Wasu Yahudawa Sun Hana Kayakin Agaji Shiga Yankin Gaza
Published: 21st, May 2025 GMT
Bayan watannin kimani biyu da rabi wanda gwamnatin HKI suka hana kayakin abinci da magunguna shiga yankin zirin Gaza, a jiya talata, gwamnatin Natanyahu ta bada damar a shigo da wasu kadan da kayakin agajin, saboda takurawar wasu shuwagabnni a kasashen yamma.
Amma duk da haka a yau wasu yahudawa fararen hula sun hana wucewar wata mota makare da abinci shigowa zirin gaza daga kofar shiga yankin ta Karen Abu Salem.
Hotunan bidiyo sun nuna yadda jerin gwanon motoci dauke da kayakin agaji zuwa gaza amma wasu yahudawa dauke da tutocin HKI sun zo sun tsaya a gaban daya daga cikinsu suna fadar cewa basu yarda a shigar da kayakin agaji zuwa gaza ba har sai sun mutu gaba daya.
Sannan a dayan bangaren kuma sojojin HKI rike da bindigogi sun zuba masu ido suna kallo.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dinkin Duniya Ta Fitar Da Rahoton Wadanda Suke Taimakawa ‘Yan Sahayoniyya Wajen Murkushe Falasdinawa
Rahoton Majalisar Dinkin Duniya mai ban tsoro ya bayyana cewa: Manyan kamfanoni suna da hannu wajen aiwatar da kisan kare dangi a Gaza
Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya bayyana sunayen wasu manyan kamfanoni na duniya sama da 60 da ke da hannu a tallafawa wajen gine-ginen matsugunan yahudawa ‘yan kaka gida a yankunan gabar yammacin kogin Jordan da kuma hare-haren wuce gona da iri kan Zirin Gaza.
Rahoton wanda wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan halin da ake ciki na kare hakkin bil adama a yankunan Falasdinawa da aka mamaye, Francesca Albanese, ta wallafa ya samo asali ne daga bayanai sama da 200 daga kasashe, kungiyoyin kare hakkin bil adama, masana ilimi da kamfanoni. Ta yi kira ga kamfanonin da su daina kasuwanci da haramtacciyar kasar Isra’ila, ta kuma yi tambayar cewa saboda rike harkokin gudanarwar kudade da kuma doka da oda don fa’idarsu da suke samu daga hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai wa yankunan Falasdinawa.
Daga cikin kamfanonin da aka ambata a cikin rahoton, mafiya shahararsu akwai kamfanonin Amurka: Google, Microsoft, IBM, Caterpillar, a heavy equipment manufacturer, Lockheed Martin, a military manufacturer, da Hyundai na kasar Koriya ta Kudu. Rahoton ya zarge su da hannu a ayyukan danniya, kera makamai, da lalata dukiyoyi a yankunan Falasdinu.
Rahoton yana wakiltar fadada jerin sunayen da aka baiwa Majalisar Dinkin Duniya a shekara ta 2023 wanda ya mayar da hankali kawai kan kamfanonin da ke da alaka gwamnatin mamaya, yayin da sabon rahoton ya kunshi bangarori masu fadi da ke da alaka da cin zarafi a Gaza. Albanese ta gabatar da wannan zargi a cikin wani cikakken bayani game da rikicin Falasdinu: “Yayin da ake kashe rayuka a Gaza kuma ake ci gaba da kara kashe-kashen a gabar yammacin kogin Jordan, wannan rahoto ya nuna cewa kisan kiyashin da ake kira ya ci gaba ne kawai saboda yana da riba ga bangarori da yawa.”