Ronaldo ya tsawaita kwantaraginsa a Al Nassr
Published: 27th, June 2025 GMT
Cristiano Ronaldo ya sanya hannu kan yarjejeniyar tsawaita kwatiraginsa da shekara biyu a ƙungiyar Al Nassr da ke buga gasar Saudi Pro League.
Wannan dai na nufin kyaftin din na tawagar Portugal zai ci gaba da zama a ƙungiyar har 2027, lokacin da zai kai shekara 42 a duniya.
Sheikh Dahiru Bauchi ya cika shekara 101 a duniya Gwamnatin Katsina ta amince da ƙidayar almajirai, makarantun IslamiyyaAl-Nassr ta bai wa Ronaldo kwantiragi mafi tsada a tarihin wasanni, inda ya rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniyar fam miliyan 24.
Ɗan wasan mai shekara 40 ya je Al Nassr ne a Disamban 2022, bayan raba gari da Manchester United.
A ƙarshen watan Yunin da muke ciki ne kwantiraginsa na farko zai ƙare a ƙungiyar da ke Saudiyya.
Bayan sanya hannun ɗan wasan wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or har sau biyar ya ce “An buɗe sabon babin buri da sha’awar ci gaba da kafa tarihi tare” a shafinsa na Instagram.
Duk da cika shekaru 40, Ronaldo ya ci gaba da taka rawar gani, inda a kakar wasan da ta gabata ya zura kwallaye 35 a wasanni 41 da ya buga a duk gasa, lamarin da ya ba shi damar karewa a matsayin dan wasan da ya fi zura kwallaye a gasar Saudi Pro League a shekaru biyu ke nan a jere.
Ronaldo wanda ke da burin kaiwa kwallaye 1,000, ya zira kwallaye 99 a cikin wasanni 111 da ya buga tun bayan zuwansa Al Nassr, inda ya kawo yanzu ya ci kwallaye 938 jimilla a tarihinsa na tamaula
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Afuwar Tinubu za ta buɗe hanyar ci gaba da aikata miyagun laifuka — Atiku
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya nuna damuwa kan yadda shugaba Bola Tinubu ya yi wa wasu mutane afuwa, ciki har da waɗanda suka aikata manyan laifuka.
A cikin saƙon da Atiku ya wallafa a shafinsa na X, ya ce ana yin afuwa ne ga waɗanda aka yi wa rashin adalci ko waɗanda suka nema gafara bayan sun shafe wani lokaci a gidan yari.
Yajin Aikin ASUU: Ba za mu biya duk wanda bai yi aiki ba — Gwamnatin Tarayya ’Yan sanda sun ceto mutum 10 daga hannun ’yan bindiga a KadunaYa ce a wannan karon an yi wa masu safarar ƙwayoyi, masu garkuwa da mutane, masu kisan kai, da kuma masu cin hanci da rashawa afuwa.
Atiku, ya ce abin mamaki ne yadda gwamnati ke yafewa irin waɗannan mutane, a daidai lokacin da ƙasar ke fama da matsalar tsaro da lalacewar tarbiyya, musamman tsakanin matasa masu shan miyagun ƙwayoyi.
Ya ce bincike ya nuna cewa kashi 29 na waɗanda aka yi wa afuwa suna da alaƙa da hakrar miyagun ƙwayoyi, yayin da Najeriya ke ƙoƙarin wanke sunanta a idon duniya kan yaƙi da miyagun ƙwayoyi.
Atiku, ya ce maimakon wannan afuwa ta zama darasi ga masu laifi, ta zama hanyar durƙusa da ɓangaren shari’a da jami’an tsaro da ke sadaukar da rayukansu wajen kamawa da hukunta masu aikata laifuka.
Ya ƙara da cewa idan gwamnati ta fara yafe wa masu laifi, hakan zai rage ƙimar shugabanci kuma ya ƙarfafa wa masu aikata laifuka su ci gaba da aikata su.
Atiku ya jaddada cewa Najeriya tana buƙatar shugabanci na gari wanda zai tabbatar da adalci a shari’a, ba tare da nuna bambanci ba.