EU ta dage takunkumin da ta kakaba wa Syria
Published: 21st, May 2025 GMT
Bayan sanarwar ba-zata da Amurka ta yi a makon da ya gabata, Tarayyar Turai ta ce za ta dage takunkumin da ta kakaba wa Syria.
Ministocin harkokin waje da ke taro a Brussels ne suka yanke shawarar dage dukkan takunkumin tattalin arzikin kan Siriya.
“Muna son taimakawa al’ummar Siriya wajen sake gina sabuwar Siriya,” in ji jami’ar kula da harkokin wajen Tarayyar Turai Kaja Kalas.
Tarayyar Turai ta kuma yi alkawarin bayar da Yuro biliyan biyu da rabi domin sake gina kasar.
Matakin dage wannan takunkumin da aka kakabawa gwamnatin Bashar al-Assad tun daga shekara ta 2011, zai bada damar sakin kadarorin kasar da har yanzu ke daskare, sannan kuma zai baiwa hukumomin kasar damar neman zuba jarin da suke bukata.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Tehran ta yi kakkausar suka kan tsare Iraniyawa a Birtaniya
Iran ta gayyaci mai kula da harkokin kasar Birtaniya a birnin Tehran, biyo bayan tsare wasu ‘yan kasarta da dama ba bisa ka’ida ba a kasar.
Shugaban bangaren kula da sashen yammacin turai a ma’aikatar harkokin wajen kasar ya yi kakkausar suka da nuna adawa da matakin na gwamnatin Birtaniyya, da kuma zarge-zargen da ba su dace ba da ake yi wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Jami’in ya ce tsare ‘yan kasar Iran ya sabawa ka’idoji da dokokin kasa da kasa da kuma hakkokin bil’adama da aka amince da su, saboda an tuhume su ba tare da wata hujja ba.
Ya kara da cewa ‘yan kasar Iran da ake tsare da su, an kuma hana su harkokin ofishin jakadanci da kuma ba su kariya…
Jami’in na Iran ya jaddada cewa gwamnatin Birtaniyya ce ke da cikakken alhakin irin wadannan ayyuka, wadanda ake ganin suna da alaka da siyasa domin matsin lamba kan Iran.
A ranar Asabar an kama wasu mutane hudu ‘yan kasar Iran, kuma An tsare su ne a karkashin dokar ta’addanci, kamar yadda kafafen yada labaran Burtaniya suka ruwaito.