Aminiya:
2025-07-06@03:06:15 GMT

Sojoji da ’yan siyasa na taimaka wa Boko Haram da bayanai — Zulum

Published: 21st, May 2025 GMT

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa wasu daga cikin sojoji da ’yan siyasa na taimaka wa ƙungiyar Boko Haram ta hanyar ba su bayanai.

A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na News Central, Zulum ya ce gwamnatinsa za ta ɗauki matakin da ya dace kan duk wanda ke taimaka wa ’yan ta’adda.

Hajjin 2025: Kashi 79 na maniyyatan Najeriya sun isa Saudiyya – NAHCON Gwamnati za ta sayar da gidaje 753 da EFCC ta ƙwato a hannun Emefiele 

Ya ce: “Akwai masu bai wa Boko Haram bayanaj a cikin sojoji, ’yan siyasa da sauran jama’a. Za mu ƙarfafa leƙen asiri, kuma mu ɗauki tsattsauran mataki a kansu.”

Gwamna Zulum ya ce dole ne a haɗa kai a yaƙi ta’addanci ta hanyar ƙoƙarin gyara rayuwar al’umma da inganta tattalin arziƙi da samar da ayyukan yi, ba kawai amfani da makamai ba.

Ya bayyana cewa daga cikin sama da mutum 300,000 da suka miƙa wuya daga ƙungiyar Boko Haram, akwai yiwuwar wasu daga cikinsu sun koma daji.

Ya kuma ce rundunar soji ba ta da isassun kayan aiki da za su iya yaƙar ta’addanci yadda ya kamata, inda ya ce ’yan ta’addan na da kayan zamani sama da na sojoji.

Sai dai ya yaba wa sojojin Najeriya saboda irin gudunmawar da suke bayarwa wajen kawo zaman lafiya.

Zulum ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya saurari shawarwarin ƙwararru, musamman sojoji, domin magance matsalar tsaro.

“Dole a kafa jami’an tsaron daji cikin gaggawa. Shugaban ƙasa ya saurari mutane masu gaskiya da fahimtar abubuwa. Ka da a ci gaba da siyasantar da matsalar tsaro,” in ji shi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan siyasa Boko Haram matsalar tsaro

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan Majalisar Wakilai bakwai na Akwa Ibom sun koma APC

A ci gaba da sauya sheƙar da ’yan Majalisar Wakilai na Tarayya ke yi a ranar Alhamis wasu mambobi bakwai daga Jihar Akwa Ibom sun sanar da sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar APC mai mulki.

Cikin waɗanda suka sauya sheƙa sun haɗa da shida daga Jam’iyyar PDP da kuma ɗaya daga Jam’iyyar YPP.

’Yan Najeriya sun fara begen Buhari saboda azabar Tinubu – Amaechi Gwamnatin Yobe ta rufe kasuwanni 3 saboda matsalar tsaro

Shugaban Majalisar Wakilan Tarayya Tajudeen Abbas ne ya karanta wasiƙunsu na sauya sheƙa a zauren Majalisar a ranar Alhamis yayin zaman majalisar.

’Yan majalisar dai sun yi nuni da ƙara samun rarrabuwar kawuna da rigingimun cikin gida a cikin Jam’iyyar PDP a matsayin dalilin da ya sa suka yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar.

Waɗanda suka sauya sheƙa daga PDP sun haɗa da: Paul Ekpo da Unyime Idem da Martins Etim da Okpolu Ukpong Etteh da Uduak Odudoh da Okon Ime Bassey.

Shi ma ɗan Majalisa Emmanuel Ukpong-Udo na Jam’iyyar YPP ya koma APC.

’Yan majalisar dai sun ce rikicin da ya ɓarke a Jam’iyyar PDP a Akwa Ibom da ma ƙasa baki ɗaya ya sa ba su iya wakiltar mazaɓarsu yadda ya kamata.

Ficewar ta zo ne makonni kaɗan bayan gwamnan Jihar Akwa Ibom, Umo Eno ya koma APC.

Da yake mayar da martani game da sauya sheƙar, shugaban marasa rinjaye na majalisar, Kingsley Chinda ya nuna baƙin cikinsa game da ci gaban da aka samu.

Chinda ya ce, iƙirarin rarrabuwar kawuna a cikin Jam’iyyar PDP bai dace ba kuma ya saɓawa doka.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi
  • 2027: Kungiyoyi 110 Ne Ke Neman Rajistan Zama Jam’iyyun Siyasa A Yanzu Haka – INEC
  • Haɗarin Da Ke Ƙunshe Da Jin Ɓangare Ɗaya Na Labari
  • Sojoji sun kashe ’yan ta’adda da ƙwato makamai a Borno
  • Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga Tare Da Kwato Makamai A Jihar Filato
  • NAJERIYA A YAU: Shin Ko Hadakar Sabuwar Jamiyyar ADC Za Ta Fidda Wa ‘Yan Najeriya Kitse Daga Wuta?
  • Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 1,191, Sun Ceto 543 Cikin Watanni Uku
  • ’Yan Majalisar Wakilai bakwai na Akwa Ibom sun koma APC
  • Gwamnatin Yobe Ta Rufe Kasuwanni Uku Saboda Fargabar Hare-haren Boko Haram
  • Gwamnatin Yobe ta rufe kasuwanni 3 saboda matsalar tsaro