NDLEA ta kafa cibiyar kula da masu shaye-shaye a Yobe
Published: 27th, June 2025 GMT
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta kafa karamar cibiyar kula da muggan kwayoyi a Damaturu babban birnin jihar Yobe.
Kwamandan hukumar a Jihar, Abdulazeez Ogunboye ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Damaturu a wani bangare na bikin ranar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta duniya ta shekarar 2025.
Ogungboye ya kara da cewa cibiyar wacce tun daga lokacin da ta fara aiki na daya daga cikin nasarorin da hukumar ta samu a jihar.
“An shigar da mutane tara da suke ta’ammali da muggan kwayoyi a cibiyar, daga cikin su an samu nasarar gyara halayyar mutum takwas halayyar su, an sallame su tare da sake haduwa da iyalansu, yayin da daya ke ci gaba da karbar hoton gyaran hali.
“Daya daga cikinsu yanzu haka ya samu tallafin fara gudanar da harkokin kasuwanci don dogaro da kai tare da watsar da waccar mummunar dabi’a ta ta’ammali da muggan kwayoyi,” in ji Ogunboye.
Kwamandan ya ce bisa la’akari da tsadar ayyuka a cibiyar, hukumar ta hada kai da masu hannu da shuni a jihar domin taimaka wa a wannan kokarin gyaran halim masu ta’ammali da kwayoyin.
Kwamandan ya kuma shawarci masu shaye-shaye a kananan hukumomi 17 na jihar da su tuntubi kwamandojin shiyya na hukumar da ke kusa da su kan yadda za su shiga wurin, wanda ya ce shi ne irinsa na farko a tarihin jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Miyagun Kwayoyi
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Cutar amosanin jini wacce aka fi sani da cutar sikila na cigaba da barazana ga rayukan masu dauke da ita.
Wannan cuta na saka masu ita da ‘yan uwan su cikin halin ha’ula’i, a wasu lokutan ma tana haifar da rasa rayukan wasu dake dauke da ita.
Rahotannin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) sun nuna cewa, kusan yara 300,000 ne ake haifa da cutar Sikila a duk shekara a fadin duniya, inda yankin Kudu da Sahara a Afirka ke dauke da kashi 75% na wannan yawan.
A Najeriya kadai, ana kiyasta cewa fiye da yara 150,000 ake haifa da cutar Sikila a kowace shekara — hakan ya sa Najeriya ke da mafi yawan masu fama da cutar Sikila a duniya.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan cutar amosanin jini don gano yadda masu fama da ita ke ji a rayuwar su.
Domin sauke shirin, latsa nan