Ma’aikatar Tsaro Ta Fitar da Rahoton Nasarori Karkashin Shirin “Sabuwar Fata” na Shugaba Tinubu
Published: 22nd, May 2025 GMT
Ma’aikatar Tsaro ta fitar da cikakken rahoton nasarorin da ta cimma daga watan Agusta 2023 zuwa Afrilu 2025, inda ta danganta nasarorin da manufofin kamfen din Shugaba Bola Ahmed Tinubu na “Sabuwar Fata.” wato (Renewed Hope).
Wannan rahoto ya samu hadin gwiwa daga Ofishin Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsare-tsare da Hadin Kai tare da Cibiyar Tsare-tsaren Aiki ta Gwamnati (CRDCU).
Daya daga cikin manyan nasarorin da rahoton ya nuna shi ne hadin gwiwa da Ofishin Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro (ONSA) don kirkiro da aiwatar da sabuwar manhaja ta hadin gwiwa tsakanin sojoji da fararen hula (CIMIC).
Wannan manhaja na da nufin inganta fahimta da aiki tare tsakanin jami’an tsaro da al’umma, musamman a yankunan da ke fama da rikice-rikice.
Ma’aikatar ta kuma samu ci gaba a fannonin tsare-tsaren tsaro, karfafa hadin gwiwar hukumomi, da kuma inganta iyawar sojoji wajen gudanar da ayyukan cikin gida da na waje. Wannan na cikin kokarin gwamnati na tabbatar da tsaro da ci gaban kasa.
Rahoton ya kwatanta wadannan nasarori da alkawuran da aka dauka a cikin Tsarin Aiki na “Sabuwar Fata,” yana mai nuna yadda gwamnati ke sauke nauyin da ke wuyanta.
A yayin da Najeriya ke ci gaba da fuskantar kalubalen tsaro, Ma’aikatar Tsaro ta tabbatar da kudurinta na ci gaba da kawo sauyi da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk fadin kasar.
Bello Wakili
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Nasarori Rahoto Sabuwar Fata Tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
Xi Ya Jaddada Kwarin Gwiwa Kan Ci Gaba Mai Inganci A Kasar Yayin Ziyararsa A Henan
A ziyarar da ya kai jerin kogon Longmen, mai shekaru sama da 1,500 wanda UNESCO ta sanya cikin jerin wuraren tarihi da aka gada na duniya, wanda kuma shi ne ke wakiltar matsayin koli na fasahar sassaka kan dutse ta kasar Sin, shugaban ya bayyana muhimmancin karewa da gado da ma yayata al’adun gargajiya na kasar Sin masu daraja. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp