Sharhin Bayan Labarai: Iran Zata Ci Gaba Da Tashe Uranium Tare Da Yarjeniya Ko Babu Ita
Published: 21st, May 2025 GMT
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka. Sharhin bayan labarammu nay au zai yi Magana dangabe da “Tattaunawar shirin Nukliyar kasar Iran da Amurka yana tanga-tanga’ wanda ni tahir amin zan karanta.
Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa, da alamun tattaunawa tsakanin kasar ta kuma Amurka dangane da shirin nukliyar kasar Iran ba zai je ko in aba, saboda yadda bangaren Amurka a cikin kafafen yada labaransu, daga ciki har da jakadan Amurka kan al-amuran gabas ta tsakiya, kuma shugaban tawagar Amurka a tattaunawar wato Steve Witkoff ya fito a kafafen yada labarai na Amurka yana fadar cewa duk wata yarjeniyar da za’a cimma da kasar Iran nan gaba dole sai ya hada da dakatar da tace makamashin Uranium kwatakwata a cikin kasar Iran.
Jagoran ya bayyana cewa tare da wannan manufar tattaunawar ba zata je ko in aba, kuma Amurka ta dage kan tattaunawa kai tsaye da Iran ne don ya nunawa duniya ya tilastawa Iran zama da Amurka tare da barazan da kuma dabarbaru da yaudara da sauransu.
Jagoran ya bayyana haka ne a shafinsa na X, a jiya litinin ya kuma kara da cewa ‘bamu san abinda zai faru ba, ammam ga dukkan alamu ba. Inda za’a je a wannan tattaunawar.
Har’ila yau jagoran ya sake nanata hakan a jawabin da ya gabatar a Hussainiyar Imam Khomaini (q) dake kusa da gidansa a nan birnin Tehran. A lokacinda ake juyayin cika shekara guda da shahadar Shahid Ibrahim Ra’isi tsohon shugaban kasar wanda ya yi tsahari da jirgin sama mai saukar ungula a lardin Aerbaijan ta gabas dake arewa maso yammacin Iran a shekarar da ta gabata.
Kafin haka dai mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Majid Takhta-Ravanci ya bayyana cewa abinda tawagar Amurka take gabatarwa a tattaunawa daban, sannan abinda take fada a kafafen yada labarai kuma daban. Haka ma shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fadi wannan maganar a yau yakuma sake fadar akasinta a gobe. Don haka shima ya sha fadin cewa manufarsu it araba Iran da makamashin Uranium kwata-kwata.
Amma ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, tun farko Iran ta bayyana cewa batun tace makamashin Uranium ba abin tattaunawa ne da kowa ba, ya kuma karada cewa sun shiga tattaunawa da Amurka saboda Trump ya sha nanata cewa manufarsa ita ce hana Iran mallakar makaman Nukliya. Sai iran ta ce, indai wannan ne kawai manufar Amurka sai an gamsar da shi kan cewa Iran bata nufin mallakar makaman Nukliya, kuma bata da wani shiri wanda yake nuna haka. Amma batun hana kasar saffara makamashin Uranium kwatakwata mafarki ne Amurka ta ke. Don ba wanda ya isa ya hana Iran sarrafa makamashin nukliya Uranium, tunda hakkinsa ne ta yi hakan, kuma yin hakan yana amfanar mutanen kasar a fannonin da dama.
Aragchi ya bayyana cewa, Iran tana iya tattaunawa kan yawan makamacin Nukliya data tace amma dakatar da tacwa kwatakwara baa bin tattaunawa da kowa bane.
Ministan harkokin wajen kasar Iran sannan shugaban tawagar tattaunawa da Amurka kan shirinta na makamashin nukliya ya bayyana cewa, Iran zata ci gaba da halartan taron tattaunawa kan shirin makamashin nukliyar, kamar yadda tayi a tarurruka guda hudu da suka gabata. Har zuwa lokacinda tawagar Amurka zata fito fili ta fada mata manufarta a tattaunawan, inda daga nan Iran zata yanke shawara kan matakan da zata dauka kan al-amarin.
Yace ya zuwa yanzu dai tun tattaunawa ta hudu, bangarorin biyu basu tsaida lokaci da kuma wurin da za’a yi tattaunawa na gababa.
Ya zuwa yanzu dai JMI ta amfana da makamashin Uranium tun lokacinda ta fara tace shi a cikin gida.
A halin yanzu Iran tana amfanin da shirinta na makamashin Uranium a cikin gida don samarwa cibiyar Nukliya dake cikin Jami’an Tehran don bincike da samar da magunguna wadanda mutanen kasar suke bukata, kuma tun shekara 2006 ta samar da magunguna daban-daban a wannan cibiyar.
Hakama shirin nukliya na kasar Iran yana samar da makamashin nukliya ga cibiyar samar da wutan lantarki ta makamashin nukliya da ke birnin Bushar na kudancin kasar. A halin yanzu cibiyar tana samar da akalla magawat 1000 na wutan lantarki a kasar. Banda haka iran tana da shirin gina wasu Karin cibiyoyin samar da wutan lantarki tare da amfani da makamashin nukliya har guda 20 nan gaba. Kafin juyin juya halin musulunci a kasar Iran a shekara 1979, kasashen yamma suna sayarwa Jami’ar Tehran makamashin da take bukata don amfani da shi a cibiyar. Amma bayan nasarar juyin juya halin musulunci a kasar sun dakatar da sayar mata. Haka madangane da cibiyar bada wutan lantarki na Bushar, wani kamfanin kasar Jamus ce take gina shi, amma bayan nasarar juyin juya halin musulunci anan kasar Iran sun dakatar da aiki. Sai da kasar Iran ta nemi taimakon kasar Rasha ta zo ta kamala aikin.
Banda wannan Iran ta fara samar da magunguna wadanda zasu taimaka wajen binkasa numa da kyautata aikinsa a cikin kasa, musaman kashe cututtukan wanda zai bawa.
Don haka Iran tana bukatar sarrafa makamshin Uranium a cikin gida bisa ka’idojin da yarjeniyar NPT ta bawa kasar karkashin kula da hukumar IAEA. Hakkin kasar Iran ce ta saffara makamshin uranium kuma ba zata yi kasa a guiwa ba wajen kare hakkinta wanda dokokin kasa da kasa suka bata. Idan Amurka ko kasashen yamma zasu iya bawa Iran bukatunta na makashin nukliya me yasa basu bata ba ko suka hanata bayan nasarar juyin juya halin musulunci a kasar. Wannan kawai ya tabbatar da cewa dole ne Iran ta ci gaba da tashe uranium a cikin gida don bukatun kanta.
Sannan ba wanda ya isa ya hadata yin hakan ko ana ha maza ha mata.
Masu sauraro karshen sharhin Kenan.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: juyin juya halin musulunci a makamashin Uranium makamashin nukliya ya bayyana cewa wutan lantarki tattaunawa da a kasar Iran a tattaunawa
এছাড়াও পড়ুন:
Taron Tehran ya bukaci tattaunawa cikin gaggawa kan kalubalen yankin
Manyan jami’ai daga kasashe da dama da ke halartar taron tattaunawa na Tehran sun yi kira da a tattauna domin tunkarar manyan al’amura a yankin.
Manyan jami’ai daga kasashe 53 da suka hada da ministoci da masana da ne ke halartar taron na kwanaki biyu.
Ministan harkokin wajen Oman Badr bin Hamad Al Busaidi ya ce a halin yanzu yankin yammacin Asiya na fuskantar kalubale da dama da ke bukatar tattaunawa cikin gaggawa.
A yayin jawabin nasa, Ministan harkokin wajen Oman ya bayyana matukar damuwarsa kan tashe-tashen hankula da kisan kiyashin da al’ummar Falasdinu ke fuskanta, yana mai bayyana wannan lamari a matsayin wani abin takaici a duniya.
A nasa bangaren, ministan harkokin wajen kasar Tajikistan ya jaddada bukatar yin tattaunawa mai ma’ana don tinkarar manyan matsalolin da duniya ke fuskanta.
Armeniya ta bakin sakatarenta na komitin sulhu Armen Grigoryan ta tabbatar da aniyar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Shi kuwa tsohon firaministan kasar Iraki Adel Abdul-Mahdi ya bayyana matukar damuwarsa game da matsalar jin kai da kuma ci gaba da kisan kiyashi a zirin Gaza.
Ya yi Allah wadai da gazawar kasashen Larabawa da kungiyoyin kasa da kasa, wadanda a cewarsa, sun kasa dakile irin ta’asar da Isra’ila ke yi.