Wani Mutum Ya Kashe Matarsa Da Duka Har Lahira A Edo
Published: 21st, May 2025 GMT
Mahaifinta, Everistus Nnadozie, ya ce an sanar da shi cewa surukinsa Esosa Imasuen ne ya yi wa ‘yarsa duka har ta samu raunika sosai.
Ya ƙara da cewa an kai ta asibiti inda likita ya tabbatar da cewa tana fama da zubar jini a cikin jikinta.
Ya ce kafin ya isa asibitin, ‘yarsa ta rasu.
Bayan haka kuma, Esosa ya ɗauki gawarta ya kai wani waje ba tare da ya sanar da iyayenta ba.
“Na je gidansa, sai aka ce ya tsere,” in ji mahaifin.
Ya ce yana ta kiran Esosa domin ya nuna masa inda aka kai gawar ‘yarsa, amma ya ƙi amsa waya.
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Edo, ya ce sun duba wurare da dama a Benin, amma babu rahoton wannan lamari.
Ana ci gaba da neman Esosa Imasuen ruwa a jallo.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Ana zargin mace da kashe ’yar uwarta a kan N800 din barkono
Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Ondo ta tabbatar da kama wata mata mai suna Iluyemi Bosede bisa zargin kashe yayarta, Tewogboye Omowumi, a Akure, babban birnin jihar.
A cewar sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, Olayinka Ayanlade, ya fitar a ranar Talata, ya ce lamarin ya faru ne a ranar shida ga Satumba, 2025, bayan wata sa’insa da ta kaure tsakanin matar da marigayiyar kan Naira 800.
Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin NajeriyaJami’in ya bayyana cewa Bosede ta ture ’yar uwarta har ta faɗi ƙasa, lamarin da ya haifar da mutuwarta.
Ya ce, “Binciken farko ya nuna cewa Iluyemi Bosede ta je wurin yayar tata, Tewogboye Omowumi mai shekaru 35, domin karbar bashinta na N800 na kudin tumatir da barkono. Sai dai tankiyar da ta fara a matsayin ƙaramin sabani ta rikide zuwa tashin hankali, inda ake zargin Bosede ta riƙe kayan marigayiyar har ta faɗi ƙasa.”
“Abin takaici, duk da an garzaya da marigayiyar asibiti don samun kulawar gaggawa, likitoci sun tabbatar da mutuwarta tun kafin a fara ba ta taimako. Wannan lamari ya nuna yadda ƙaramin sabani zai iya rikidewa zuwa mummunar husuma idan ba a magance shi cikin lumana ba.”
Bayan faruwar lamarin, rundunar ta ce ta kama wadda ake zargi kuma tana tsare da ita a halin yanzu, yayin da bincike ke ci gaba.
Rundunar ta kuma tabbatar da cewa za a gurfanar da wadda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike, domin ta girbi abin da ta shuka.