Ma’ariv: “Isra’ila” Ta Zama Saniyar Ware A Duniya
Published: 22nd, May 2025 GMT
Jaridar ‘yan sahayoniya ta “Ma’ariv’ ta buga labarin da yake cewa; Isra’ila tana fuskantar matsalar diplomasiyya saboda ci gaba da yakin Gaza.
Jaridar ta kuma ce; A halin yanzu “Isra’ila” tana fuskantar abinda ta kira “Tsunami Na Diplomasiyya” saboda yakin da take ci gaba da yi a Gaza.
Haka nan kuma jaridar ta soki gwamnatin Netanyahu tare da bayyana ministan harkokin waje Gadion Sa’ir wanda ta ce, ba abinda ya dame shi kamar ci gaba da zama akan kujerarsa, da cewa; Ba ya fahimtar girman musifar da take tunkaro Isra’ila.
Har ila yau, jaridar ta yi suka ga ministar sufuri Miri Rigiv da cewa saboda ta’annuti, ta ki yin furuci da cewa Isra’ila tana karkashin takunkumin zirga-zirga ta sama, kuma abu ne mai yiyuwa ta fuskanci takunkumi na ruwa.”
Akan ministan ilimi Yoav Kish, jaridar ta ce, babu abinda yake gabansa sai rikicin siyasa akan jami’ar Tel Aviv, maimakon ya mayar da hankali akan yanke alaka da jami’oin duniya su ka yi da jami’o’in Isra’ila.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Imam Khaminae Ya Halarci Makokin Ashoora A Gidansa A Tehran
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya halarci zaman makokin da aka gudanar a hussainiyar Imam Khomaini (q) da cikin gidansa a nan birnin Tehran a daren Ashoorah a jiya Asabar da yamma.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Hujjatul Islam Masaoud Ali wanda ya karanta makokin yana fadar cewa, kasar Iran zata dauki darasi daga Imam Hussain (a) na rashin mika kai da azzalumai.
Ya kuma bayyana yunkurin da Iraniyawa suke yi a halin yansu yana daga cikin gwagwarmayan duniya don fuskantar azzaluman duniya karkashin jagorancin HKI da Amurka.
Ya kuma kara da cewa musulunci ne yake gaba da gaba da kafircin duniya a cikin yakin kwanaki 12 wanda HKI da Amurka suka jagoranta kan JMI. Kuma wannan yunkirin da sauran masu gwagwarmaya a duniya zasu ci gaba da gwagwarmaya tare da jagorancin Imam Sayyid Aliyul Khaminae. Wannan dai shi ne bayyanar Jagoran a karon farko bayan yakin kwanaki 12.
Malamin ya kara da cewa, iraniyawa ba zasu mika kai ba har zuwa nasara kamar yadda muka koya daga Imam Hussain (a) hakan a ranar Ashoorah.
A lokacinda Mahmoud Karimi zai karanta makokin an ga Imam Khaminae (H) yana fadawa Karimi wani abu a kunnensa , inda daga baya Karimin ya bayyana cewa ya umurce shi y ace, kasata zaki wanzu a zuciyata da raina.