Jigajigan Jihar Kebbi Sun Bukaci Hadin Kan ‘Ya’yan Jam’iyyar APC
Published: 21st, May 2025 GMT
Sanatocin jihar Kebbi guda uku da suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC, tare da Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Sanata Atiku Bagudu, sun bukaci hadin kai tsakanin mambobin jam’iyyar domin samun nasara a zaben 2027.
Sanata Adamu Aliero, wanda ya yi jawabi a madadin sauran sanatocin, ya bayyana haka a wani taron jiga-jigan jam’iyyar APC da reshen jihar ya shirya a Birnin Kebbi.
Sanata Aliero ya ce sauya shekar su daga jam’iyyar adawa PDP zuwa jam’iyya mai mulki APC, domin cigaban jihar ne gaba ɗaya.
A cewarsa, akwai ayyuka da dama da za a aiwatar a jihar Kebbi, amma saboda wakilan jihar a majalisa suna jam’iyyar adawa, aka hana jihar damar cin gajiyar wadannan ayyukan.
Game da matsalar tsaro a ƙasar, Sanata Aliero ya bayyana cewa gwamnati na kokarin shawo kan kalubalen tsaro da kuma rage talauci a ƙasar.
Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Sanata Atiku Bagudu, ya bukaci magoya bayan APC da su mara wa Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Nasiru Idris baya domin samun nasara a wa’adinsu na biyu a shekarar 2027.
Gwamnan jihar Kebbi, Nasiru Idris, ya nuna godiyarsa bisa yadda mambobin jam’iyyar da manyan baki suka halarci taron.
Ya kuma bukaci hadin kai daga mambobin jam’iyyar domin tabbatar da nasarar jam’iyyar daga matakin shugaban kasa har zuwa gwamnoni da ‘yan majalisun tarayya da na jiha a zaben 2027.
Cikin wadanda suka halarci taron akwai Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Sanata Atiku Bagudu, Sanata Abdullahi Yahaya, Sanata Musa Maidoki, mambobin majalisar tarayya da na jiha, tsohon gwamnan Kebbi Sa’idu Nasamu Dakingari, Daraktan Hukumar NAMA da na HYPERDEC, Sakataren Tsare-tsaren Jam’iyyar APC, da sauransu.
Daga Abdullahi Tukur
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Tsare tsaren jihar Kebbi
এছাড়াও পড়ুন:
Abba Ya Yi Sabbin Naɗe-naɗe A Jihar Kano
Gwamna Abba ya bayyana gamsuwarsa da ƙwarewar sabbin jami’an da aka naɗa, inda ya bayyana cewa za su taka rawar gani wajen aiwatar da manufofin gwamnatinsa.
Ya ce jajircewa da ƙwarewarsu na daga cikin dalilan da suka sa aka zaɓe su domin su taimaka wajen ci gaban Jihar Kano.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp