nan su ƙara ƙaimi wajen yaƙi da aikata laifuka.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Rabiu Muhammad, ya tabbatar wa jama’a cewa jami’an tsaro za su ci gaba da matsa wa miyagu lamba.
Ya ce za su ci gaba da yin gwiwa da rundunonin tsaro domin tabbatar da tsaro a jihar.