Mai magana da yawun rundunar ‘ƴansandan jihar, Abubakar Sadiq ya ce; tuni jami’ansu sun je unguwar da gidan yake amma kafin su karasa tuni ‘ƴan bindigar sun tafi da Janar Tsigan.

Sai dai ya bayyana cewar jami’an tsaro suna aiki ba dare ba rana tare da haɗin guiwa da masu ruwa da tsaki domin kamo ‘yan bindigar.

A wani ci gaban kuma, rundunar ‘ƴansandan jihar ta Katsina ta kama wasu mutane 45 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a jihar.

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Yansanda Garkuwa Janar Tsiga

এছাড়াও পড়ুন:

Rukunin Karshe Na Alhazan Jigawa Ya Tashi Zuwa Kasa Mai Tsarki

Rukunin ƙarshe na mahajjatan Jigawa 368 ya tashi daga Filin Jirgin Sama na Nuhu Muhammadu Sunusi zuwa Saudiyya don aikin hajjin shekarar 2025.

A wata hira da aka yi da shi a Radio Nigeria kafin tashinsu a daren Laraba, Darakta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya bayyana cewa rukunin ƙarshe na mahajjatan 368 sun fito ne daga ƙananan hukumomin Birnin Kudu, Buji, da Taura na jihar.

A cewarsa, wannan rukunin ƙarshe ya haɗa da Amirul Hajj na jihar, malamai  masu wa’azi, wasu jami’an shiyyoyi da cibiyoyi, da kuma wasu jami’an hukumar.

Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana cewa, jihar ta kammala aikin tantance mahajjata cikin nasara ba tare da wata tangarda ba.

Ya yabawa Gwamnan jihar, Malam Umar Namadi, bisa goyon baya da haɗin kai da ya bayar ga hukumar.

Darakta Janar ɗin ya kuma yi kira ga sauran mahajjatan Najeriya da ba a ɗauka ba su ƙara haƙuri tare da ci gaba da karanta littattafan da aka basu lokacin bita da shirye-shiryen hajji a jiharsu.

A jawabin bankwana da ya gabatar a filin jirgin sama, Gwamna Umar Namadi ya shawarci mahajjatan da su yi addu’a don jiharsu da ƙasar baki ɗaya.

Namadi ya kuma ja hankalinsu da su bi dokokin da ƙasar Saudiyya ta shimfiɗa.

Wasu daga cikin mahajjatan da suka yi magana da Radio Nigeria kafin tafiyarsu sun gode wa Allah da ya basu damar zuwa kasa mai tsarki domin gudanar da aikin hajjin bana.

Sun yabawa shugabannin hukumar kula da jin daɗin mahajjata ta jihar Jigawa bisa tanadin abinci da abin sha da suka yi musu yayin da suke sansanin Alhazai da filin jirgi.

Mahajjatan sun bayyana jin daɗinsu da yadda aka tsara wa’azi tare da yabawa jami’an hukumar da yadda suka kula da su a sansanin Alhazai.

Radio Nigeria ya ruwaito cewa, jami’an hukumar shige da fice, kwastam, da NDLEA ne suka tantance mahajjatan tare da jakunkunansu masu nauyin kilo 8.

 

Usman Muhammad Zaria.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Faransa
  • An ceto matar da aka yi garkuwa da ita, da kama mutum 2 a Yobe 
  • An kama wani matashi da ya yi shigar mata a Adamawa
  • An yi Jana’izar Shugaban Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Ƙasa a Zariya
  • Rukunin Karshe Na Alhazan Jigawa Ya Tashi Zuwa Kasa Mai Tsarki
  • Sin Tana Da Karfi Wajen Tinkarar Hadari Da Kalubale A Fannoni Daban Daban
  • Jihar Jigawa Za Ta Sayi Motoci 36 Ga Mambobin Kungiyar NURTW
  • Malamai sun gindaya sharaɗi kafin janye yajin aiki a Abuja 
  • Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran Ya Ce: Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ba Ta Da Alkiblar Siyasa
  • Hare-Haren Wuce Gona Da Irin Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Janyo Shahadan Falasdinawa Masu Yawa