Abin Da Ya Sa Muke Ci Gaba Da Tuntubar Kasar Sin A Kai A Kai
Published: 27th, June 2025 GMT
Taron dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya na lokacin zafi na Davos, wanda aka gudana a tsakanin ranar 24 zuwa ranar 26 ga watan nan da muka ciki, a birnin Tianjin na kasar Sin, ya samu halartar wakilai kimanin 1800 daga kasashe da yankuna sama da 90, adadin da ya kai koli cikin tarihi. Kamar yadda babban daraktan dandalin Davos Borge Brende ya bayyana, “in muka duba yanayin kasashen duniya, za a gane cewa, wakilai a fannonin masana’antu da kasuwanci na kasashe da dama, suna fatan zuba jari a kasar Sin, tare da zurfafa hadin gwiwar cinikayya dake tsakaninsu da kasar Sin.
A halin yanzu, kasuwannnin kasar Sin suna ci gaba da samun kyautatuwa da karuwa, lamarin da ya samar da damammaki ga bunkasar hadin gwiwar cinikayya a tsakanin kasa da kasa. Ci gaba da yin kirkire-kirkire a kasar Sin, ya samar da sabon karfi na neman samun bunkasa. A ciki kuma, bunkasar fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam ta AI ta janyo hankulan jama’a cikin taron Davos. Masana na ganin cewa, idan muka yi amfani da fasahohin da abin ya shafa kan aikin nazarin sabbin kayayyaki, zai ninka saurin gudana da ayyukanmu sau 100 har ma zuwa sau 1000. Kuma kasar Sin za ta taka muhimmiyar rawa cikin wannan babban sauyi.
Haka kuma, cikin farkon watanni 5 na bana, an kafa sabbin kamfanoni masu jarin waje guda 24,018 a cikin kasar Sin, adadin da ya karu da kaso 10.4 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. Kamfanonin kasashen duniya sun nuna fatansu na hada kai da kasar Sin. Kamar yadda tsohon firaministan kasar Burtaniya Tony Blair ya bayyana a yayin taron Davos cewa, “ya kamata a ci gaba da tuntubar kasar Sin a kai a kai.” (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: a kasar Sin
এছাড়াও পড়ুন:
Shirin Iskar Gas Na CNG Abin A Yaba Wa Shugaba Tinubu Ne -Shugaban IPMAN Na Ƙasa
Garima wanda har ila yau shi ne, and Jakadan Gwandu ya yi nuni da cewa, cibiyoyin na CNG da gwamnatin taraya ta samar a jihohin Kano da Kaduna, za su taimaka wajen samar da Iskar Gas ɗin a Arewa ta tsakiya da kuma Arewa ta Gabas.
Kazalika ya ce, samar da cibiyar a jihar Sokoto wadda take kusa da Jamhuriyyar Nijar, hakan zai ƙara bunƙasa tattalin arzikin jihar
Garima ya sanar da cewa, Iskar Gas ɗin ta CNG tsafatattaciya ce kuma bata da wani tsada, inda kuma ta rage gurɓatar muhalli.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp