HausaTv:
2025-11-03@21:34:47 GMT

 Fiye Da  Falasdinawa 50 Ne Su Ka Yi Shahada A Yau Alhamis

Published: 22nd, May 2025 GMT

Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa; Daga safiyar yau Alhamis zuwa yanzu adadin falasdinawan da su ka yi shahada sun haura 50.

Kididdigar ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta bayyana cewa  a cikin sa’oi 24 da su ka wuce an kai shahidai 107 zuwa asibitoci daga cikinsu da akwai wasu shahidai 3 da aka fito da su daga cikin baraguzai; haka nan kuma wasu mutanen da adadinsu ya kai 247 sun jikkata.

Ya zuwa yanzu adadin wadanda su ka yi shahada tun daga ranar 7 ga watan Oktoba 2023 zuwa yanzu, sun kai dubu 53,762. Sai kuma wadanda su ka jikkata sun kai 1222, 197.

Daga sake dawo da yaki akan alummar Gaza, a ranar 18 ga watan Maris, adadin wdanda su ka yi shahada sun kai 3,613, sai kuma wadanda su ka jikkata da su ka kai 10,156.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta kuma ce, da akwai wani adadi mai yawa na shahidai da suke a karkashin baraguzai da rashin kayan aiki ya hana masu aikin ceto isa gare su.

Adadin kananan yaran da su ka yi shahada tun daga fara yakin, fiye da shekara daya da rabi, sun kai 16,503.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Wadi Al-Salam: Maƙabartar Musulmai Mafi Girma A Duniya

Imam Ali shi ne halifan Annabi Muhammad na hudu a mahangar Ahlussunnan, amma mabiya mazhabar Shi’a na daukar sa a matsayin na farko daga cikin imamansu 12.

Wannan ya sanya akasarin mabiya Shi’a na Iraki kan bukaci a binne su a makabartar, kuma sanadiyyar saukin sufuri a zamunnan baya-bayan nan, wasu mabiya Shi’a daga kasashen duniya kan so a binne su a makabartar.

Tsarin makabartar ya kasance cakuduwa ce ta gine-ginen hubbarai irin na zamanin baya, da hanyoyi masu tsuku da suka ratsa ta cikinta da kuma wasu wurare da ake yi wa kallon masu tsarki.

 

Me ya sa ake kiran makabartar Wadi al-Salam?

Ana kiran makabartar da sunan Wadi al-Salam, wato ‘kwarin aminci’ ne saboda dalilai na tarihi da dama.

Dalilai na addini: Ana yi wa makabartar daukar mai daraja, tare da imanin cewa wadanda ke kwance a cikinta na cikin rahama.

Alaka da Imam Ali: Makabartar tana makwaftaka da kabarin Imam Ali bin Abi Talib a birnin Najaf, wanda hakan ya sa Musulmai, musamman mabiya akidar Shi’a ke girmama ta kuma suke kwadayin ganin an binne su a cikinta.

Girma: Makabartar ta kasance mafi girma a duniya, inda ta mamaye wuri mai girman gaske, kunshe da miliyoyin kaburbura, inda ta zamo tamakar wani birni na mamata.

Ziyara: Masu ziyara zuwa birnin Najaf, mai tsarki ga mabiya akidar Shi’a sukan bi ta cikin makabartar tare da karanta Fatiha da kuma yin addu’o’in samun rahama ga wadanda ke kwance, lamarin da ya mayar da wurin tamkar wuri na ziyarar ibada.

Wadannan dalilai ne suka sanya tuntuni aka yi wa wurin lakabi da ‘kwarin aminci’ tun asali, kuma ake ci gaba da kiranta da hakan har yanzu.

 

Tarihin kafuwar makabartar Wadi al-Salam

Makabartar ta samo asali ne tun kafin zuwan addinin Musulunci a lokacin Annabi Muhammad, inda tun kafin wancan lokaci ake binne mutane a wurin.

Wuri ne mai muhimmanci wanda ke karbar bakuncin masu bincike na kimiyya da masana addini, musamman mabiya Shi’a daga sassa daban-daban na duniya.

Wadi al-Salam na da kofofi da dama da ake bi wajen shigar ta, inda hakan ke saukake zirga-zirga ga masu ziyara, kuma yawancin wadannan kofofi na karuwa ne bisa fadadar makabartar.

A shekara ta 2016 ne Hukumar kula da ilimi da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana makabartar a matsayin daya daga cikin wuraren tarihi na duniya.

 

Kalubalen da makabartar ke fuskanta

Daya daga cikin manyan kalubalen da makabartar ke fuskanta shi ne karuwar mutane da ake binnewa a lokacin yaki.

Misali, a lokacin da aka yi fama da rikicin kungiyar ISIS a Iraki, yawan mutanen da ake binnewa a kowace rana a makabartar ya daga zuwa 150 ko 200 a kowace rana, daga gawa 80 zuwa 120 da aka saba.

Wannan ya sanya wuraren binne sabbin mamata ya yi karanci.

 

Farashin binne mamaci

Farashin binne mamaci a makabartar Wadi al-Salam ya danganta ne da lokaci da kuma halin da ake ciki na zaman lafiya.

Ya zuwa farkon shekara ta 2025, kudin sayen filin binne mamaci mai girman murabba’in mita 25 ya kai miliyan biyar na kudn kasar Iraki, wato kimanin Dala 4,100, inda hakan ya nunka farashin da ake biya a lokutan da ake zaman lumana sosai.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Tsokaci Dangane Da Juyin Mulki A Nahiyar Afirka November 2, 2025 Manyan Labarai An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano November 2, 2025 Manyan Labarai Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima November 1, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mutum Daya Ya Yi Shahada Sanadiyyar Harin Sojojin HKI A Kudancin Lebanon
  • Falasdinawa Biyu Sun Yi Shahada A Nablus Da Khalil
  • Kano Pillars ta koma ƙarshen teburin Gasar Firimiyar Nijeriya
  • Zamfara Ta Tashi Daga Matsayi Na 36 Zuwa Na 17 A Shekara Biyu Ƙarƙashin Gwamna Lawal — Rahoton BudgIT
  • Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazanar Sa Ga Nijeriya
  • Wadi Al-Salam: Maƙabartar Musulmai Mafi Girma A Duniya
  • Gwamnatin Isra’ila Tana Ci Gaba Da Hana Masu Jinya Zuwa Kasashen Waje Neman Magani Daga Gaza
  • Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon
  •  Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada
  • Sanata Sunday Marshall Katung Ya Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar APC