An yi Jana’izar Shugaban Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Ƙasa a Zariya
Published: 22nd, May 2025 GMT
An gudanar da Jana’izar Malam Maikudi Umar (Cashman) Shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Ƙasa a garin Zariya, Jihar Kaduna.
Marigayin dan shekaru 62, jarumi ne, mai shirya finafinai kuma ma darakta da ke gudanar da aikace aikacen sa a masana’antar Kannywood da Nollywood.
Dan uwan mamacin, Abdul Azeez Muazu, Talban Tudun Jukun yace Umar ya rasu ne bayan gajeriyar jinya a Asibitin Koyarwa Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Shika, Zariya.
Yace rasuwar ya faru ne a daren ranar laraba sailin da akayi Jana’izar sa a ranar Alhamis a makabarta dake Zariya.
Shi dai Marigayin har ilau malami ne a Kwalejin kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli dake Zariya.
Ya rasu ya bar yan uwanshi da dama
Hoton Marigayi Maikuɗi Umar CASHMAN
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da janye dokar ta-baci a Jihar Rivers daga ƙarfe 12 na daren 17 ga watan Satumban 2025.
Shugaban Ƙasar, a wata sanarwa da ya sanya wa hannu, ya ce dokar ta-bacin da ta dakatar da Gwamna, Mataimakiyarsa, da ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida ta cimma manufarta na dawo da zaman lafiya a jihar.
Tinubu ya bayyana cewa ya yi amfani da Sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulkin 1999 ne a watan Maris na 2025 sakamakon durƙushewar mulki a Jihar Rivers.
A cewarsa, rashin jituwa tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Majalisar Dokokin Jihar, da kuma lalata muhimman kadarorin gwamnati sun jefa jihar cikin rikici.
“Lamarin ya kai ga Babbar Kotun Ƙoli ta bayyana a ɗaya daga cikin hukuncinta cewa babu gwamnati a Jihar Rivers.” In ji Shugaban Ƙasa.
Ya gode wa Majalisar Ƙasa bisa amincewa da wannan sanarwa, tare da yabawa Sarakuna da jama’ar jihar bisa haɗin kan da suka bayar.
Tinubu ya kuma yaba wa masu adawa da suka kalubalanci wannan mataki a kotu, yana cewa wannan shi ma wani ɓangare ne na dimokuraɗiyya.
Da yake magana kan sabuwar fahimta tsakanin manyan ‘yan siyasa a jihar, Shugaban Ƙasa ya ce babu dalilin ƙara tsawaita dokar ta-bacin.
Ya bayyana cewa Gwamna Siminalayi Fubara, da Mataimakiyarsa Ngozi Nma Odu, da Shugaban Majalisar Dokoki Martins Amaewhule da dukkan mambobin majalisar jihar za su koma bakin aiki daga 18 ga Satumban 2025.
Tinubu ya yi kira ga shugabannin siyasa a faɗin Najeriya da su ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai domin isar da fa’idodin dimokuraɗiyya ga al’umma.
Daga Bello Wakili