Gwamnatin Tarayya ta fitar da cikakken rahoto na tsakiyar zangon mulki da ke bayyana muhimman nasarorin da Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya ta cimma daga watan Mayu 2023 zuwa Afrilu 2025.

Rahoton, wanda Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsare-Tsare da Daidaita Ayyuka ya gabatar, ya bayyana ci gaba mai ma’ana da aka samu a fannin gine-ginen ababen more rayuwa, musamman hanyoyi, karkashin shirin Renewed Hope Action Plan na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Daya daga cikin manyan nasarorin da rahoton ya nuna shi ne ci gaba da aiwatar da shirin Highway Development and Management Initiative (HDMI), wanda ke amfani da tsarin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu (PPP). Wannan tsarin ya ba da damar janyo hannun jari daga masu zaman kansu don gyara da gina sabbin manyan hanyoyi da ke haɗa manyan birane da cibiyoyin kasuwanci a faɗin ƙasar.

Ma’aikatar Ayyuka ta kuma canja fasaha wajen gina hanyoyi daga amfani da kwalta zuwa amfani da fasahar siminti (concrete technology), wacce aka sani da jurewa dogon lokaci da rage buƙatar gyare-gyare akai-akai.

Wannan sabon tsarin yana tabbatar da cewa hanyoyin da ake ginawa yanzu za su dawwama, za su kasance masu aminci, kuma su fi araha a nan gaba.

Rahoton ya kuma nuna yadda Ma’aikatar Ayyuka ta ke kirkirar hanyoyin samun kuɗi na musamman don aiwatar da manyan ayyuka.

Hanyoyin sun haɗa da fita kasuwa don neman jari, fitar da takardun lamuni na gine-ginen ababen more rayuwa, da kuma ƙara faɗaɗa haɗin gwiwa da masu zaman kansu.

Wannan ya taimaka wajen ɗora ma’aikatar kan tafarkin da zai kai ga ingantaccen sauyi duk da ƙalubalen tattalin arziki.

“Manufar Renewed Hope ba ƙalmar kamfen ba ce kawai — tsari ne mai rai da ake aiwatarwa a kowane yanki na Najeriya,” in ji rahoton. “Ma’aikatar Ayyuka na aiki ba dare ba rana don tabbatar da cewa al’umma sun ji daɗin wannan sauyi.”

Wasu daga cikin manyan ayyukan da ake aiwatarwa ko aka kammala sun haɗa da faɗaɗa titin Legas-Ibadan, aikin titin Abuja-Kano, da sauran hanyoyin haɗin jihohi da ke da mahimmanci ga ciniki, noma da haɗin kai na ƙasa.

Masana sun bayyana cewa waɗannan nasarori na nuni da gaskiya da nufin gyara ƙasa bisa tsari da tasiri. Da sauran shekaru biyu kafin ƙarshen wannan zangon mulki, ana sa ran za a ci gaba da jan ƙasa da sauri domin samar da ci gaba mai ɗorewa.

Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsare-Tsare da Daidaita Ayyuka (CRDCU) ya jaddada cewa bin diddigin aiki da nuna gaskiya a bainar jama’a su ne ginshiƙan tsarin mulki na Renewed Hope.

Yayin da Najeriya ke ci gaba da tafiya zuwa ga zamanancewar ababen more rayuwa, Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya na taka rawa mai muhimmanci wajen gina tubalin ci gaban ƙasa da haɗa al’umma da juna.

Bello Wakili

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Ayyuka Nasarori

এছাড়াও পড়ুন:

Yadda ‘Yan Majalisa Ke Cusa Ayyuka Marasa Amfani A Kasafin Kuɗi – Rahoto

BudgIT ta buƙaci gwamnati da ta riƙa bin gaskiya da adalci wajen tsara kasafin kuɗi, domin a tabbatar kuɗin gwamnati na yi wa jama’a amfani kai tsaye.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ma’aikatar Tsaro Ta Fitar da Rahoton Nasarori Karkashin Shirin “Sabuwar Fata” na Shugaba Tinubu
  • Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Nasarorin Noma da Tsaron Abinci Karkashin Shirin Renewed Hope
  • Trump Zai Shirya Liyafar Musamman Ga Manyan Ƴan Crypto 
  • Yadda ‘Yan Majalisa Ke Cusa Ayyuka Marasa Amfani A Kasafin Kuɗi – Rahoto
  • Shirye-shiryen Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Minista
  • Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Minista
  • Sharhin Bayan Labarai: Iran Zata Ci Gaba Da Tashe Uranium Tare Da Yarjeniya Ko Babu Ita
  • DAGA LARABA: “Abba Al-Mustafa Ba Shi Da Hurumin Dakatar Da Fina-finanmu”
  • Zulum zai saya wa sojoji da ’yan sa-kai ƙarin motoci don yaƙar Boko Haram