Mai kwashe sharar da ya shekara 40 yana tara kuɗin Hajji ya isa Saudiyya tare da matarsa
Published: 22nd, May 2025 GMT
Wani dattijo mai aikin kwashe shara da ya shekara 40 yana tara kuɗin domin zuwa aikin Hajji ya samu cika burinsa a bana.
A karshe dattijoin dan qasar Indosauke ya samu damar zuwa sauke farali inda ya isa Kasa Mai Tsarki tare da matarsa.
Wanni dattijon wanda ya nuna tsananin juriya da jajircewa ya bayyana yadda kwashe shekara 40 yana tara 1,000 na kuɗin ƙasarsu a kullum, domin tara kuɗin da zai sauke farali shi da mai ɗakinsa.
A yayin da ake yake hira da Kamfanin Dillancin Labarai na kasar Saudiyya bayan isarsu ƙasar domin sauke farali, dattijoin ya bayyana cewa tun ashekarar 1986 ya fara tara wannan kuɗi bayan samun goyon bayan matarsa.
Ya bayyana cewa a duk loƙacin da ya dawo daga aikinsa na kwashe shara sai ya ware wannan kuɗin domin cika masu burinsu.
Har wa yau ce duk da halin matsi da rashi da suke tsintar kansu a wasu lokuta wannan bai sa sun sauya ra’ayinsu na tara kuɗin Hajjin ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: mai kwashe shara tara kuɗin
এছাড়াও পড়ুন:
Bayan Shekaru 42 Babu Kofi, Tottenham Ta Lashe Gasar Europa League Akan Manchester United
Duka kungiyoyin biyu sun kasa tabuka abin azo agani a wannan kakar a gasar Firimiya Lig, inda Manchester United ke matsayi na 16 Tottenhma na bi mata, amma wannan nasarar da yaran na Postecoglu suka samu ya sa sun samu gurbi kai tsaye a gasar Zakarun Turai ta badi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp