Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa jarirai dubu 14 a Gaza kan iya rasa rayukansu muddin Irsa’ila ta ci gaba da killace Zirin da hana shigar da kayan agaji.

Mataimakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Tom Fletcher na maida martini ne kan matakin gwmanatin Isra’ila na kyale manyan motoci hudu na agaji su shiga Gaza inda ya ce wannan tamkar”digo ne a cikin teku.

“Akwai jarirai 14,000 da za su mutu a cikin sa’o’i masu zuwa idan ba za mu iya kaiwa gare su ba inji shi.

Ya ce motocin agajin da ke dauke da kayan abinci na jarirai da abinci mai gina jiki, suna cikin Gaza amma ba su kai ga farar hula ba saboda gwamnatin Isra’ila ba ta yarda da hakan ba.

Halin jin kai a Gaza ya ta’azzara sosai tun daga ranar 18 ga Maris saboda yadda gwamnatin Isra’ila ta takaita shigar abinci, man fetur, magunguna, da ruwa cikin Zirin na Gaza.

A cewar hukumar Integrated Food Security Phase Classification (IPC), kusan yara 71,000 ‘yan kasa da shekaru biyar suna fuskantar barazanar rashin abinci mai gina jiki.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Majalisar Jigawa Ta Isa Roni A Ci Gaba Da Rangadin Kananan Hukumomi

Kwamatin Harkokin Kananan Hukumomi na Majalisar Dokokin jihar Jigawa ya fara rangadin kwanaki biyu a karamar hukumar Roni a ci gaba da rangadin kananan hukumomin jihar 27 da kwamatin ya kaddamar.

A jawabin sa a sakatariyar karamar hukumar Roni, Shugaban kwamatin Alhaji Aminu Zakari, ya ce tsarin mulkin kasa ya bai wa majalisa ikon dubawa da kuma tantance yadda bangaren zartaswa ke aiwatar da manufofi da shirye shiryen gwamnati.

Ya ce ziyarar za ta mayar da hankali ga dubawa da kuma tantance kundin bayanan sha’anin mulki da na harkokin kudi da suka hada da kundin kasafin kudi na shekarar 2024 zuwa 2025 da Asusun kula da matsalolin muhalli da kundin bayanan kwamitocin karamar hukumar da takardun biyan kudade wato Voucher domin tabbatar da bin tanade tanaden kashe kudaden gwamnati kamar yadda ya kamata.

Alhaji Aminu Zakari ya kara da cewar a rana ta biyu kwamatin zai duba ayyukan raya kasa da karamar hukumar Roni ta gudanar daga watan Oktobar 2024 kawo yanzu sannan a karbi rahoton Yan kwamatin wadda hakan zai bada cikakkiyar fahimta game da halin da karamar hukumar ta ke ciki.

Kazalika, yace ziyarar za ta bada damar ganawa tsakanin ‘yan kwamatin da bangaren zartaswa da na kansiloli da ma’aikata domin karfafa wanzuwar dabi’ar aiki tare da kuma kyakkyawar alaka a tsakanin bangarorin karamar hukumar.

A jawabin sa na maraba, shugaban karamar hukumar Roni Dr. Abba Ya’u, ya bayyana amannar cewar ziyarar kwamatin za ta kawo gyara wajen gudanar da mulkin kananan hukumomi.

Dr. Abba ya kuma bayyana kudurin sa na aiki da shawarwarin kwamatin domin kawo cigaban karamar hukumar.

 

Usman Mohammed Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Babban Mufti Na Masarautar Oman Ya Yi Kakkausar Suka Kan Masu Son Kulla Alaka Da H.K.Isra’ila
  • Akalla Mutane 52 Suka Rasa Rayukansu Saboda Ambaliyan Ruwan Sama A Jihar Texas Na Kasar Amurka
  • Tsadar rayuwa ta sa ’yan Nijeriya na siyan abincin da ya lalace
  • Sojojin Mamayar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Kashe Masu Neman Karbar Kayan Agaji A Gaza
  • Ayyukan ‘Yan Ta’adda Na Barazana Ga Shirin Gwamnati Na Wadata Kasa Da Abinci
  •  Antonio Guterres Ya Kadu Saboda Mummunan Halin Da Falasdinawan Gaza Suke Ciki
  • Majalisar Jigawa Ta Isa Roni A Ci Gaba Da Rangadin Kananan Hukumomi
  • Majalisar Mali ta ƙara wa Goita wa’adin mulkin shekara biyar
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Fitar Da Rahoton Wadanda Suke Taimakawa ‘Yan Sahayoniyya Wajen Murkushe Falasdinawa
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Fitar Da Rahoton Wadanda Suke Taimakawa Yahudawan Sahayoniyya Wajen Murkushe Falasdinawa